African LanguagesHausa

Fayyace zargin cewa gwajin cutar dajin mahaifa, na matan da ke kwanciya da maza da yawa ne kadai

Labarai marasa tushe dangane batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ba sabon abu ba ne, amma na yi matukar mamaki da na ji cewa wai gwajin kwayoyin halittan da ke mahaifar ma ce dan tantance ko tana dauke da cutar daji wanda aka fi sani da “Pap smear” da turanci, ba kowace mace ke yi ba, sai wadda ke kwanciya da maza da yawa.

Na sami wannan labarin ne yayin da na ke tattaunawa da kawa ta ina fada ma ta cewa ya kamata in daina jinkiri in sa rana in je in yi nawa. Daga nan ne martanin da ta mayar mun ya bani mamaki sosai. Kawai sai ta kalle ni ta ce tana mamakin wai ina so in je in yi irin wannan gwajin duk da cewa ina da aure. A cewarta “Irin wannan gwajin ba na irin wadanda ba su da kamun kai ba ne? Ai ke baki bukata.”

Ta yaya rashin kamun kai ko kuma ma yin lalata da maza da yawa ya ke da dangantaka da wannan gwajin mai mahimmanci ga mata wanda ke da lokutan da ya kamata a ce an rika yi.

Ganin yadda kawa ta wadda ke da ilimi ma ke nan ta ke da irin wannan ra’ayin ya sa ni tunanin cewa mai yiwuwa akwai mata da yawa irin ta wadanda suka yi imanin da hakan kuma suna can suna yawo ba tare da sanin cewa wannan irin tunanin zai iya kai su ga hallaka ba. Wajibi ne mutane su sami bayanai masu nagarta dan su iya yanke shawarwari masu inganci dangane da kiwon lafiyarsu. Wannan  ne ya sa muka dauki nauyin yin wannan binciken dan tantance gaskiya.

Tantancewa

Shin mene ne ma Pap smear?

Pap smear, ko kuma abun da ake kira gwajin Pap ko ma sunan shi na kimiyya Papanicolaou test, wani gwaji ne mara wuya wanda ake yi a al’aura da mahaifa dan a duba a gani ko mutun na da kwayoyin da ke janyo cutar daji ko kuma ma kwayoyin na sauyawa ta yadda za su iya kai wa ga cutar dajin mahaifa

Cutar dajin mahaifa kan fara ne daga cikin mahaifar kuma sau daya a kan gano shi a mata sadda ya riga ya makara saboda shi baya bayyana alamunsa sai a lokacin da ya riga ya yi nisa. 

Yawancin wadanda ke kamuwa da cutar (kashi 99 cikin 100) na da alaka da cututtuka masu hadari. Kwayar cutar da aka fi sani da HPV na daya daga cikin cututtukan da ake samu ta hanyar jima’i. 

Idan har alamun cutar dajin mahaifa suka bayyana, yawanci babu wanda kan yi tunanin cutar daji ne, wasu sukan zaci ko jinin haila ne ko kuma dai irin cututtukan nan ne da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i. Wasu daga cikin alamun cutar dajin mahaifan sun hada da zuban jini bayna an gama ganin jinin hailar da aka saba gani wata-wata, ko kuma bayan an yi jima’i, fitowar ruwan farji mai wari sosai wanda kuma ya banbanta da sauran, zuwa fitsari a kai-a kai da kuma jin zafi a duk sadda aka je yin fitsari.

Me ya sa kamata a yi gwajin Pap Smear

Pap smear na daya daga cikin abubuwa masu mahimmancin gaske ga mata idan ya zo ga kula da lafiyarsu. Bisa bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cutar dajin mahaifa ita ce cutar dajin da aka fi samu a mataki na hudu . Baya ga neman kwayoyin da suke shirin zama cutar daji da ma wadanda suka riga suka zama cutar, gudanar da wannan gwajin a bakin mahaifa yana iya taimakawa wajen gano sauran matsaloli kamar cututtuka da kumburi. Domin ana yin shi a lokaci guda ne da gwajin da ake yi a kugun mace, ana iya gwajin da zai gano nau’o’i daban-daban na kwayoyin HPV 

Wa ke bukatar Pap smear?

Kungiyar cutar daji ta Amurka na bayar da shawarar cewa ya kamata kowace mace ta fara gwajin daga shekaru 25 na haihuwa, kuma duk macen da ke da shekaru tsakanin 25 da 65 wajibi ne ta yi gwajin HPV kowani shekaru biyar. Idan har babu gwajin HPV ya kamata a yi amfani da gwajin da ke duba kwayoyin cuta biyu, wato HPV da Pap daga shekaru uku zuwa biyar ba fashi.

Matan da ke dauke da kwayar cutar HIV ko kuma wadanda ke da garkuwar jikin da ba ta da karfi sosai saboda magungunan cutar daji na chemotherapy ko kuma an taba musu dashen gabobi sun fi hatsarin kamuwa da cutar daji ko kuma dai wata cuta dan haka wajibi ne a rika musu na su gwajin a kai- a kai ba sai an yi shekaru 3 zuwa biyar ba.

