African LanguagesHausa

Duk da sabuwar dokar Laberiya mai takardar wata kasa ban da ta Laberiyar ba zai iya neman kujera a majalisun wakilai da na dattawa ba

Zargi: ‘Yan Laberiyan da ke da halatattun takardun ‘yan kasa na kasashe biyu za su iya tsayawa takara dan samun kujeru a majilaisun wakilai da na dattawa a kasar.

Duk da sabuwar dokar Laberiya mai takardar wata kasa ban da ta Laberiyar ba zai iya neman kujera a majalisun wakilai da na dattawa ba

Babu inda dokokin kasar su ka tanadi bai wa masu takardun ‘yan kasa na kasashe biyu damar tsayawa takara don neman kujerua a majalisar wakilai da na dattawa

Cikakken bayani

Bayi wadanda da su ka sami ‘yancin kansu daga wadanda su ka saye su a Amurka ne suka girka kasar Laberiya a shekarar 1847 a matsayin wata “mafaka ko masauki na ‘yantattun mutane masu bakar fata.” Kundin tsarin mulkin kasar ya yi amfani da irin kalaman wancan lokacin wajen kwatanta masu bakar fata inda ya ce mutanen da suka kasance “Negro ko kuma masu zuri’a Negro.” A nan Negro kalmar da ta ke nufin mutun mai bakar fata ke nan.

Na tsawon shekaru da dama yanzu matsalar wadanda ke da takardun ‘yan kasa a kasashe biyu ke kasancewa babbar mahawara a kasar tun bayan yakin duniya. Wannan ya kasance haka ne domin lokacin da kasar ta yi fama da yakin basasa, ‘yan Laberiya da yawa suka bar kasar zuwa wadansu kasashen dan samun mafaka musamman a kasashen Turai da Amurka inda daga baya kuma suka dauki takardun zama ‘yan kasa a wadannan kasashen da suka ba su mafakar bisa dalilai daban-daban.

Dokar ta yi tanadin sharuddan da suka bayyana cikakken dan kasa wadda ake kira da turanci Old alien and Nationality Law ya ce. “ Yaro/yarinya wanda ya kasance dan Laberiya bisa tanadin karamin sakin layi (b) wannan sashen zai rasa matsayin shi na dan kasa muddin bai zauna a Liberiya a mafi yawan rayuwarsa ba, sai dai idan kafin ya cika shekaru 23 na haihuwa ya je gaban jakadan Laberiya ya yi rantsuwar mubaya’a ga jamhuriyar Laberiyar wanda ake bukata idan har mutun na so ya tabbatar da matsayin shi na dan kasa.

Wannan dokar ta kuma kara da cewa “(a) Mutumin da ya kasance mai bakar fatam ko kuma tsatson bakake, wanda aka haifa a Laberiya wanda kuma ke karkashin dokokin kasar. (b) Mutumin da aka haifa a wajen Liberiya wanda mahaifinsa (i) an haife shi a Laberiya; (ii) Dan Laberiya ne a lokacin da aka haifi dan, kuma (iii) ya zauna a Laberiya kafin lokacin da aka haifi yaron/yarinyar.”

Sadda ya hau karagar mulkin kasar Laberiya a shekarar 2018, Shugaba George Manneh Weah yayin da ya ke jawabinsa na farko ya ce kundin tsarin mulkin kasar na nuna wariya, kuma ba shi mahimmanci sa’annan kuma bai dace da kasar ba dan haka ya yi alkawarin cire dokar da ta hana baki zuwa su zama cikakkun ‘yan kasa.

Matsayarsa ta sake samun karfi a shekarar 2019 lokacin da aka yi wata shari’ar da babban kotun Laberiyar ta yanke hukuncin cewa kasancewa dan kasa ‘yanci ne da ba za’a iya sokewa ba tare da an je kotu ba. To sai dai, wasu sun yi imanin cewa akwai ‘yan Laberiyar da ke da takardun fasfo na kasashe biyu a boye musamman masu hannu da shuni.

Bacin mahimmancin shari’ar, hukuncin da aka yanke bai bai wa ‘yan Laberiya ‘yancin daukar fasfon guda biyu ba.

Dan haka an cigaba da gwagwarmayar samar da dokar da za ta baiwa ‘yan kasa ‘yancin daukar takardun wata kasar daura da ta su inda mazauna kasashen waje su ka taka muhimmiyar rawa. Bayan an shafe shekaru ana jayayya har ma da kuri’ar jin ra’ayin da ta tanadi a yi watsi da dokar dokar Dual Citizenship a watan Disemban 2020, yanzu kasar ta amice ‘yan kasar su dauki fasfo biyu a sabuwar dokar da ake kira Dual Citizens 2022.

To sai dai har yanzu ana jayayya dangane da irin ‘yancin da ya kamata a baiwa masu amsa kasashe biyun. Lokacin wani shirin da aka watsa a gidan rediyon Okay 99.5 FM ranar laraba 10 ga watan Ogosta, 2022, Dixon Seboe wakilin gundumar Montserrado ya yi zargin cewa a karkashin dokar da aka yi wa kwaskwarima wato dokar Old Aliens and Nationality Law of Liberia, masu takardun kasashe biyu za su iya tsayawa takarar neman kujerun ‘yan majilasar dokoki da na dattawa amma ba za’a iya zaben su a matsayin kakakin majalisar dokoki ko kuma ma jagirar majalisar dattawan ba.

Wannan zargin ya bulla a wajen minti 14 na shirin rediyon wanda aka sa kai tsaye a shafi Facebool inda mutane fiye da dubu biyu su ka kalla wasu 150 kuma su ka yi tsokaci a kai. Wannan shirin na daya daga cikin wadanda ‘yan Liberiya su ka fi sauraro.

Tantancewa

Ganin yadda batun ke tattare da sarkakiya na tsawon shekaru da dama yanzu da ma yadda ya ke cigaba da daukar hankali sakamakon dokar da aka kwaskware kwanann ne ya DUBAWA ta dauki matakin tantance zargin da Dixon Seboe ya yi.

Wanda ya tantance wannan labarin ya fara da yin la’akari da tanade-tanaden wannan dokar da ake neman sauyawa. Dokokin na ainihi sun kunshi Kashi na III Babu na 20, sashe na 20.1; Babi na 21, sassan 21.30, 21.31, 21.51, da 21.52 da Babi na 22, Sassan 22.1, 22.1 da 22.4 na Aliend and Nationality Law of the Liberian Code of Law Revised Vol.II

Daga nan sai DUBAWA ta nemi wanda aka kwaskware kafin majalisa ta amince da shi domin gano ko zargin wakilin gaskiya ne.

Ana iya samun kadan daga cikin dokar da aka kwaskware a cikin wani rahoton da aka yi wanda ya yi amfani da sassan da suka fi mahimmanci ga mahawarar da ake yi kamar haka:

“Dan Laberiyar da ke takardun wata kasa ba zai iya tsayawa takarar a wani gurbin siyasa ba muddin yana rike da takardun wata kasa ta daban banda Laberiya,” a cewar majalisar dokoki

“Idan mutumin na so ya yi takara, dole sai ya yi watsi da takardun dayan kasar akalla shekara guda kafin ya nemi tsayawa takarar da Hukumar Zabe ta Kasa ya kuma nuna ma ta hujjar cewa ya yanke dangantaka da kasar sa’anan ya bayyana haka a kotun Laberiya”

“Haka nan kuma mutumin da ke rike da izinin kasancewa dan kasa a wata kasa daban ban da Laberiya ba zai iya samun mukamin gwamnati a ma’aikatar Kudi da Tsare-Tsare, da Ma’aikatar Tsrao da ma gwamnan babban bankin kasar ta Laberiya.”

Kamar yadda mu ka gani yanzu dokar ta hana masu izinin ‘yan kasa a kasashe biyu takara da ma rike mukaman gwamnati a fannonin kudi, tsaro da babban bankin kasar.

Kafafen yada labarai da jaridu sun yi sharhi sosai dangane da kwaskwarimar da aka yi wa dokar wandanda za’a iya samu a shafuka daban-daban.

A Karshe

Binciken da DUBAWA ta yi dangane da zargin da dan majalisa Dixon Seboe ya yi ya nuna cewa yayin da dokar ta halatta wa ‘yan Laberiya samun izinin kasancewa ‘yan kasa a wadansu kasashen banda Laberiya,  ta haramta musu yin takara ko kuma ma kasancewa a mukamai  masu mahimmanci da sarkakiya a kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button