Fasahar AI aka yi amfani da wajen hada bidiyon dake nuna yadda sojoji ke faretin wasu maharan da suka kama a Arewacin Najeriya

Video showing foreign soldiers parading bandits in northern Nigeria, AI-generated
Hoton dakarun AmurkaAsalin hoton: The Cable
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Micah Ado a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo na yadda wasu sojoji suka kama mahara a wani kauye dake Arewacin Najeriya.

Fasahar AI aka yi amfani da wajen hada bidiyon dake nuna yadda sojoji ke faretin wasu maharan da suka kama a Arewacin Najeriya

Hukunci: Karya ce. DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da fasahar AI wajen hada bidiyon sannan abin da bidiyon ke nunawa na yadda wasu bakin sojoji suka kama mahara a Arewacin Najeriya karya ne. babu gidan jaridar da ta buga labari game da haka sannan jami’an tsaro basu fitar da sanarwa game da haka ba.

Cikakken Bayani  

A ranar 28 ga Agusta 2026 Micah Ado a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo mai tsawon sakan 10 da ke nuna yadda wasu sojoji baki suka kama wasu mutane da ake zargin mahara ne a wani wuri da ba a sani ba.

Da’awa da (aka saka a nan) ya ce “Abun ya faru fa”.  

Bidyon ya nuna maharan a durkushe sannan ga bindigoginsu da sauran makaman su an jera su a gaban su. Wasu sojoji na tsaye bayan maharan sannan da wani soja bature na magana yana Kallon kamara.

Sojan ya ce “Barka, rukunin sojojin mu yau sun kama mahara mutum 10 a wani kauye a Arewacin Najeriya. Bindigogin da sauran makaman maharan na jere a gaban su. Sun mika wuya bayan batakashin da suka yi da sojoji. Babu farin hulan da ya ji rauni. Za a damkasu hannun hukumomin Najeriya domin daukan mataki nan gaba…”

Bidiyon na nuna cewa bakin sojoji sun kai farmaki a Arewacin Najeriya, an kama su sannan an damka su hannun hukumomin Najeriya.

An hada wasu bidiyo biyu tare da wannan bidiyon inda daya na nuna wani mutum dauke da kamara sannan daya ya nuna wani dan kungiyar kare hakkin dan adam kuma dan soshial mediya Martins Vincent Otse da aka fi sani da sunan ‘VeryDarkMan (VDM).

Zuwa ranar 1 ga Satumba 2026 wannan da’awar da aka saka a Facebook ya nuna mutum 158,000 sun kalli bidiyon, 1,600 sun nuna Alamar ganin bidiyon, 160 sun mai da martani da 423 sun sake wallafa bidiyon.

Wasu mutane a Facebook sun nuna alamun amincewa da bidiyon a matsayin da gaske hakan ya faru.

Wani Bassey Bigger ya rubuta cewa “Ku gama da su kawai kada ku bari ya yi nisa”, sannan Stanley Obasi ya alakanta wadannan mutane a matsayin ‘Yan ta’adda musulmai”.

Wani Emmanuel Chuks y ace “Ku daina yaudaran mu, idan har kuna so ku tallafa wa Najeriya ku tallafa domin mutane na mutuwa”.

Ganin halin tabarbarewar tsaron da ake fama da shi da yadda bidiyon ya jawo ra’ayin mutane ya sa DUBAWA ta gudanar bincike.

Tatancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike game da bidiyon domin samin Karin bayani game da kama maharani da bakin sojoji suka yi a Arewacin Najeriya inda sakamakon ya nuna babu labarin da aka rubuta game da haka musamman a lokacin da aka wallafa bidiyon.

Dubawa da bincika shafin yanar gizon hadikwatan tsaron Najeriya da na rundunar sojin Najeriya domin ganin ko sun fitar da sanarwa game da haka amma bata gani ba.

Yayin da rundunar sojin kasar Amurka ke aiki a Najeriya domin taimakawa wajwn inganta tsaron kasar nan a tare da amincewar rundunar sojin Najeriya karkashin Shirin AFRICOM Hedikwatan tsaron Najeriya da  na Amurka da AFRICOM sun tabbatar cewa tallafin da sojojin Amurka ke badawa bai shafin kai wa mahara farmaki ba.

Duk da haka DUBAWA ta kara amfani da wasu matakan gudanar da bincike domin kara tattance bidiyon.

Gidan jaridar ta yi amfani da na’uran ‘Reverse-image searches’ da Google Lens da Yandex wajen tattance bidiyon inda sakamakon ya nuna rashiniya tabbarar da inda aka samu bidiyon.

Gidan jaridar ta yi amfani da na’urar AI guda uku inda daya daga cikin na’urorin FauxLens alamun an yi amfani da na’urar AI kusan kashi 95%.

Gidan jaridar ta yi amfani da na’urar VigilAI da ya nuna “alamun yin amfani da na’urar AI” kusan kashi 97%.

Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa an yi amfani da dabarinyanar gizo na zamani wajen hada bidiyon.

DUBAWA ta yi amfani da na’urar AI Video Detector domin kara tattance bidiyon inda sakamakon ya nuna kashi 61% da kashi 64% na an yi amfani da dabarun yanar gizo wajen hada bidiyon.

 

Video showing foreign soldiers parading bandits in northern Nigeria, AI-generated

 

A takaice dai na’urorin AI uku da aka yi amfani da su wajen tattance bidiyon sun nuna bidiyon karya ne dake nuna ayyukan sojoji.

A karshe

Bidiyon dake nuna bakin sojoji sun kama mahara a Arewacin Najeriya yaudara ce. Sakamakon binciken yanar gizo ya tabbatar cewa and yi amfani da dabarun yanar gizo wajwn hada bidiyon sannan rundunar sojiji da gidajen jaridu duk sun tabbatar cewa bidyion na karya ne.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).