{"id":27617,"date":"2026-02-06T09:17:15","date_gmt":"2026-02-06T08:17:15","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=27617"},"modified":"2026-02-11T08:48:01","modified_gmt":"2026-02-11T07:48:01","slug":"shin-takardun-epstein-sun-tabbatar-da-cewa-an-aika-wani-%c6%99yalle-na-kaaba-zuwa-ga-jeffrey-epstein","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/shin-takardun-epstein-sun-tabbatar-da-cewa-an-aika-wani-%c6%99yalle-na-kaaba-zuwa-ga-jeffrey-epstein\/","title":{"rendered":"Shin Takardun Epstein sun tabbatar da cewa an aika wani \u0199yalle na Ka\u2019aba zuwa ga Jeffrey Epstein?"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wani mai amfani da Facebook ya yi <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/17iMKenbNg\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ikirarin<\/a> cewa sabbin takardun Epstein Files, sun tabbatar da cewa an aika wani bangare na mayafin Ka\u2019aba zuwa ga Jeffrey Epstein a Amurka.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"135\" height=\"57\" data-attachment-id=\"20095\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/live-fact-check-dubawa-nfc-monitor-mis-disinformation-on-edo-governorship-election\/true-1-1-2\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?fit=135%2C57&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"135,57\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"TRUE-1-1\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?fit=135%2C57&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/TRUE-1-1.png?resize=135%2C57\" alt=\"\" class=\"wp-image-20095\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#0aa403\"><strong>Hukunci:<\/strong> Gaskiya ne. Takardun da Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka (DOJ) ta fitar sun ha\u0257a da imel da wasi\u0199u da ke bayyana yadda aka aika mayafin daga Saudiyya zuwa ga Jeffrey Epstein ta hannun wasu \u01b4an kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><a href=\"https:\/\/en.wikipedia.org\/wiki\/Epstein_Files_Transparency_Act\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Epstein Files<\/a> wasu tarin manyan takardu ne da suka ha\u0257a da hotuna, imel, bayanan jiragen sama, bayanan ku\u0257i, da hujjoji da suka shafi gurfanar da mai aikata lalata da yara, Jeffrey Epstein, da kuma wa\u0257anda ke da ala\u0199a da shi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A watan Janairun 2026, Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka ta <a href=\"https:\/\/www.justice.gov\/epstein\/doj-disclosures\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">fitar<\/a> da wani kundin takardu da ke da ala\u0199a da shari\u2019ar a matsayin wani \u0253angare na aiwatar da dokar Epstein Files Transparency Act.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayanan da aka fitar sun&nbsp; \u0199unshi miliyoyin shafuka daga bayanai daban-daban, ciki har da imel tsakanin Epstein da abokansa na kusa, abokan kasuwanci, da masu shiga tsakani a sassa daban-daban na duniya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wani mai amfani da Facebook ya yi <a href=\"http:\/\/archive.today\/gZXwK\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ikirarin<\/a> cewa wasu daga cikin takardun sun nuna an aika wani bangare na Kiswah \u2014 mayafin \u0257aki mai tsarki da ke rufe Ka\u2019aba a Makka \u2014 zuwa gidan Epstein a Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun gano irin wa\u0257annan sakonni da dama a Facebook da X, kamar yadda aka gani a <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/p\/1AcoB8khv9\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/p\/17wDycWLWG\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, da kuma <a href=\"https:\/\/x.com\/i\/status\/2018278363828240700\">nan<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan bayani ya tayar da ce-ce-ku-ce da suka haifar da martani mai zafi a cikin al\u2019ummomin Musulmi, ganin cewa Kiswah ba mayafi ne ka\u0257ai ba, alama ce ta \u0257aki mai tsarki ga Musulmi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ra\u2019ayoyin mutane sun bambanta inda wasu sun \u0199i yarda da yiwuwar a aika irin wannan abu mai tsarki zuwa ga mutum irin Epstein. Wasu kuma sun fara tambayar dalilan da suka sa aka aika irin wannan abu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ka&#8217;Ab Abubakar Zage ya zargi wasu manyan Larabawa da hannu, yana cewa \u201can yi hakan ne da sani da amincewar larabawa\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai Nouradine Daje Gaoudi ya \u0199aryata labarin da ke yawo cewa an aika Kiswah zuwa ga Jeffrey Epstein.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda muhimmancin lamarin, DUBAWA ta yanke shawarar tantance gaskiyar ikirarin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Don tantance ikirarin, DUBAWA ta binciki kundin <a href=\"https:\/\/www.justice.gov\/epstein\/doj-disclosures\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">bayanai<\/a> na Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mun gano cewa imel da takardun suna nan cikin bayanan da DOJ ta fitar, kuma sun bayyana aka aika sakon Kiswah, kamar yadda aka gani a <a href=\"https:\/\/www.justice.gov\/epstein\/files\/DataSet%209\/EFTA01051761.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, <a href=\"https:\/\/www.justice.gov\/epstein\/files\/DataSet%209\/EFTA00571214.