Zargi: Wani sakon da ke yawo a WhatsApp na zargin wai gwamnatin Dubai na bayar da $110 a matsayin kudin tallafi ko sadaka na watan Ramadan

Sakamakon Bincike: KARYA. Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wani kudin tallafin da gwamnatin Dubai ke bayarwa kuma wadanda suka rika yada sakon sun yi hakan da mugun nufi ne.
Cikakken Bayani
A duniya baki daya, Musulmi kan fara azumin shekara-shekara a watan Ramadana ne. Lokacin azumin, a kan samu bayanai da yawa dangane da ibadan a shafukan intanet.
Yayin da ake azumin dai, duk musulmi na da bukatar sayen abinci da kuma gudanar da azumin cikin koshin lafiya, abun da kuma ke bukatar kudi.
Ana haka ne, wani sako ya bulla yana zargin cewa gwamnatin Dubai na raba dalar AMurka $110 a matsayin sadaka ko kuma wani tallafi na watan Ramadan kuma kowa na iya samun kudin ko da ma daga kasar kake ba.
Yadda sakon ya yadu da yawan sakonnin da DUBAWA ta samu masu bukatar mu fayyace gaskiyar batun ne ya saka muka dauki nauyin yin hakan.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi dangane da kudaden tallafin Ramadanan na Dubai dan ganin ko za ta ga labarin a wani wuri a shafukan yanar gizo amma batun bai bulla ba. Sai dai mun gano wadansu kungiyoyi na masu bayar da tallafin da ke taimakwa mutane da abinci lokacin Ramadan.
Bisa bayanan jaridar Arab News, shugaban Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum, ya kaddamar da wani shiri mai dorewa wanda zai baiwa daruruwan miliyoyin jama’ar da ke bukata duk abincin da suke so lokacin Ramadan.
Alamun rashin sahihancin labarin
Mun dauki adireshin da aka yi labarin mun sa a shafin Whois.com domin tantance inda shafin ya fito, sai muka gano cewa a jihar Oyon Najeriya aka kirkiro shafin ba a Dubai ba.
Wata alamar rashin gaskiyar batun kuma ita ce duk wanda ya ziyarci shafin, zai iya wuce matakin da ke bukatar mutane su cike fam wato “application form” wanda ya kamata ya ba su damar samun tallafin. Abun da ya nuna cewa keta ce kawai aka shirya dan rinjayar wadanda ba su ji ba su gani ba.
Har wa yau, wata alamar kuma ita ce akwai tsokace-tsokace na karya a jikin shafin. Wannan salo ne da mazambata suka saba amfani da shi wajen rinjayar jama’a. Duk da cewa ko an latsa adiresoshin da ake zargi suna dauke da bayanan wadanda suka sami kudaden ba su aiki, kasancewarsu a shafin na iya yaudarar jama’a.
Bayan an latsa kalmar “submit” wanda ke nufin a tura duk bayanan da aka cike a fam din, ko da kuwa ba’a cike komai a cikin shafin ba, mun gano sakonni da dama da ke nuna mana cewa an kayyade adadin wadanda za su iya samun tallafin zuwa 50,000
Bayan an tura fam din, shafin kan bukaci karin bayani daga masu amfani da shafin kafin su iya shiga rukunin wadanda ke neman tallafin.
Daga cikin abubuwan da sukan so su sani akwai bukatar raba labarin da ‘yan uwa da abokan arziki abun da ya bayyana mana cewa dalilin da ya sa sakon ya yadu sosai ke nan.
A karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa gwamnatin Dubai ba ta bayar da wasu kudaden tallafi ko ma sadaka na Ramadan kuma sakon da aka yada an yi shi da nufin yaudarar jama’a ne dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne.