African LanguagesHausa

Duk abubuwan da ya kamata a sani dangane da taken kasar da aka fara amfani da shi yanzu

Getting your Trinity Audio player ready...

A ’yan makwannin da suka gabaci 29 ga watan Mayun 2024, ba’a ga jama’a suna dokin zagayowar bukukuwan da ke karrama Ranar Dimokiradiyya ta ‘yan Najeriyar kamar yadda aka saba ba. Wannan hakan ne saboda an sauya ranar gudanar da bukin a karkashin gwamnatun Muhammadu Buhari daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni dan martaba M.K.O Abiola wanda ya kamata a ce ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993. Haka nan kuma a maimakon dokin, a wannan karon an yi ta jita-jitar da aka yi ta yayatawa na cewa za’a sauya taken kasa ne zuwa tsohuwar da aka fara da ita “Nigeria, We Hail Thee” ta gamu da shakku da mamaki

‘Yan Najeriya da dama sun gaza fahimtar yadda wannan bangaren kasar mai cike da tarihi zai kasance abin da za’a sauya a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin da suka fi wannan mahimmanci, kamar yanayin tabarbarewar tattalin arziki da zamantakewar kasar. To sai dai tun kafin a kai ko’ina suka lura cewa fa babu gudu, babu ja da baya domin da wayewar garin 29 ga watan Mayu kowa ya tashi ya gamu da abin da ke zahiri: Jita-jitar gaskiya ne. Shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu ya sa hannu kan kudurin dokar taken kasa na 2024 kuma ya zama doka. Sobada haka taken Najeriya ta koma wadda aka rika rairawa kafin ‘yancin kai a hukumance. 

A bayam taken Najeriya ya fara ne da “Arise, O Compatriots,” kuma a shekarar 1978 aka fara amfani da shi – taken mai shkaru 46 yanzu, mutane biyar suka rubuta wadanda suka hada da John A. Ilechukwu, Eme Etim Akpan, B.A. Ogunnaike, Sotu Omoigui, da P.O. Aderibigbe– ya kuma kasance kira ne ga hadin kan kasa, kishin kasa da aiki tare wajen gina babbar kasa bayan bala’in shekaru uku na yakin basasar da aka kammala a shekarar 1970. Kafin “Arise, O compatriots,” taken da ake amfani da shi, “Nigeria, We Hail Thee,” shi ne aka yi amfani da shi daga lokacin da aka sami ‘yancin kai a shekarar 1960 har zuw ashekarar 1978. Wannan taken wanda ma’aikatan mulkin mallakar Burtaniya,  Lillian Jean Williams da Frances Berda suka tsara suka kuma rubuta ya nuna alfahari da kyakyawar fatan kasar a shekarunta na farko bayan  ta sami ‘yancin kai.

Kalaman taken

Ga kalaman da ake fada a taken da ake amfani da shi yanzu,

 “Nigeria, We Hail Thee:”

Nigeria we hail thee,

Our own dear native land,

Though tribe and tongue may differ,

In brotherhood we stand,

Nigerians all are proud to serve

Our sovereign Motherland.

Our flag shall be a symbol

That truth and justice reign,

In peace or battle honoured,

And this we count as gain,

To hand on to our children

A banner without stain.

O God of all creation,

Grant this our one request,

Help us to build a nation

Where no man is oppressed,

And so with peace and plenty

Nigeria may be blessed.”

Martanonin Jama’a

A watan Mayu aka fara yunkurin sauya taken sadda aka fara gabatar da kudurin dokar kafin nan da nan ya sami amincewar duka majalisun tarayyar guda biyu. ‘Yan majalisar sun jaddada mahimmancin sake saita alkiblar kasar da tarihinta tare da al’adunta na asali. Ya wuce karatu na farko da na biyu duk a ranar 23 ga watan Mayun 2024, bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kira da a yi zabe a kan shi kafin ya tura shi zuwa kwamitocin Shari’a, Hakkin dan Adam, Al’amuran Sharia da harkokin cikin gida dan daukar sauran matakan da doka ta tanadar. To sai dai, amincewar da shugaban kasa ya yi da dokar – wuni guda bayan da ta wuce karatu na uku a Majalisar Dokoki — ya tayar da damuwa ganin cewa ko kundin tsarin mulki ta tanadi da a jira har zuwa kwanaki 30 bayan dokar ta wuce karatu na uku kafin a bayar da amincewa na karshe.

Tsakanin ‘yan majalisar,  sun nuna cewa tun da dadewa ya kamata a yi wannan sauyin inda wadansun su ke da’awar cewa taken mai shekaru 46 bai bayyana irin hadin kan da ake bukata dan tabbatar da daidaito a irin rikice-rikicen da ake fama da su masu tayar da hankali. Sauya taken ke nan abu ne da ake gani sai sake jaddada hadin kai da asalin da ke tabbatar da ‘yan kasa a matsayin tsintsiya madaurinki daya kuma abin alfahari.

To sai dai da yawa na nuna damuwa dangane da yawan kudin da za’a kashe wajen aiwatar da wannan sauyin, inda suke mahawarar cewa gara a yi amfani da wannan kudin a wani wurin da aka fi bukata a wannan lokacin da kusan kowa ke cikin wani hali na ha’ula’i. Daya dagani cikin mahimman kwatancen da ake mi shi a soshiyal mediya shi ne rashin sanin ya kamatan gwamnati.  Kusan wannan ne ra’ayin da mutane da yawa suka bayyana, har da manyan ‘yan Najeriya irin su Reno Omokri da Oby Ezekwesili. KO da shi ke al’ummar kasa da kasa ta yi tsit ba ta ce komai ba tun bayan wucewar kudurin dokar.

Gwamnatin ta kaddamar da gangamin da zai koya wa ‘yan kasa kalaman da yadda ake raira taken da ma mahimmancin shi dan ganin cewa mutane sun amince da shi. Shugaban Hukumar Wayar da Kan ‘Yan Kasa Malam Lanre Issa-Onillu ya umurci duka ma’aikatan hukumarsa da ke kananan hukumomin kasar 774 da su bayar da kai wajen haddace sabon taken kafin litinin uku ga watan Yunin 2024 kamar yadda wata sanarwa mai sa hannun  mataimakin darektan da ke hulda da ‘yan jarida, Paul Odeniyi, ya bayyana, a matsayin wani bangare na yunkurin ganin sabon taken ya shiga harkokin yau da kullun na ‘yan kasa. Daga yanzu za’a fara amfani da wannan taken lokacin duk wasu shirye-shirye da bukuwan kasa, wadanda suka hada da wasanni da kuma ayyukan kasa da kasa bayar da shugaba Tinubu ya kai ziyara majalisar dokoki ranar 29 ga watan Mayu, inda aka raira sabon taken. 

A karshe

Shawarar sauya taken Najeriya ya bi duka dokokin da aka tanadar, duk da cewa an yi gaggawa wajen fara amfani da shi, wato tun ma kafin a sami hadin kan kasa da irin fadakarwar da ya kamata, yiwuwar raba kai sakamakon kalaman da ke cikin taken ya yi haifar da rashin gamsuwa da shakku tsakanin ‘yan kasa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button