African LanguagesHausa

Gwamnatin Tarayya ta ce ta na nan kan bakarta dangane da janye tallafin man fetur

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Gwamnatin tarayya ta amince ta biya tallafin man fetur.

Hukunci: Yaudara ce! Shugaba Tinubu bai ce zai bada tallafin man fetur ba kamar in da ake yaɗawa a kaffofin yaɗa labarai daban-daban. Rahotannin da aka gani fadar shugaban kasar ta ce daftari ne na shawarwari dangane da shirin rage matsalar rayuwa wadanda ba’a riga an aiwatar da su ba

Cikakken Bayani

Tun bayan da geamnatin Shugaba Tinubu ta ce ta janye tallafin man fetur ake kai kawo dangane da gaskiyar wannan batun kuma a kusan ko da yaushe ko da gwamnati ta hakikance kan batun sai maganar ta sake dawowa.

Batutuwa biyu ne dai a kan gaba a cikin abubuwan da sanya shakku a zukatan al’umma. Na daya shi ne an tsayar da farashin man fetur ba tare da ya motsa ba a kan farashin da ke tsakanin N670 zuwa N700 farashin da NNPC ce kadai ta ke iya shigo da man fetur din da saida shi a hakan.

Na biyu kuma farashin ya cigaba da kasancewa a hakan ne duk da cewa an rage darajar takardar kudin naira har sau biyu sa’annan ana cigaba da fama da hauhawar farashin kayayyaki. Bisa la’akari da yadda kasashe irin su Saudiyya – wadanda suma suke da arzikin man fetur din suke sayar da sh da tsada, da yawa na sanya alamar tambaya kan yadda aka yi Najeriyar ke sayar da man a hakan idan har ta ce ta janye tallafi

Shi ya sa da wani daftarin rohoto mai suna “Accelerated Stabilisation and Advancement Plan” (ASAP) a turanci wato Shirin gaggauta daidaito da cigaba ya fito, batun ya sake dawowa. Bayanai sun nuna cewa ministan kudi da kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ne ya gabatar wa shugaba Tinubu da wannan rahoton.

Wannan rahoton dai, ya nuna cewa an biya kudaden tallafin mai na Naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024 wanda ma rahoton ya ce ya haura na 2023 da Naira tiriliyan 1.8. Batun ya sake dawowa. Kamar yadda muka gani cikin wannan rahoton da aka yi a shafin ATV Hausa

Gwamnatin Tarayya ta ce ta na nan kan bakarta dangane da janye tallafin man fetur

Wannan rahoton ya fito ne daura da wani rahoton wanda shi kuma aka yi mi shi taken “Inflation reduction and price stability measure” wato rage hauhawar farashin kayayyaki da matakin tabbatar da daidaito

A baya dai, gwamnatin Tinubu ta tsaya tsayin daka cewa ba ta janye tallafin man fetur a abin da ta ce ya kasance tarihi sai dai da fitowar wadannan rahotannin akwai shakku dangane da hakan.

Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya kuma ya ke daukar hankalin al’ummar Najeriya saboda mahimmancin da ya ke da shi ga rayuwarsu ta yau da kullun ne ya sa DUBAWA tantance wannan batun

Tantancewa

DUBAWA dai daga farko ta ga wannan labarin tallafin a shafin ATV Hausa a manharajar Facebook sai muka  fara bincike dan mu gani idan da gaske ne shugaban ƙasa Tinubu ya ce zai bada tallafi na mai. Mun yi amfani da mahimman kalmomi a manharajar Google in da muka ga cewa kafofin yada labarai da dama wadanda suke da nagarta har da jaridar Daily Trust din da ATV ta yi amfani da ita a matsayin majiya, sun yi wannan bayanin kamar yadda muka gani a wadannan shafukan na turanci a nan da nan da nan.

Cikin bincike domin samun tabbacin lamarin, mun gane cewar mai baiwa shugaban ƙasa shawara Bayo Onanuga ya roƙi yan Najeriya da su yi fatali da daftarin. Bayo Onanuga ya yi bayanin ne ya na cewa, “an ja hankalin fadar shugaban kasa kan wasu rahotanni guda biyu wadanda ke yawo a kafofin yada labarai da ma shafukan sada zumunta na soshiyal mediya,” ya ce kuma ya yi kira da a daina yadawa domin rahotannin biyu duka na matakin daftari ni sa’annan kamar yadda aka sani ya kan dauki lokaci kafin a dauki mataki irin wannan sai an yi ta shawara. 

Kuma bisa bayanan da ke ciki ana tsara shirin ne don magance manyan kalubalen da suka shafi yunkurin yin gyare-gyare da habaka cigaba a sassa daban-daban na tattalin arziki.

Mun ga sanarwa da ya wallafa a ranar 6 ga watan Yuni 2024 a manhajar X in da ya shaida da cewa lallai shugaba Tinubu bai ce zai bada tallafin man fetur ba kamar yadda ake yaɗawa, zancen tallafin man fetur ya zama tarihi a Najeriya. Ya kuma kara da cewa duk wani shiri da ake yi yanzu na rage tsada da matsalolin rayuwa ne ba na sake maido tallafin man fetur ba.

Haka nan kuma jaridun kasar masu sahihanci kamar su The Guardian, su ma sun dauki labarin inda takensu ma ke bayyanawa a turanci cewa matsayar fadar shugaban kasa dangane da janye tallafin man fetur ba ta sauyawa ba. 

A Karshe


Da’awar da ake yi da cewar Gwamnatin Tarayya za ta bayar tallafin mai Naira tiriliyan 5.4 a shekara 2024, Yadara ce! Domin fadar gwamnatin ta karyata batun ta bakin mai magana da yawunta Bayo Onanuga. Kuma duk da cewa rahotannin na sa jama’a tunanin cewa lallai akwai tallafin mai gwamnati ta hakikance kan cewa ba ta yi amai ta lashe ba.

Wannan rahoton aikin bincike an yi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Deborah Majingina Habu a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »