African LanguagesHausa

Gaskiya ne INEC na daukar ma’aikata gabannin zaben 2023

Zargi: Wani sakon da ke yawo a Whatsapp na zargin wai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC har yanzu tana daukar wadanda za su yi aikin zabe kafin zabukan na watan gobe (2023)

Gaskiya ne INEC na daukar ma’aikata gabannin zaben 2023

Ana kira ga ‘yan Najeriya su yi la’akari cewa INEC ta rufe shafin daukar ma’aikata tun 14 ga watan Disemban 2022. Wannan shafin na masu yaudara ne wanda suka tsara shi dan satar bayanan jama’a.

Cikakken bayani

Yayin da zaben 2023 ke kara kusantowa, masu ruwa da tsaki, har da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC na cigaba da gudanar da shirye-shiryen zaben da za’a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da kuma 11 ga watan Maris 2023. Sai dai, yayin da masu ruwa da tsakin ke aikin ganin an gudanar da zaben cikin nagarta da aminci, mayaudara na amfani da damar da suka samu wajen amfani da bayanan ‘yan Najeriyar da ba su ji ba su gani ba, wadanda kuma ke muradin bayar da ta su gudunmawar wajen tabbatar da sahihin zaben, dan aikata asha.

A watan Satumban 2022 INEC ta yi kira ga ‘yan kasa wadanda suka cancan kuma su ke sha’awar aikin da su tura takardunsu. A wata sanarwar da ta wallafa a shafinta hukumar ta ce duk mai sha’awa ya yi rajista tsakanin 14 ga watan Satumba da 14 ga watan Disemna 2022 a shafinta na mussaman na daukar ma’aikatan zabe.

Tun bayan da INEC ta kaddamar da shirin daukar ma’aikatan a Satumba shafukan bogi da yawa sun bulla da nufin satar bayanan mutanen da ba su ji ba su gani ba, wadanda suke da muradin taimakawa a zabukan masu zuwa.

Kamar yadda ta sanar, an rufe shafin daukar ma’aikata na INEC tun 14 ga watan Disemba 2022 amma ko a ranar 1 ga watan Janairun 2023 shafunkan WhatsApp da dama na cike da sakonnin da ke cewa INEC ta cigaba da daukar ma’aikata.

Sakon na dauke da wani adireshi wanda ke bai wa jama’a damar yin rajista a matsayin ma’aikatan zabe gabanin zaben na shekarar 2023.

Matakin farko na neman aikin ya kunshi adireshin da ke bukatar masu sha’awa sun shigar da bayanansu kamar suna da adireshin email da sauransu. Bayan wadannan bayanai, sai a kai shi wani shafin wanda ke cewa a raba sakon da mutane 15 ko kuma kungiyoyin WhatsApp kafin ya iya samun lambar da za ta bashi damar ganawa da ofishin.

Da zarar an kammala wannan, sai a shiga shafin da ke bayanin cewa an tura lambar ko kuma appointment ID zuwa adireshin email din da aka bayar amma

kuma mutun na da zabin buga lambobin inda aka sa “print form” sai dai idan aka je shafin ba abin da ake gani.

A wata hirar da muka yi da daya daga cikin mutanen da suka raba sakon da mutane suka kuma cike fam, ya tabbatar mana da cewa bayan an kammala komai babu wani abin da ke tabbatar da cewa sun sami takardun kamar yadda ya kamata a samu a irin wannan lamarin.

DUBAWA tana ganin kamar da walakin goro a miya tunda duk wata hukuma mai nagarta ta kan tura sako da zarar aka tura mata takardun neman aiki, kuma wannan shafin na kama da na mayaudara wadanda kan yi kokarin satar bayanan wadanda ba su ji ba su gani ba.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tantance shafin a shahararren shafin WHOIS. WHOIS shafin ne da ke tantance duk wani kundin bayani na yanar gizo da ke ajiyar bayanan wadanda suka yi rajistar shafin yanar gizo, masu amfani da shafin , da ainahin sunan shafin da adireshin shi. WHOIS bai ba mu bayanai masu gamasarwa dangane da shafin ba, yawancin amsoshin da ke jikin tambayoyi na bayanin cewa an sakaya bayanin bisa dalilai na kariya, abin da ya nuna mana cewa da gangar aka sakaya bayanan.

DUBAWA sai ta yi kokarin cika fam din ta gani. Nan da nan aka ba ta damar shiga shafin ba tare da ta bayar da adiresoshinta na gida da na email ba. Wanda kuma ba zai taba faruwa a shafin INEC ba domin sai ka cika bayananka a matakin farko kafin ka sami izinin zuwa mataki na gaba.

Mun sake duba shafin “scamdadviseer.com” shafin da ke tantance adiresoshi ya bayyana ko suna da nagarta ko kuwa a’a, inda shafin ya nuna mana cewa ana amfani da adireshin na INEC wajen aikata miyagun ayyuka. Hasali ma miyagun abubuwa wajen 12 shafin ya bayyana cewa ana yi, ciki har da guda uku wadanda ke da dangantaka da yakin neman zaben shugaban kasa na dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da guda daya wanda shi kuma ya ke da dangantaka da dan takarar jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu. Mayaudaran na amfani da shafin su dauki bayanan jama’a.

Ms Iqmot wadda ta yi rajistan neman aikin wajejen watan Oktoban 2022 ta ce tana sane da ire-iren wadannan shafukan sadda ta yi rajistar dan haka ta dauki matakan kare kanta dan ka da ta fada tarkonsu.

“Na yi rajista a babban shafin INEC, kuma ina kammalawa aka aiko mun da takardar cewa sun sami bayanai na ta adireshi na na email. Har yanzu tana wuri na, zan iya nuna mu ku idan kuna bukata.”

Da muka yi wa takardar kallon kwa-kwaf, an bayyana cewa takardar ta fito daga shafin INEC ne kuma ya na dauke da lambar QR (QR code) wadda daga ka dauki hoton ta, duk bayanan mutun za su bayyana. Da mu ka nuna wa Ms Iqmot shafin da mu ke zargi na bogi ne, cewa ta yi:

“Wannan lallai shafin bogi ne, domin dole sai ka kirkiri sabon shafi da sunanka kafin ka iya yin rajista a shafin na INEC PRES, bacin haka ma wa’adin yin rajistan ya cika dan haka an rufe tun a tsakiyar watan Disemba.

Bugu da kari, takardar da aka turawa Iqmot bayan ta yi rajista na dauke da hoton ta amma na dayan shafin babu.

DUBAWA ta kuma gano cewa bayan da wadanda suka kirkiro shafin sun boye sunayensu, sun kirkiro wani adireshin da su ke rabawa a WhatsApp dan yaudarar jama’a

Ga adireshin da ake gani a WhatsApp:

Sai dai ainihin adireshin shafin da aka gano daga baya shi ne

DUBAWA ta kuma iya samun hujjojin da suka nuna cewa shafin https://yourclaims.com/Inec-Recruitment/   na bogi ne wanda ake amfani da shi wajen satar bayanan jama’a wadanda ba su ji ba su gani ba

Mayaudaran sun shirya shafin sosai yadda zai taimake su wajen yaudara domin har da tambarin hukumar INEC kuma tsarin shafin ma baki daya sun yi shi cikin irin suffan da aka yi shafin hukumar zaben na ainihi.

A Karshe

Ana kira ga ‘yan Najeriya su yi la’akari cewa INEC ta rufe shafin daukar ma’aikata tun 14 ga watan Disemban 2022. Wannan shafin na masu yaudara ne wanda suka tsara shi dan satar bayanan jama’a.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »