African LanguagesHausa

Gunkin Christiano Ronaldo da aka sassaka a dutsen farar kasa an yi ne da kirkirarriyar fasaha ta AI – na’urar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani hoto (image) na danwasan kasar Portugal Christiano Ronaldo, da aka sassaka akan dutsen farar kasa an yada shi a shafin Facebook na GOAL Africa inda aka nunar da cewa wani yaro ne ya sassaka kamar yadda aka gani a hoton.

Gunkin Christiano Ronaldo da aka sassaka a dutsen farar kasa an yi ne da kirkirarriyar fasaha ta AI - na'urar da ke kwaikwayon dabi'un dan adam

Hukunci: Da’awar karya ce. An hada hoton ne ta hanyar amfani da kirkirariyar fasaha ta AI.

Cikakken Sakon

Wani shafin Facebook mai suna Goal Africa, wanda ke zama shafi ne na Intanet da ke yada  labaruka da ke da alaka da harkokin wasannin kwallon kafa, ya yada wani hoton fitaccen dan wasan kwallon kafar nan dan asalin kasar Portugal Christiano Ronaldo,(claiming) ana da’awar cewa an sassaka gunkinsa kuma wani matashin yaro da ke a hoton shi ya sassaka shi.

Wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu wato Likes 96,000 da wadanda suka yi tsokaci wato Comments su 2,100 da wadanda suka sake yadawa shares su 1,600. An dai rika samun sabanin ra’ayi kan wannan wallafa wasu na cewa yaron ne ya sassaka gunkin wasu kuma na cewa an yi amfani da kirkirariyar fasaha ce ta AI wajen fitar da hoton gunkin.

 “Wannan babar bajinta ce yayi,” a cewar Henry Akisikpo.

Akisikpo ya kuma yi kira ga masu amfani da shafukan na sada zumunta da su ja hankalin Ronaldo don ya ga wannan sassaka ta yadda zai taimaka wa wannan yaro.

Ya kara da cewa “Wa ya sani ma ko wannan zai sa yaron ya samu sauyi a rayuwarsa.”

An samu rudani a dangane da asalin hoton, inda Victor Joshua Jnr yayi tantama ko wannan hoton ma an yi shine daga fasahar ta AI.

Ya kara da cewa yanzu duniya an shiga rudani yana da wahala ka fahimci me ke zama na gaskiya da wadanda ba na gaskiya ba.

Shi kuwa Ahmad Adam nuna mamakinsa yayi ga wadanda suke ganin cewa wannan hotonma na gaske ne. Ya ce “Ina ma mamakin yadda wasu ke ganin wannan hoton na gaske ne ba su fahimci cewa an yi shi ne da fasahar AI ba.”

DUBAWA ya gudanar da bincike kan wannan da’awa ganin yadda za ta iya sanya al’umma a cikin rudu.

Tantancewa

DUBAWA yayi amfani da fasahar tantance asalin hoto ta Google Reverse Image Search. Hukuncin da ya gano, ya nunar da cewa an yada wannan hoto sau da dama kamar a nan  here, here, here, da nan  here.

Ta wannan hanya, DUBAWA ta bibiyi hotuna na Facebook da ke nuna yadda aka yi hotuna da fasahar ta AI, aka nuna wasu fitattun mutane da shugabanni a duniya. Duk da cewa shafin bai ce hotuna ne da aka wallafa da fasahar ta AI ba ne, bincike ya gano irin wadannna hotuna da aka nuna yara ne suka kirkira inda suke a tsaye a gefen hoton.

Christiano Ronaldo’s statue carved on limestone, AI-generated

Hoton da aka kirkira da fasahar AI da aka dora a shafin Facebook mai lakabin (Bestboy Talents)

Akwai ma wasu hotunan da aka ba su take kamar “Amazing Young Boy (Amazing Artwork).” 

Wannan hoton an kuma yi nazarinsa ta hanyar amfani da wata fasahar ta AI, AI ive AI wanda ya nuna cewa an samo hoton ne daga fasahar ta AI, sakamako ya nunar da kaso 99 cikin dari. Sannan ta amfani da fasahar  Is it AI ta nunar da cewa wannan hoto an samo shi ne daga fasahar ta AI kamar yadda binciken ya nunar da kaso 90.72 cikin dari .

Christiano Ronaldo’s statue carved on limestone, AI-generated

Kwafin hoton da aka dauka da  Is it AI ya nunar da cewa hoton na AI ne da kaso 90.72 cikin dari.Christiano Ronaldo’s statue carved on limestone, AI-generatedKwafin hoto na  Hive ya nuna kaso 99.9 cikin dari ya nuna hoton na AI ne.s

Karshe

Gunkin da ke nuna hoton Christiano Ronaldo an samar da shi ne da fasahar AI. Ba kuma yaron ne ya sassaka shi ba.

Wannan rahoton aikin bincike an yi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar jaridar Daily Trust a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button