{"id":26184,"date":"2025-11-23T05:43:36","date_gmt":"2025-11-23T04:43:36","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=26184"},"modified":"2025-11-23T05:43:39","modified_gmt":"2025-11-23T04:43:39","slug":"shin-gwamnati-ta-gaza-yin-komai-bayan-kisan-gilla-a-majamiar-owo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-gwamnati-ta-gaza-yin-komai-bayan-kisan-gilla-a-majamiar-owo\/","title":{"rendered":"Shin gwamnati ta gaza yin komai bayan kisan gilla a Majami\u2019ar Owo?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\">Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/100001454238911\/posts\/25059259147039214\/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>George Udom<\/strong><\/a>, yayi da\u2019awar cewa babu wanda aka kama ko aka kai kotu bayan harin da aka kai a majami\u2019ar St. Francis Catholic Church da ke Owo, jihar Ondo.\u00a0<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\">Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa hukumomin tsaro sun kama wadanda ake zargi ana kuma gudanar da shari\u2019a, ba a kai ga kammalawa ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Sako<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shugaban kasar Amurka Donald Trump a baya-bayan nan ya fitar da wata wallafa <a href=\"https:\/\/www.reuters.com\/world\/china\/trump-says-christians-face-existential-threat-nigeria-adds-country-watch-list-2025-10-31\/?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>post<\/strong><\/a> inda yake cewa \u201cKirista na fuskantar barazanar kawar da su a Najeriya\u201d sannan ya bayyana Najeriya a matsayin \u2018kasa da ya kamata a bata kulawa ta musamman\u2019, yace Amurka za ta sake nazari kan taimakon da take ba wa Najeriya muddin mahukuntan kasar suka gaza yin abin da ya dace na ba da kariya ga al\u2019umma mabiya addinin Kirista.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da take mayar da martani Gwamnatin Najeriya (<a href=\"https:\/\/www.premiumtimesng.com\/news\/top-news\/832176-nigeria-reacts-to-us-country-of-concern-designation-denies-christian-genocide-allegation.html?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Federal Government<\/strong><\/a>) tayi fatali da zargin cewa ana kisan kiyashi, tana mai cewa da\u2019awar Amurka ba cikakkiya bace ta dogara ne da bayanai da aka tattara wadanda ba cikakku ba ko ma na yaudara. Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki da kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ba wa kowa tabbaci na damar gudanar da addininsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan faruwar wannan sai aka samu wasu hare-haren irin wadannan suka sake bayyana a shafin sada zumunta, inda a wasu lokutan aka rika sake kanun labaran zuwa kisan kiyashi a shafukan sada zumunta. Daya daga cikin irin wadannan shine abin da ya faru a ranar 5 ga watan Yuni, 2022 inda aka kai hari a Cocin\u00a0 Katolika ta St. Francis a Owo jihar Ondo.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A sake duba wannan labarin tashin hankali ne wani mai amfani da shafin Facebook&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/100001454238911\/posts\/25059259147039214\/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>George Udom<\/strong><\/a> yayi ikirarin cewa hari ne aka tsara shi a kokarin kawar da Kiristoci a doran kasar Najeriya sannan gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin shari\u2019a ga wadanda suka kitsa harin. Ya rubuta cewa \u201cSun zo Owo, jihar Ondo a wata ranar Lahadi kamar haka, sun aikata kisan gilla kan abokaina da iyayensu. Fiye da mutane 50 ne aka halaka. Ka san abin mamaki? Babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari\u2019a. Na so ace na shiga sojan Amurka da na san wasu matsaloli kadan da zan yi maganinsu. \u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An dai rika samun mabanbantan martani kan wannan Umoh Bassey kuma \u201char yanzu Musulmi na cewa babu kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista a Najeriya..!\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Richards Junior Amana ya mayar da martanmi da cewa \u201cAn kama akalla mutum biyr daga cikinsu, kuma mambobi ne na kungiyar ISWAP,\u201d&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Don Onoja U. Samuel&nbsp; ya yi martani ne da cewa \u201cKisa ne na kasa don haka ne ma babu wanda aka kama\u201d yayin da&nbsp; Brave Udofia yayi tambaya da cewa , \u201cIna gwamnan jihar a wannan lokaci?\u201d&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Fola Ramsey ya kara da cewa, \u201cGeorge Udom, a karon farko dana yarda da abin da kake wallafawa, ina ga mun yi tarayya da kai muna da abokin gaba guda daya duk da banbancin siyasa da ke tsakaninmu. Najeriya ita ce kasa daya tilo da muke da ita kuma za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin ta ci gaba da wanzuwa. Gaba dai gaba dai Najeriya.\u201d&nbsp; Wannan wallafa an yada ta sau 61 ya zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan ta samu martani da dama.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ya ga dacewar gudanar da binciken gano gaskiya kan harin na Owo kasancewarsa babban abin tashin hankali da ya shafi iyalai da dama da mabiya darikar ta Katolika da \u2018yan Najeriya baki daya. Wannan lamari&nbsp; an cukurkuda shi da ma danganta shi da wata da\u2019awa mara tushe wato shigar da mahukunta na kasa wajen goyon bayan kisan kiyashi, wannan karfafa gwiwa ce wajen yada labaran da ba haka ba ko jita-jita, abin da ka iya harzuka rikici na addini&nbsp; da jawo daukar ramuwa ta wani bangare da jawo rashin mutuntawa ga bangaren shari\u2019a.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sabanin abin da mai da\u2019awar ke fadi \u201cbabu wanda aka kama da gurfanarwa a gaban shari\u2019a.\u201d Mahukunta sun kama tare da gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a wannan hari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A watan Agusta,2025, mahukunta a Najeriya sun gurfanar da mutane 5 da ake zargi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja saboda alakantasu da harin da aka kai a ranar 5 ga watan Yuni,2022 wadannan mtane da ake zargi kamar yadda aka ba da rahoto sune&nbsp; Idris Omeiza da Al Qasim Idris da Jamiu Abdulmalik da Abdulhaleem Idris da Momoh Otuho Abubakar wadanda suka ce basu aikata laifin komai ba an kuma ci gaba da tsare su (<a href=\"https:\/\/www.reuters.com\/world\/africa\/nigeria-arraigns-five-accused-2022-catholic-church-massacre-abuja-court-2025-08-11\/?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>remanded<\/strong><\/a>) a wajen jami\u2019an tsaro na farin kaya (DSS).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An gurfanar da su a gaban kuliya ne bisa tuhumar aikata laifi na ta\u2019addanci sauran abubuwa da suka biyo baya sun hadar da neman beli da sauran zaman kotu sannan an dage zaman kotun zuwa\u00a0 10 ga Satumba,<a href=\"https:\/\/www.reuters.com\/world\/africa\/nigerian-court-rule-bail-deadly-church-attack-suspects-sept-10-2025-08-19\/?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Sept.<\/strong><\/a> 2025 inda anan ne kotu ta hana beli bisa kafa hujjar kasancewarsu barazana ga tsaro. A watan Nuwamba, jami\u2019an na <a href=\"https:\/\/www.channelstv.com\/2025\/11\/04\/dss-confirms-prosecution-of-owo-church-attack-other-suspected-terrorists\/?utm_source=chatgpt.com\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>DSS <\/strong><\/a>a bayyane sun tabbatar da cewa sun gabatar da wadanda ake zargi da harin na Owo a gaban kuliya, a wani yunkuri na gurfanar da mutanen bisa tuhumar ta\u2019addanci<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awar cewa babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari\u2019a a dangane da harin ta\u2019addancin na Owo wannan ba gaskiya ba ne.Rahotanni da aka tabbatar sun nunar da cewa wadanda ake zargin jami\u2019an tsaro sun kama su kuma an gurfanar da su a gaban babbar kotun shari\u2019a ta tarayya, ana dai shari\u2019a ba kammala ba, don haka wani yace babu abin da ake daga bangare gwamnati wannan kuskure ne ya sabawa abin da yake na zahiri wanda kuma irin hakan na haifar da rura wutar rikici na addini da yada jita-jita.\u00a0\u00a0<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, George Udom, yayi da\u2019awar cewa babu wanda aka kama ko aka kai kotu bayan harin da aka kai a majami\u2019ar St. Francis Catholic Church da ke Owo, jihar Ondo.\u00a0 Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa hukumomin tsaro sun kama wadanda ake zargi ana kuma gudanar da shari\u2019a, ba a kai ga kammalawa ba. Cikakken Sako Shugaban kasar Amurka Donald Trump a baya-bayan nan ya fitar da wata wallafa post inda yake cewa \u201cKirista na fuskantar barazanar kawar da su a Najeriya\u201d sannan ya bayyana Najeriya a matsayin \u2018kasa da ya kamata a bata kulawa ta musamman\u2019, yace Amurka za ta sake nazari kan taimakon da take ba wa Najeriya muddin mahukuntan kasar suka gaza yin abin da ya dace na ba da kariya ga al\u2019umma mabiya addinin Kirista. Da take mayar da martani Gwamnatin Najeriya (Federal Government) tayi fatali da zargin cewa ana kisan kiyashi, tana mai cewa da\u2019awar Amurka ba cikakkiya bace ta dogara ne da bayanai da aka tattara wadanda ba cikakku ba ko ma na yaudara. Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki da kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ba wa kowa tabbaci na damar gudanar da addininsa. Bayan faruwar wannan sai aka samu wasu hare-haren irin wadannan suka sake bayyana a shafin sada zumunta, inda a wasu lokutan aka rika sake kanun labaran zuwa kisan kiyashi a shafukan sada zumunta. Daya daga cikin irin wadannan shine abin da ya faru a ranar 5 ga watan Yuni, 2022 inda aka kai hari a Cocin\u00a0 Katolika ta St. Francis a Owo jihar Ondo. A sake duba wannan labarin tashin hankali ne wani mai amfani da shafin Facebook&nbsp; George Udom yayi ikirarin cewa hari ne aka tsara shi a kokarin kawar da Kiristoci a doran kasar Najeriya sannan gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin shari\u2019a ga wadanda suka kitsa harin. Ya rubuta cewa \u201cSun zo Owo, jihar Ondo a wata ranar Lahadi kamar haka, sun aikata kisan gilla kan abokaina da iyayensu. Fiye da mutane 50 ne aka halaka. Ka san abin mamaki? Babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari\u2019a. Na so ace na shiga sojan Amurka da na san wasu matsaloli kadan da zan yi maganinsu. \u201d An dai rika samun mabanbantan martani kan wannan Umoh Bassey kuma \u201char yanzu Musulmi na cewa babu kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista a Najeriya..!\u201d Richards Junior Amana ya mayar da martanmi da cewa \u201cAn kama akalla mutum biyr daga cikinsu, kuma mambobi ne na kungiyar ISWAP,\u201d&nbsp; Don Onoja U. Samuel&nbsp; ya yi martani ne da cewa \u201cKisa ne na kasa don haka ne ma babu wanda aka kama\u201d yayin da&nbsp; Brave Udofia yayi tambaya da cewa , \u201cIna gwamnan jihar a wannan lokaci?\u201d&nbsp; Fola Ramsey ya kara da cewa, \u201cGeorge Udom, a karon farko dana yarda da abin da kake wallafawa, ina ga mun yi tarayya da kai muna da abokin gaba guda daya duk da banbancin siyasa da ke tsakaninmu. Najeriya ita ce kasa daya tilo da muke da ita kuma za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin ta ci gaba da wanzuwa. Gaba dai gaba dai Najeriya.\u201d&nbsp; Wannan wallafa an yada ta sau 61 ya zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan ta samu martani da dama. DUBAWA ya ga dacewar gudanar da binciken gano gaskiya kan harin na Owo kasancewarsa babban abin tashin hankali da ya shafi iyalai da dama da mabiya darikar ta Katolika da \u2018yan Najeriya baki daya. Wannan lamari&nbsp; an cukurkuda shi da ma danganta shi da wata da\u2019awa mara tushe wato shigar da mahukunta na kasa wajen goyon bayan kisan kiyashi, wannan karfafa gwiwa ce wajen yada labaran da ba haka ba ko jita-jita, abin da ka iya harzuka rikici na addini&nbsp; da jawo daukar ramuwa ta wani bangare da jawo rashin mutuntawa ga bangaren shari\u2019a.&nbsp; Tantancewa Sabanin abin da mai da\u2019awar ke fadi \u201cbabu wanda aka kama da gurfanarwa a gaban shari\u2019a.\u201d Mahukunta sun kama tare da gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a wannan hari. A watan Agusta,2025, mahukunta a Najeriya sun gurfanar da mutane 5 da ake zargi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja saboda alakantasu da harin da aka kai a ranar 5 ga watan Yuni,2022 wadannan mtane da ake zargi kamar yadda aka ba da rahoto sune&nbsp; Idris Omeiza da Al Qasim Idris da Jamiu Abdulmalik da Abdulhaleem Idris da Momoh Otuho Abubakar wadanda suka ce basu aikata laifin komai ba an kuma ci gaba da tsare su (remanded) a wajen jami\u2019an tsaro na farin kaya (DSS). An gurfanar da su a gaban kuliya ne bisa tuhumar aikata laifi na ta\u2019addanci sauran abubuwa da suka biyo baya sun hadar da neman beli da sauran zaman kotu sannan an dage zaman kotun zuwa\u00a0 10 ga Satumba,Sept. 2025 inda anan ne kotu ta hana beli bisa kafa hujjar kasancewarsu barazana ga tsaro. A watan Nuwamba, jami\u2019an na DSS a bayyane sun tabbatar da cewa sun gabatar da wadanda ake zargi da harin na Owo a gaban kuliya, a wani yunkuri na gurfanar da mutanen bisa tuhumar ta\u2019addanci A Karshe Da\u2019awar cewa babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari\u2019a a dangane da harin ta\u2019addancin na Owo wannan ba gaskiya ba ne.Rahotanni da aka tabbatar sun nunar da cewa wadanda ake zargin jami\u2019an tsaro sun kama su kuma an gurfanar da su a gaban babbar kotun shari\u2019a ta tarayya, ana dai shari\u2019a ba kammala ba, don haka wani yace babu abin da ake daga bangare gwamnati wannan kuskure ne ya sabawa abin da yake na zahiri wanda kuma irin hakan na haifar da rura wutar rikici na addini da yada jita-jita.\u00a0\u00a0<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":25882,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4087],"class_list":["post-26184","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6Ok","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4087,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"juliet-buna","display_name":"Juliet Buna","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/image-57.jpeg?fit=1500%2C844&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26184","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=26184"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26184\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":26185,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26184\/revisions\/26185"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/25882"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=26184"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=26184"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=26184"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=26184"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=26184"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}