Lura! Yana da mahimmanci a yi la’akari da shekaru ne wajen zuwa yin gwajin ba yawan mutanen da mace ke kwanciya da su ba, saboda kwayar cutar HPV wata sa’a ta kan zauna shiru ne ba tare da ta yadu ba amma wata rana babu sanannan ciki sai ta bayyana ta fara yaduwa.

Yaya ake yin Pap smear?

Pap smear ba gwaji mai dadi ba ne amma kuma ana gama wa da sauri. Lokacin gwajin, likita zai dibi wasu kwayoyin da ke kan mahaifa da wuraren da ke kewaye da ita dan a gwada. Ana amfani da wani karamin tsinke da aka nade bakin da auduga a goge bakin mahaifar yadda za su kama jikin audugar. Daga nan sai a sanya shi a karkashin madubin binciken da ke kara griman kwayoyin halitta. A nan ne za’a go kwayoyin suna da lafiya ko kuma dai suna kan hanyarsu ta rikida zuwa wani abun da zai iya kaiwa ga cutar dajin.

Lura! Haila ko kuma yin jima’i wuni guda kafin gwajin da shan wasu magunguna kamar tetracycline kan yi kutse a gwajin.

Kwayar cutra HPV da Cutar daji

Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) ta ce ‘yan matan da ba su riga sun balaga ba na bukatar allurar rigakafin HPV daga shekaru tara na haihuwa zuwa 26 dan su sami kariya daga kwayar cutar HPV wanda zai kare su daga kamuwa da cututtukan da ka iya kai wa ga cutar daji.

Bisa shawarar CDC, masu shekaru 11 zuwa 12 ya kamata su karbi allurai biyu wanda za’a bayar da tazarar akalla watanni 12 a tsakaninsu. A kan bayar da shawarar ba su allurar farko sadda su ke da shekaru 11 ko 12 amma kuma ana iya ba su tun suna da shekaru tara.

Idan har ba’a ba su allurar farko kafin sadda za su cika shekaru 15 ba, allurai biyu ya kamata a ba su, amma idan yaran da ke tsakanain shekaru tara da 14 suka karbi allurar da tazarar watanni kasa da biyar tsakanin alluran dole a ba su na uku.

Matasa wadanda suka fara karbar alluran daga baya misali daga shekaru 15 zuwa 26, su ma suna bukatar allurai uku. Wadanda suka wuce shekaru 26 ba a cika ba su shawarar karbar allurar ba.

Lura: Wadanda suka karbi allurar kariya daga kwayar cutar HPV su ma ya kamata su rika zuwa gwajin pap smear tare da sauran wadanda suke a rukunin shekarun da suke da shi.

Ra’ayin kwararru

Wani likitan mata da ke asibitin Garki a Abuja, Sunday Idoko ya ce matan da suka riga suka san namiji ne ake musu gwajin pap smear. Sai dai macen da ke kwanciya da maza da yawa ta fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar daji da wanda kwayar cutar HPV ke haddasawa. Ya kuma kara da cewa jima’i ba turmi da tabarya ne kawai ba akwai wadansu abubuwan da su ma ake kira jima’i.

“Pap smear gwaji ne na gudanar da bincike kan mutanin da ba su da cutar daji ko wani jin ciwo a mahaifa. A kan yi shi ne a kan matan da suka riga suka san namiji wadanda ke da shekaru tsakanin 21 zuwa 50. Sakamakon gwajin ne ke bayyana irin matakin da za’a dauka. Matan da kan yi amfani da baki ko sauran na’urori masu kama da al’aurar maza ma a kan ba su shawarar gudanar da gwajin.” 

Da ya ke bayani kan allurar rigakafi, ya ce maza da mata daga wadanda ke tsakanin shekaru tara da 21 bai kamata a yi mu su rigakafin ba domin cututtukan da ake samu ta hanyar jima’i ne yawanci su ke janyo cutar dajin da ke da nasaba da mahaifa. 

Wata ma’aikaciyar lafiya, Lynda Effiong-Agim, a asibitin kwararru na Chivar Specialist ta amince da bayanin Dr Idoko kuma ta kara da cewa yawan wadanda ake kwanciya da su ba shi ne ya ke bayyana irin matan da za su ci moriyar gwajin ba.

“Pap smear gwaji ne da ke bai wa mata masu shekaru 21 zuwa sama, wadanda kuma suka san namiji su gudanar (ko da irin jima’in da suke yi ba ta farji ake shiga ba). Yawan mutanen da mutun ke kwana da su ba shi ne zai sa gwajin ya wajaba ga mata ba, kowace macen da ta kai shekarun da aka sa ne ya kamata ta yi.

“Idan dai har suna kwanciya da namiji, wajibi ne a rika musu pap smear akalla bayan kowani shekaru uku, ” ta kara da cewa.

A Karshe

Duk da cewa shawarar ita ce matan da suka san namiji masu shekaru tsakanin 21 da 50 su je a yi musu wannan gwajin, bincikenmu ya nuna mana cewa ba masu kwana da maza da yawa ne kadai gwajin ya wajaba a kansu ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »