{"id":28605,"date":"2026-04-12T05:29:24","date_gmt":"2026-04-12T04:29:24","guid":{"rendered":"http:\/\/dubawa.org\/dir\/?p=28605"},"modified":"2026-04-12T05:32:34","modified_gmt":"2026-04-12T04:32:34","slug":"bidiyon-yanka-wuyan-wasu-da-ake-yadawa-ba-na-yan-mata-da-aka-sace-a-kebbi-ba-ne","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/bidiyon-yanka-wuyan-wasu-da-ake-yadawa-ba-na-yan-mata-da-aka-sace-a-kebbi-ba-ne\/","title":{"rendered":"Bidiyon yanka wuyan wasu da ake yadawa ba na \u2018yan mata da aka sace a Kebbi ba ne"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"has-cyan-bluish-gray-background-color has-background wp-block-paragraph\"><strong>Da\u2019awa:<\/strong> Wani bidiyo da ake yadawa a WhatsApp ya nuna cewa \u2018yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an kashe su ta hanyar yanke&nbsp; wuyansu.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"alignright size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" decoding=\"async\" width=\"132\" height=\"55\" data-attachment-id=\"23856\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/3bn-electric-car-sales-by-ibrahim-traore-false\/false-4-17\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"132,55\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"FALSE-4\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?fit=132%2C55&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/FALSE-4.png?resize=132%2C55\" alt=\"\" class=\"wp-image-23856\" title=\"\"><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p class=\"has-background wp-block-paragraph\" style=\"background-color:#f41216\"><strong>Hukunci:<\/strong> Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon ba shi da ala\u0199a da Najeriya, kuma ana kyautata zaton ya fito daga yankin Afirka ta Tsakiya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Cikakken Bayani&nbsp;<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A yayin da matsalar rashin <a href=\"https:\/\/www.thisdaylive.com\/2025\/11\/20\/we-are-doing-our-best-army-chief-tells-nigerians-over-nations-growing-insecurity\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">tsaro<\/a> ke \u0199ara ta\u2019azzara a Najeriya, wani bidiyo mai tayar da hankali ya fara yawo a WhatsApp, inda ake ikirarin cewa \u2018yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an \u201cyanka su kamar kaji.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 12 ya nuna hotunan kisan gilla masu matu\u0199ar tayar xa hankali, inda ake ganin an kashe wasu mutane.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cikin rubutun da aka saka cikin bidiyon, an ce: \u201cAn sace \u2018yan mata 25 daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi a ranar Lahadi an yanka su kamar kaji\u2026 Gaskiya wannan al\u2019amari ya wuce gona da iri\u2026\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan ikirari na iya janyo tsoro da fushin jama&#8217;a a kafafen sada zumunta, musamman ganin tarihin sace \u0257alibai a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Saboda muhimmancin batun da kuma ha\u0257arin ya\u0257a labarin \u0199arya, DUBAWA ta gudanar da bincike don tantance gaskiyarsa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Tantancewa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta fara ne da nazarin sauti da hoton da ke cikin bidiyon.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bincike ya nuna cewa harshen da ake magana a bidiyon ba Ingilishi ba ne, kuma ba \u0257aya daga cikin manyan harsunan Najeriya ba ne. Don tabbatar da hakan, DUBAWA ta yi amfani da manhajar Google Gemini wajen fassara sautin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sakamakon ya nuna cewa ana amfani da ha\u0257in Arabic da Swahili cikin bidiyon.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u0253angaren Larabci, an ji wani mutum addu\u2019ar bu\u0257e taro a addinin musulunci, da kuma karanta ayar Al-Qur\u2019ani, musamman Suratul Muhammad aya ta 4.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u0253angaren Swahili kuma, mai magana yana bayani ga jama\u2019a yana danganta kisan a matsayin \u201cumarnin addini.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken hotuna ya nuna wasu rashin daidaito. Mayakan da ke cikin bidiyon suna sanye da kakin soja da ba ya kama da na sojojin Nijeriya ko na kungiyoyin da aka sani kamar ISWAP ko \u2018yan bindiga.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-full\"><img data-recalc-dims=\"1\" fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"412\" data-attachment-id=\"28606\" data-permalink=\"https:\/\/dubawa.org\/dir\/bidiyon-yanka-wuyan-wasu-da-ake-yadawa-ba-na-yan-mata-da-aka-sace-a-kebbi-ba-ne\/image-1504\/\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/image-26.jpeg?fit=720%2C412&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"720,412\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"image\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/image-26.jpeg?fit=720%2C412&amp;ssl=1\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/image-26.jpeg?resize=720%2C412\" alt=\"\" class=\"wp-image-28606\" title=\"\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/image-26.jpeg?w=720&amp;ssl=1 720w, https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/image-26.jpeg?resize=300%2C172&amp;ssl=1 300w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em>Hoton bidiyo da aka za\u0199ulo<\/em><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan ya nuna cewa bidiyon ba a Najeriya ba ne.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An sha danganta kungiyar <a href=\"https:\/\/main.un.org\/securitycouncil\/en\/sanctions\/1533\/materials\/summaries\/entity\/allied-democratic-forces-%28adf%29\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">ADF<\/a> da ke amfani da Swahili wajen ya\u0257a bidiyoyin farfaganda tare da aiwatar da munanan hare-hare ciki har da yankan mutane a yankunan Beni da Ituri.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Binciken masana tsaro daga Cibiyar Ya\u0199i da Ta\u2019addanci ta Jami\u2019ar Sojojin Amurka da ke West Point ya dade yana <a href=\"https:\/\/ctc.westpoint.edu\/the-rising-threat-to-central-africa-the-2021-transformation-of-the-islamic-states-congolese-branch\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">danganta<\/a> irin wadannan alamu da \u0199ungiyar ADF, wadda ke aiki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da wasu sassan Afirka ta Tsakiya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Babu hujjar kisan dalibai a Kebbi<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Don tabbatar da ikirarin sace daliban, DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi a Google kan lamarin da ake magana a Maga, Jihar Kebbi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rahotanni sun tabbatar cewa an sace daliban a ranar 17 ga Nuwamba, 2025 a makarantar mata GGCSS, Maga, amma daga baya an ce an <a href=\"https:\/\/www.theguardian.com\/world\/2025\/nov\/25\/nigerian-schoolgirls-rescued-after-mass-abduction-in-kebbi\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">kubutar<\/a> da su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Rahotanni sun nuna cewa an sako daliban a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, kuma an <a href=\"http:\/\/channelstv.com\/2025\/11\/26\/military-hands-over-24-rescued-maga-schoolgirls-to-kebbi-gov\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">mika<\/a> su ga gwamnati, wanda hakan ya sabawa ikirarin cewa an kashe su.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">DUBAWA ta kuma tuntubi <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/1CNmtMsazM\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Rundunar \u2018Yan Sandan Jihar Kebbi<\/a> ta hannun Kakakinta, <a href=\"https:\/\/www.facebook.com\/share\/1KhDLxpK4U\/\" target=\"_blank\" rel=\"noopener\">Bashir Usman<\/a>, wanda ya tabbatar cewa babu wani rahoton kisan daliban da aka sace a jihar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u201cDalibai mata 25 da aka sace a Maga an sako su kuma an hada su da iyalansu tun shekarar 2025\u201d, in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>A Karshe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bidiyon da ake yadawa a WhatsApp da ke ikirarin cewa an yanka dalibai mata 25 da aka sace a Maga, Jihar Kebbi, karya ne.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Da\u2019awa: Wani bidiyo da ake yadawa a WhatsApp ya nuna cewa \u2018yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an kashe su ta hanyar yanke&nbsp; wuyansu. Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon ba shi da ala\u0199a da Najeriya, kuma ana kyautata zaton ya fito daga yankin Afirka ta Tsakiya. Cikakken Bayani&nbsp; A yayin da matsalar rashin tsaro ke \u0199ara ta\u2019azzara a Najeriya, wani bidiyo mai tayar da hankali ya fara yawo a WhatsApp, inda ake ikirarin cewa \u2018yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an \u201cyanka su kamar kaji.\u201d Bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 12 ya nuna hotunan kisan gilla masu matu\u0199ar tayar xa hankali, inda ake ganin an kashe wasu mutane. A cikin rubutun da aka saka cikin bidiyon, an ce: \u201cAn sace \u2018yan mata 25 daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi a ranar Lahadi an yanka su kamar kaji\u2026 Gaskiya wannan al\u2019amari ya wuce gona da iri\u2026\u201d Wannan ikirari na iya janyo tsoro da fushin jama&#8217;a a kafafen sada zumunta, musamman ganin tarihin sace \u0257alibai a Najeriya. Saboda muhimmancin batun da kuma ha\u0257arin ya\u0257a labarin \u0199arya, DUBAWA ta gudanar da bincike don tantance gaskiyarsa. Tantancewa DUBAWA ta fara ne da nazarin sauti da hoton da ke cikin bidiyon. Bincike ya nuna cewa harshen da ake magana a bidiyon ba Ingilishi ba ne, kuma ba \u0257aya daga cikin manyan harsunan Najeriya ba ne. Don tabbatar da hakan, DUBAWA ta yi amfani da manhajar Google Gemini wajen fassara sautin. Sakamakon ya nuna cewa ana amfani da ha\u0257in Arabic da Swahili cikin bidiyon. A \u0253angaren Larabci, an ji wani mutum addu\u2019ar bu\u0257e taro a addinin musulunci, da kuma karanta ayar Al-Qur\u2019ani, musamman Suratul Muhammad aya ta 4. A \u0253angaren Swahili kuma, mai magana yana bayani ga jama\u2019a yana danganta kisan a matsayin \u201cumarnin addini.\u201d Binciken hotuna ya nuna wasu rashin daidaito. Mayakan da ke cikin bidiyon suna sanye da kakin soja da ba ya kama da na sojojin Nijeriya ko na kungiyoyin da aka sani kamar ISWAP ko \u2018yan bindiga. Hoton bidiyo da aka za\u0199ulo Wannan ya nuna cewa bidiyon ba a Najeriya ba ne. An sha danganta kungiyar ADF da ke amfani da Swahili wajen ya\u0257a bidiyoyin farfaganda tare da aiwatar da munanan hare-hare ciki har da yankan mutane a yankunan Beni da Ituri. Binciken masana tsaro daga Cibiyar Ya\u0199i da Ta\u2019addanci ta Jami\u2019ar Sojojin Amurka da ke West Point ya dade yana danganta irin wadannan alamu da \u0199ungiyar ADF, wadda ke aiki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da wasu sassan Afirka ta Tsakiya. Babu hujjar kisan dalibai a Kebbi Don tabbatar da ikirarin sace daliban, DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi a Google kan lamarin da ake magana a Maga, Jihar Kebbi. Rahotanni sun tabbatar cewa an sace daliban a ranar 17 ga Nuwamba, 2025 a makarantar mata GGCSS, Maga, amma daga baya an ce an kubutar da su. Rahotanni sun nuna cewa an sako daliban a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, kuma an mika su ga gwamnati, wanda hakan ya sabawa ikirarin cewa an kashe su. DUBAWA ta kuma tuntubi Rundunar \u2018Yan Sandan Jihar Kebbi ta hannun Kakakinta, Bashir Usman, wanda ya tabbatar cewa babu wani rahoton kisan daliban da aka sace a jihar. \u201cDalibai mata 25 da aka sace a Maga an sako su kuma an hada su da iyalansu tun shekarar 2025\u201d, in ji shi. A Karshe Bidiyon da ake yadawa a WhatsApp da ke ikirarin cewa an yanka dalibai mata 25 da aka sace a Maga, Jihar Kebbi, karya ne.<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":28607,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"hannibal_claim_source":"","hannibal_source_label":"","hannibal_card_color":"blue","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","_wpscppro_dont_share_socialmedia":false,"_wpscppro_custom_social_share_image":0,"_facebook_share_type":"","_twitter_share_type":"","_linkedin_share_type":"","_pinterest_share_type":"","_linkedin_share_type_page":"","_instagram_share_type":"","_medium_share_type":"","_threads_share_type":"","_google_business_share_type":"","_bluesky_share_type":"","_mastodon_share_type":"","_selected_social_profile":[],"_wpsp_enable_custom_social_template":false,"_wpsp_social_scheduling":{"enabled":false,"datetime":null,"platforms":[],"status":"template_only","dateOption":"today","timeOption":"now","customDays":"","customHours":"","customDate":"","customTime":"","schedulingType":"absolute"},"_wpsp_active_default_template":true},"categories":[123,3137,2451],"tags":[],"verdict":[],"ppma_author":[4439],"class_list":["post-28605","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-mainstream","category-african-languages","category-hausa"],"jetpack_shortlink":"https:\/\/wp.me\/p8R6dE-7rn","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"authors":[{"term_id":4439,"user_id":0,"is_guest":1,"slug":"ukashatu-wakili","display_name":"Ukashatu Wakili","avatar_url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/?s=96&r=g","author_category":"","user_url":"","last_name":"","first_name":"","job_title":"","description":""}],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/dubawa.org\/dir\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/wakili.jpg?fit=512%2C288&ssl=1","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/28605","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=28605"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/28605\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":28608,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/28605\/revisions\/28608"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media\/28607"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=28605"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=28605"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=28605"},{"taxonomy":"verdict","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/verdict?post=28605"},{"taxonomy":"author","embeddable":true,"href":"https:\/\/dubawa.org\/dir\/wp-json\/wp\/v2\/ppma_author?post=28605"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}