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>, da kuma <a href=\"https:\/\/www.justice.gov\/epstein\/files\/DataSet%209\/EFTA00570816.pdf\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">nan<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wadannan sakonnin sun gudana ne tsakanin wata \u2018yar kasuwa \u2018yar Hadaddiyar Daular Larabawa, Aziza Al-Ahmadi, da wani abokin hul\u0257a daga Saudiyya, Abdullah Al-Maari, wanda ya shirya a kai kayan zuwa ga Epstein a Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Takardun sun nuna cewa jigilar ta \u0199unshi sassa uku daban-daban na Kiswah, an rubuta bayanansu dalla-dalla tare da jigilar su ta jirgin British Airways daga Saudiyya zuwa Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai dai, takardun ba su yi bayani kan dalilin aika kayan ba, illa dai sun bayyana yadda aka yi jigilar mayafin da wasikun da suka shafe shi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ikirarin cewa Epstein Files sun tabbatar da cewa an aika mayafin Ka\u2019aba zuwa ga Jeffrey Epstein Gaskiya ne.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa sabbin takardun Epstein Files, sun tabbatar da cewa an aika wani bangare na mayafin Ka\u2019aba zuwa ga Jeffrey Epstein a Amurka. Hukunci: Gaskiya ne. Takardun da Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka (DOJ) ta fitar sun ha\u0257a da imel da wasi\u0199u da ke bayyana yadda aka aika mayafin daga Saudiyya zuwa ga Jeffrey Epstein ta hannun wasu \u01b4an kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Cikakken Bayani Epstein Files wasu tarin manyan takardu ne da suka ha\u0257a da hotuna, imel, bayanan jiragen sama, bayanan ku\u0257i, da hujjoji da suka shafi gurfanar da mai aikata lalata da yara, Jeffrey Epstein, da kuma wa\u0257anda ke da ala\u0199a da shi. A watan Janairun 2026, Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka ta fitar da wani kundin takardu da ke da ala\u0199a da shari\u2019ar a matsayin wani \u0253angare na aiwatar da dokar Epstein Files Transparency Act. Bayanan da aka fitar sun&nbsp; \u0199unshi miliyoyin shafuka daga bayanai daban-daban, ciki har da imel tsakanin Epstein da abokansa na kusa, abokan kasuwanci, da masu shiga tsakani a sassa daban-daban na duniya. Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin takardun sun nuna an aika wani bangare na Kiswah \u2014 mayafin \u0257aki mai tsarki da ke rufe Ka\u2019aba a Makka \u2014 zuwa gidan Epstein a Amurka. Mun gano irin wa\u0257annan sakonni da dama a Facebook da X, kamar yadda aka gani a nan, nan, da kuma nan. Wannan bayani ya tayar da ce-ce-ku-ce da suka haifar da martani mai zafi a cikin al\u2019ummomin Musulmi, ganin cewa Kiswah ba mayafi ne ka\u0257ai ba, alama ce ta \u0257aki mai tsarki ga Musulmi. Ra\u2019ayoyin mutane sun bambanta inda wasu sun \u0199i yarda da yiwuwar a aika irin wannan abu mai tsarki zuwa ga mutum irin Epstein. Wasu kuma sun fara tambayar dalilan da suka sa aka aika irin wannan abu. Ka&#8217;Ab Abubakar Zage ya zargi wasu manyan Larabawa da hannu, yana cewa \u201can yi hakan ne da sani da amincewar larabawa\u201d. Sai dai Nouradine Daje Gaoudi ya \u0199aryata labarin da ke yawo cewa an aika Kiswah zuwa ga Jeffrey Epstein. Saboda muhimmancin lamarin, DUBAWA ta yanke shawarar tantance gaskiyar ikirarin. Tantancewa Don tantance ikirarin, DUBAWA ta binciki kundin bayanai na Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka. Mun gano cewa imel da takardun suna nan cikin bayanan da DOJ ta fitar, kuma sun bayyana aka aika sakon Kiswah, kamar yadda aka gani a nan, nan, da kuma nan. Wadannan sakonnin sun gudana ne tsakanin wata \u2018yar kasuwa \u2018yar Hadaddiyar Daular Larabawa, Aziza Al-Ahmadi, da wani abokin hul\u0257a daga Saudiyya, Abdullah Al-Maari, wanda ya shirya a kai kayan zuwa ga Epstein a Amurka. Takardun sun nuna cewa jigilar ta \u0199unshi sassa uku daban-daban na Kiswah, an rubuta bayanansu dalla-dalla tare da jigilar su ta jirgin British Airways daga Saudiyya zuwa Amurka. Sai dai, takardun ba su yi bayani kan dalilin aika kayan ba, illa dai sun bayyana yadda aka yi jigilar mayafin da wasikun da suka shafe shi. A Karshe Ikirarin cewa Epstein Files sun tabbatar da cewa an aika mayafin Ka\u2019aba zuwa ga Jeffrey Epstein Gaskiya ne.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":27618,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-27617","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-7br","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/Kaaba.jpg?fit=512%2C268&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27617","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=27617"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27617\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":27619,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/27617\/revisions\/27619"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/27618"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=27617"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=27617"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=27617"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=27617"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=27617"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}