{"id":26471,"date":"2025-12-06T07:00:00","date_gmt":"2025-12-06T06:00:00","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=26471"},"modified":"2025-12-06T00:49:10","modified_gmt":"2025-12-05T23:49:10","slug":"babu-hukka-kan-ikirarin-wani-mai-amfani-da-instagram-cewa-sinadarin-fluoride-na-sa-yin-furfura-da-wuri","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/babu-hukka-kan-ikirarin-wani-mai-amfani-da-instagram-cewa-sinadarin-fluoride-na-sa-yin-furfura-da-wuri\/","title":{"rendered":"Babu hujja kan ikirarin wani mai amfani da Instagram cewa sinadarin fluoride na sa yin furfura da wuri"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Sinadarin fluoride da ke cikin man goge hakora na jawo furfura a gemu da wuri ga maza.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci:<\/strong> \u0198ARYA CE. Binciken DUBAWA ya gano cewa babu wata huja ta kimiyya, likitanci ko hukumar da ta danganta fluoride ko man goge hakora da farin gashin maza.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Fluoride wani sinadari ne da ake samu a cikin ruwa, \u0199asa, abinci, da kuma yawancin kayan tsaftar hakora. Cibiyoyin kiwon lafiya na duniya irin su <a href=\"https:\/\/www.who.int\/news-room\/fact-sheets\/detail\/oral-health\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar Lafiya ta Duniya<\/a> (WHO) da <a href=\"https:\/\/www.ada.org\/resources\/research\/science-and-research-institute\/oral-health-topics\/toothpastes\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kungiyar Likitocin Amurka<\/a> (ADA) suna nanata cewa fluoride da ke cikin man goge hakora ba mai hatsari ne ba, muddin aka yi amfani da shi yadda ya kamata. Haka kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen rage lalacewar hakora.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewar shafin yanar gizo <a href=\"https:\/\/www.healthline.com\/health\/white-hair#takeaway\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Healthline<\/a>, furfura wani lamari ne na halitta wanda ke fitowa saboda abubuwa kamar: tsarin halitta, shekaru, shiga damuwa, da \u0199arancin wasu bitamin \u2014 musamman B12, ba\u0199in \u0199arfe (iron) da tagulla (copper).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani shafin Instagram mai suna <a href=\"https:\/\/www.instagram.com\/reel\/DRKjW9LDUUK\/?igsh=MTI4YnRvbWRmMXBkdQ%3D%3D\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">northern_vine<\/a> ya yada wani bidiyo (<a href=\"https:\/\/archive.is\/bMVrJ\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">an adana nan<\/a>) inda wani mutum ke cewa yawancin samari ba wai shekaru ne ke kawo musu farin gashi a gemunsu ba, sai dai fluoride daga man goge hakora.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mutumin ya ce, ruwan man goge hakora da yake zuba a gemu lokacin wanke hakora yana shiga gashin gemu ne, kuma shi ke haddasa furfura da wuri.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zuwa ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025, an kalli bidiyon sau 6,991 da an yi martani sau 185.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu masu amfani da Instagram sun karyata ikirarin, wasu kuma sun yi barkwanci akai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani @zumariouss ya rubuta: \u201cFarin gashi halitta ne; ma har \u0257an shekara 12 a gidansu suna da shi, wasu kuma suna kai 50 ba su da ko \u0257aya.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Shi kuwa @mcyareema ya yi raha yana cewa zai fara goge hakora sosai \u201cdomin ya fito da farin gashi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda irin yaduwar bayanan \u0199arya kan lafiya a kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gabatar da bincike don tabbatar da sahihancin ikirarin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta duba bayanan hukumomin lafiya na duniya da suka ha\u0257a da&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.who.int\/teams\/environment-climate-change-and-health\/chemical-safety-and-health\/health-impacts\/chemicals\/inadequate-or-excess-fluoride\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar Lafiya ta Duniya<\/a> (WHO) da <a href=\"https:\/\/www.ada.org\/resources\/ada-library\/oral-health-topics\/fluoride-topical-and-systemic-supplements\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Kungiyar Likitocin Amurka<\/a> (ADA) da <a href=\"https:\/\/www.cdc.gov\/oral-health\/prevention\/about-fluoride.html\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar Ya\u0199i da Cututtuka Masu Ya\u0257uwa<\/a> (CDC) da <a href=\"https:\/\/www.nafdac.gov.ng\/wp-content\/uploads\/Files\/Resources\/Directorate_Resources\/Lab_Services_CDCL\/List-Of-Products-Analysed-In-CDCL-2021.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Hukumar Tantance Inganci Abinci da Magunguna ta Najeriya<\/a> (NAFDAC).<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun gano cewa hukumar ADA ta bayyana cewa yawan amfani sinadarin fluoride a lokacin da hakora ke girma na iya jawo raunin ha\u0199ora, wanda alamunsa suka ha\u0257a da, farin layi a ha\u0199ori, ko \u0199uraje a hakora idan sun tsananta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hukumar CDC kuma ta shawarci iyaye su rika tabbatar da yara sun zubar da man goge hakora ba tare da hadiyewa ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">WHO ta bayyana cewa \u0257aukar dogon lokaci ana amfani da fluoride zai iya jawo raunin ha\u0199ora, da bayyanar fatar dasashi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Amma babu wani rahoto daga wadannan hukumomi da ya nuna cewa sinadarin fluoride na haifar da furfura da wuri.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Ra\u2019ayin Masana<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta tuntubi Aliyu Argungu, masanin lafiyar fata a Asibitin Koyarwa ta Jami\u2019ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, wanda ya bayyana cewa wannan da\u2019awar ba ta da madogara.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cBan taba ganin wani bincike ko wani rahoto da ya nuna fluoride na haddasa farin gashi ba. Kuma ban taba ganin wani mara lafiya da wannan matsalar ta same shi saboda fluoride ba\u201d in ji Likita<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya kara da cewa furfura na faruwa ne saboda yawan shekaru, gado, matsalolin fatar jiki, damuwa, ko kuma shan taba, amma ba fluoride ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Haka kuma wani Farfesa a fannin kimiyyar sinadarai, Sani Gumel na Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana cewa farin gashi wata dabi\u2019a ce ta halitta da mutum zai iya fara samu a ko wane lokaci bayan ya balaga.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cBabu wata hanya ta sinadari ko hujar kimiyya da ta nuna fluoride na haddasa farin gashi. Abubuwan da ke haddasa shi sun shafi tsufa da damuwa da raguwar sinadarin melanin a jiki, ba fluoride.\u201d<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ikirarin cewa sinadarin fluoride daga man goge hakora yana haifar da furfura da wuri ba gaskiya ba ne.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Sinadarin fluoride da ke cikin man goge hakora na jawo furfura a gemu da wuri ga maza. Hukunci: \u0198ARYA CE. Binciken DUBAWA ya gano cewa babu wata huja ta kimiyya, likitanci ko hukumar da ta danganta fluoride ko man goge hakora da farin gashin maza. Cikakken Bayani Fluoride wani sinadari ne da ake samu a cikin ruwa, \u0199asa, abinci, da kuma yawancin kayan tsaftar hakora. Cibiyoyin kiwon lafiya na duniya irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Likitocin Amurka (ADA) suna nanata cewa fluoride da ke cikin man goge hakora ba mai hatsari ne ba, muddin aka yi amfani da shi yadda ya kamata. Haka kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen rage lalacewar hakora. A cewar shafin yanar gizo Healthline, furfura wani lamari ne na halitta wanda ke fitowa saboda abubuwa kamar: tsarin halitta, shekaru, shiga damuwa, da \u0199arancin wasu bitamin \u2014 musamman B12, ba\u0199in \u0199arfe (iron) da tagulla (copper). Wani shafin Instagram mai suna northern_vine ya yada wani bidiyo (an adana nan) inda wani mutum ke cewa yawancin samari ba wai shekaru ne ke kawo musu farin gashi a gemunsu ba, sai dai fluoride daga man goge hakora. Mutumin ya ce, ruwan man goge hakora da yake zuba a gemu lokacin wanke hakora yana shiga gashin gemu ne, kuma shi ke haddasa furfura da wuri. Zuwa ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025, an kalli bidiyon sau 6,991 da an yi martani sau 185. Wasu masu amfani da Instagram sun karyata ikirarin, wasu kuma sun yi barkwanci akai. Wani @zumariouss ya rubuta: \u201cFarin gashi halitta ne; ma har \u0257an shekara 12 a gidansu suna da shi, wasu kuma suna kai 50 ba su da ko \u0257aya.\u201d Shi kuwa @mcyareema ya yi raha yana cewa zai fara goge hakora sosai \u201cdomin ya fito da farin gashi.\u201d Saboda irin yaduwar bayanan \u0199arya kan lafiya a kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gabatar da bincike don tabbatar da sahihancin ikirarin. Tantancewa DUBAWA ta duba bayanan hukumomin lafiya na duniya da suka ha\u0257a da&nbsp; Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Likitocin Amurka (ADA) da Hukumar Ya\u0199i da Cututtuka Masu Ya\u0257uwa (CDC) da Hukumar Tantance Inganci Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC). Mun gano cewa hukumar ADA ta bayyana cewa yawan amfani sinadarin fluoride a lokacin da hakora ke girma na iya jawo raunin ha\u0199ora, wanda alamunsa suka ha\u0257a da, farin layi a ha\u0199ori, ko \u0199uraje a hakora idan sun tsananta. Hukumar CDC kuma ta shawarci iyaye su rika tabbatar da yara sun zubar da man goge hakora ba tare da hadiyewa ba. WHO ta bayyana cewa \u0257aukar dogon lokaci ana amfani da fluoride zai iya jawo raunin ha\u0199ora, da bayyanar fatar dasashi. Amma babu wani rahoto daga wadannan hukumomi da ya nuna cewa sinadarin fluoride na haifar da furfura da wuri. Ra\u2019ayin Masana DUBAWA ta tuntubi Aliyu Argungu, masanin lafiyar fata a Asibitin Koyarwa ta Jami\u2019ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, wanda ya bayyana cewa wannan da\u2019awar ba ta da madogara. \u201cBan taba ganin wani bincike ko wani rahoto da ya nuna fluoride na haddasa farin gashi ba. Kuma ban taba ganin wani mara lafiya da wannan matsalar ta same shi saboda fluoride ba\u201d in ji Likita Ya kara da cewa furfura na faruwa ne saboda yawan shekaru, gado, matsalolin fatar jiki, damuwa, ko kuma shan taba, amma ba fluoride ba. Haka kuma wani Farfesa a fannin kimiyyar sinadarai, Sani Gumel na Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana cewa farin gashi wata dabi\u2019a ce ta halitta da mutum zai iya fara samu a ko wane lokaci bayan ya balaga. \u201cBabu wata hanya ta sinadari ko hujar kimiyya da ta nuna fluoride na haddasa farin gashi. Abubuwan da ke haddasa shi sun shafi tsufa da damuwa da raguwar sinadarin melanin a jiki, ba fluoride.\u201d A Karshe Ikirarin cewa sinadarin fluoride daga man goge hakora yana haifar da furfura da wuri ba gaskiya ba ne.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":26472,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,1571,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-26471","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-fact-check","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-6SX","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/Gemu.png?fit=512%2C341&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26471","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=26471"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26471\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":26474,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/26471\/revisions\/26474"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/26472"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=26471"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=26471"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=26471"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=26471"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=26471"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}