{"id":27077,"date":"2026-01-03T10:10:23","date_gmt":"2026-01-03T09:10:23","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=27077"},"modified":"2026-01-03T10:10:25","modified_gmt":"2026-01-03T09:10:25","slug":"shin-da-gaske-ne-shugaban-kasar-afurka-ta-kudu-ya-bukaci-najeriya-ta-saki-nnamdi-kanu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-da-gaske-ne-shugaban-kasar-afurka-ta-kudu-ya-bukaci-najeriya-ta-saki-nnamdi-kanu\/","title":{"rendered":"Shin da gaske ne shugaban kasar Afurka ta Kudu ya bukaci Najeriya ta saki Nnamdi Kanu?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wani mai amfani da shafin Facebook, <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/profile.php?id=61572217782367&amp;__cft__[0]=AZWJQTZGvcqh09aRbvIDodcf73FJVy_LHDA36MJZttEZMXeSoMoq-FQMah9ba_2MH0dwvey5ST97npRQNuW5rlkZnaYcl2_tMxRDHsblyZX8IXxKsoOdHwV6ir9LZnGcANxQ1abDBOYiyDzWsk-SYqdkBa5L0_-mF9AGffa58boNKg&amp;__tn__=-UC%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">@Celebrity Blogger<\/a>, ya rubuta cewa shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu don samun zaman lafiya a kasar.\u00a0<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci:<\/strong> Karya ce. Shirin DUBAWA ya fahimci cewa babu wata sheda sahihiya da ta tabbatar da wannan da\u2019awa. Bayanan da aka tattara daga dukkanin bangarorin kasashen sun tabbatar da cewa babu inda aka gabatar da wannan bukata.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayanin<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025 shugaban haramtacciyar kungiyar \u2018yan awaren Biafra Nnamdi Kanu, an <a href=\"https:\/\/www.aljazeera.com\/amp\/news\/2025\/11\/20\/nigeria-convicts-separatist-leader-nnamdi-kanu-on-terrorism-charges\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>yanke masa hukunci<\/strong><\/a> bisa laifuka bakwai da aka same shi da su <a href=\"https:\/\/www.cnn.com\/2025\/11\/20\/africa\/nnamdi-kanu-terrorism-conviction-intl\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>masu alaka da ta\u2019addanci <\/strong><\/a>inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a wata kotun Najeriya. Ya dai ki amincewa da daukaka kara, sannan kotu ta fada masa cewa duk wani yunkuri na neman shari\u2019a a wajen Najeriya hakan haramun ne ya saba kundin tsarin mulkin kasa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko bayan yanke wannan hukunci an ci gaba, da <a href=\"https:\/\/www.vanguardngr.com\/2025\/12\/why-i-dont-want-to-stay-in-sokoto-prison-nnamdi-kanu\/amp\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>cece-ku-ce<\/strong><\/a> kan batun, tare da wasu da\u2019awowi da DUBAWA ta <a href=\"http:\/\/dubawa.org\/dir\/videos-of-nnamdi-kanu-in-prison-ai-generated\/\"><strong>fayyace<\/strong><\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da shafin Facebook <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/profile.php?id=61572217782367&amp;__cft__[0]=AZWJQTZGvcqh09aRbvIDodcf73FJVy_LHDA36MJZttEZMXeSoMoq-FQMah9ba_2MH0dwvey5ST97npRQNuW5rlkZnaYcl2_tMxRDHsblyZX8IXxKsoOdHwV6ir9LZnGcANxQ1abDBOYiyDzWsk-SYqdkBa5L0_-mF9AGffa58boNKg&amp;__tn__=-UC%2CP-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Celebrity Blogger<\/strong><\/a> yayi da\u2019awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bukaci a saki Nnamdi Kanu. Mai da\u2019awar ya kara da cewa neman kare kai ba laifi ba ne karkashin dokar kasa da kasa kuma kowa yana da hakki a saurare shi a kotu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wallafar ta kammala da cewa ci gaba da rike Kanu zai iya kara dagula lamura abin da zai zubar da kimar Najeriya a kokarin da ake na samun sulhuntawa.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani bangare na wallafar yayi nuni da cewa&nbsp; \u201cLabari da Dumi-Dumi: Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, yayi kira ga gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu ba tare da sanya wani sharadi ba don samun zaman lafiya a kasar.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya zuwa ranar 7 ga Disamba,2025 wannan wallafa ta samu masu nuna sha\u2019awa wato (Likes) 53 da wadanda suka sake yada labarin su 27 (shares) da masu tsokaci su biyu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Daga cikin masu tsokaci <a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/chibuzo.aku.2025?comment_id=Y29tbWVudDoxMjIxNTE2NzEwNjA3NDA1OTJfMTkyMjY3NTYzMTk5ODQ1MQ%3D%3D&amp;__cft__[0]=AZWJQTZGvcqh09aRbvIDodcf73FJVy_LHDA36MJZttEZMXeSoMoq-FQMah9ba_2MH0dwvey5ST97npRQNuW5rlkZnaYcl2_tMxRDHsblyZX8IXxKsoOdHwV6ir9LZnGcANxQ1abDBOYiyDzWsk-SYqdkBa5L0_-mF9AGffa58boNKg&amp;__tn__=R]-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Chibuzo Aku <\/strong><\/a>yace, \u201c da Allah a sake shi. Shi danfafutuka ne, ya lura cewa Najeriya&nbsp; bata tafiya yadda ya dace shi ya sanya yake fafutuka saboda al\u2019ummarsa.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/web.facebook.com\/profile.php?id=61555337519342&amp;comment_id=Y29tbWVudDoxMjIxNTE2NzEwNjA3NDA1OTJfMjEzODIxNTQ5MzI1Mjg1MQ%3D%3D&amp;__cft__[0]=AZWJQTZGvcqh09aRbvIDodcf73FJVy_LHDA36MJZttEZMXeSoMoq-FQMah9ba_2MH0dwvey5ST97npRQNuW5rlkZnaYcl2_tMxRDHsblyZX8IXxKsoOdHwV6ir9LZnGcANxQ1abDBOYiyDzWsk-SYqdkBa5L0_-mF9AGffa58boNKg&amp;__tn__=R]-R\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>@Master Gold <\/strong><\/a>ya kara da cewa&nbsp; \u201cDa Allah a kyale shi ya tafi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babu tantama Nnamdi Kanu lamarinsa na ci gaba da daukar hankali,inda a lokuta da dama a ke fadin abin da ba haka yake ba a game da shi, munga dacewar gudanar da bincike kan wannan da\u2019awa dukmda cewa babu martani sosai a kanta.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara da bincikar shafin <a href=\"https:\/\/www.thepresidency.gov.za\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Fadar shugan kasa a Afurka ta Kudu<\/strong><\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ciki kuwa har da <a href=\"https:\/\/x.com\/CyrilRamaphosa?s=20\"><strong>sahihin<\/strong><\/a> <a href=\"https:\/\/www.instagram.com\/cyrilramaphosa\/#\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>shafin<\/strong><\/a> Shugaba Cyril Ramaphosa sai babu inda aka ga shugaban na bukatar Najeriya ta saki Nnamdi Kanu&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sannan mun binciki wasu kafofin yada labarai na kasar ta Afurka ta Kudu ciki kuwa har da&nbsp; <a href=\"https:\/\/www.news24.com\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>News24<\/strong><\/a> da <a href=\"https:\/\/www.timeslive.co.za\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>TimesLIVE<\/strong><\/a> da <a href=\"https:\/\/www.ewn.co.za\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>Eyewitness News <\/strong><\/a>(EWN), haka kuma kafafan yada labarai na Najeriya duka cikin wadannan babu inda fadar shugaban aka ga ta bayyana wannan bukata. Babu kuma inda aka ga wani bayani ko tattaunawa ko wallafawa ko wani rahoto sahihi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA a tattaunawa da Lebo Tlhabi, wata fitacciyar \u2018yarjarida a Afurka ta Kudu kan wannan da\u2019awa tace babu tantanma tana bibiyar labarai na siyasar Najeriya ciki kuwa har da batun na Nnamdi Kanu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cTabbas ya kamata kasa ta samu kulawa daga wata takwararta ba kawai don harkar diflomasiya ba don ma zaman lafiyar nahiyar, da duniya da ma al\u2019ummarta. Batun Nnamdi Kanu abu ne da babu wata kasa da za ta sanya bakinta akansa, musamman idan bata da wata bukata a kai, ina tabbatar maka da cewa irin wannan wallafa ana yinta ne don kawai a jawo cece-ku-ce mara dalili a jawo tsana,\u201d a cewarta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ta kara da cewa Afurka ta Kudu na da manyan batutuwa da ke gabanta da kalubale don haka babu wani dalili da ma shugabanta zai kutsa kai cikin al\u2019amuran wata kasa.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tare da taimakon Lebo DUBAWA ya tuntubi Sipho Mbele jami\u2019i mai hulda da kafafan yada labarai a fadar shugaban kasa, mun tuntubi Sipho ta hanyar WhatsApp don neman karin haske amma dai babu wani bayani da aka samu.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun kuma yi kokari na tuntubar <a href=\"https:\/\/www.instagram.com\/governmentza?igsh=d3B2NHAzNWRpYnI3\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\"><strong>shafi<\/strong><\/a> na gwamnatin shima anan babu wata amsa da muka samu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da\u2019awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa yayi kira na a saki Nnamdi Kanu karya ce babu wata hujja da ta tabbatar da haka.&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, @Celebrity Blogger, ya rubuta cewa shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu don samun zaman lafiya a kasar.\u00a0 Hukunci: Karya ce. Shirin DUBAWA ya fahimci cewa babu wata sheda sahihiya da ta tabbatar da wannan da\u2019awa. Bayanan da aka tattara daga dukkanin bangarorin kasashen sun tabbatar da cewa babu inda aka gabatar da wannan bukata. Cikakken Bayanin A ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025 shugaban haramtacciyar kungiyar \u2018yan awaren Biafra Nnamdi Kanu, an yanke masa hukunci bisa laifuka bakwai da aka same shi da su masu alaka da ta\u2019addanci inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a wata kotun Najeriya. Ya dai ki amincewa da daukaka kara, sannan kotu ta fada masa cewa duk wani yunkuri na neman shari\u2019a a wajen Najeriya hakan haramun ne ya saba kundin tsarin mulkin kasa. Ko bayan yanke wannan hukunci an ci gaba, da cece-ku-ce kan batun, tare da wasu da\u2019awowi da DUBAWA ta fayyace. Wani mai amfani da shafin Facebook @Celebrity Blogger yayi da\u2019awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bukaci a saki Nnamdi Kanu. Mai da\u2019awar ya kara da cewa neman kare kai ba laifi ba ne karkashin dokar kasa da kasa kuma kowa yana da hakki a saurare shi a kotu. Wallafar ta kammala da cewa ci gaba da rike Kanu zai iya kara dagula lamura abin da zai zubar da kimar Najeriya a kokarin da ake na samun sulhuntawa.&nbsp; Wani bangare na wallafar yayi nuni da cewa&nbsp; \u201cLabari da Dumi-Dumi: Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, yayi kira ga gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu ba tare da sanya wani sharadi ba don samun zaman lafiya a kasar.\u201d Ya zuwa ranar 7 ga Disamba,2025 wannan wallafa ta samu masu nuna sha\u2019awa wato (Likes) 53 da wadanda suka sake yada labarin su 27 (shares) da masu tsokaci su biyu. Daga cikin masu tsokaci @Chibuzo Aku yace, \u201c da Allah a sake shi. Shi danfafutuka ne, ya lura cewa Najeriya&nbsp; bata tafiya yadda ya dace shi ya sanya yake fafutuka saboda al\u2019ummarsa.\u201d @Master Gold ya kara da cewa&nbsp; \u201cDa Allah a kyale shi ya tafi.\u201d Babu tantama Nnamdi Kanu lamarinsa na ci gaba da daukar hankali,inda a lokuta da dama a ke fadin abin da ba haka yake ba a game da shi, munga dacewar gudanar da bincike kan wannan da\u2019awa dukmda cewa babu martani sosai a kanta. Tantancewa DUBAWA ta fara da bincikar shafin Fadar shugan kasa a Afurka ta Kudu Ciki kuwa har da sahihin shafin Shugaba Cyril Ramaphosa sai babu inda aka ga shugaban na bukatar Najeriya ta saki Nnamdi Kanu&nbsp; Sannan mun binciki wasu kafofin yada labarai na kasar ta Afurka ta Kudu ciki kuwa har da&nbsp; News24 da TimesLIVE da Eyewitness News (EWN), haka kuma kafafan yada labarai na Najeriya duka cikin wadannan babu inda fadar shugaban aka ga ta bayyana wannan bukata. Babu kuma inda aka ga wani bayani ko tattaunawa ko wallafawa ko wani rahoto sahihi. DUBAWA a tattaunawa da Lebo Tlhabi, wata fitacciyar \u2018yarjarida a Afurka ta Kudu kan wannan da\u2019awa tace babu tantanma tana bibiyar labarai na siyasar Najeriya ciki kuwa har da batun na Nnamdi Kanu. \u201cTabbas ya kamata kasa ta samu kulawa daga wata takwararta ba kawai don harkar diflomasiya ba don ma zaman lafiyar nahiyar, da duniya da ma al\u2019ummarta. Batun Nnamdi Kanu abu ne da babu wata kasa da za ta sanya bakinta akansa, musamman idan bata da wata bukata a kai, ina tabbatar maka da cewa irin wannan wallafa ana yinta ne don kawai a jawo cece-ku-ce mara dalili a jawo tsana,\u201d a cewarta. Ta kara da cewa Afurka ta Kudu na da manyan batutuwa da ke gabanta da kalubale don haka babu wani dalili da ma shugabanta zai kutsa kai cikin al\u2019amuran wata kasa.&nbsp; Tare da taimakon Lebo DUBAWA ya tuntubi Sipho Mbele jami\u2019i mai hulda da kafafan yada labarai a fadar shugaban kasa, mun tuntubi Sipho ta hanyar WhatsApp don neman karin haske amma dai babu wani bayani da aka samu.&nbsp; Mun kuma yi kokari na tuntubar shafi na gwamnatin shima anan babu wata amsa da muka samu. A Karshe Da\u2019awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa yayi kira na a saki Nnamdi Kanu karya ce babu wata hujja da ta tabbatar da haka.&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":26610,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"default","_twitter_share_type":"default","_linkedin_share_type":"default","_pinterest_share_type":"default","_linkedin_share_type_page":"default","_instagram_share_type":"default","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4069],"class_list":["post-27077","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-72J","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4069,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"rejoice-taddy","display_name":"Rejoice Taddy","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/12\/image-35.png?fit=976%2C549&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27077","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=27077"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27077\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":27078,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27077\/revisions\/27078"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/26610"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=27077"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=27077"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=27077"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=27077"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=27077"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}