Ranar 26 ga watan Oktoban 2022, Hukumar kula da harkokin kudin Najeriya, wato babban bankin kasar CBN, ya sanar cewa zai janye tsofaffin takardun kudin N200, N500 da N1000 ya maye gurbin su da wadansu sababbi wadanda za’a zana.
Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin ya bayyana cewa sabon zanen da janye tsoffin takardun kudin da za’a yi na daga cikin irin yunkurin da hukumarsa ke yi na janye kudaden da ake kiyasin sun fi Nera triliyan 2.72, wadanda kuma ke yawo a cikin kasar a maimakon kasancewa a hannun banki. Bacin haka zai taimaka wa CBN wajen samun “cikakken iko kan yawan kudaden da ke yawo a hannayen jama’a.”
Ba da dadewa ba bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin kudin, da yawa suka fara bayyana fargabar cewa kudin zai yi saukin kwaikwaya musamman a hannun wadanda suka saba yin kudaden bogi.
Hasali ma, tun kafin a kaddamar da sabbin takardun kudin aka fara samun labarai masu kawo rudani dangane da abun da kudaden za su yi kama da . Har wa yau, bayan da aka gabatar da kudaden wasu sun yi zargin cewa takardun kudin ba su da karko kuma ba wuya zasu yi zuba. Wasu ma sun yi zargin cewa ‘yan siyasa na nan suna buga na su kudaden wadanda za su raba wa jama’a lokacin zabe, sa’annan an rika samun bayanan wadanda ke amfani da takardun kudin bogi.
Da labarai iri-iri dangane da takardun kudin bogin da ke hannun jama’a, mutane da dama suna fargabar rasa kudadensu wadanda zufar su ce kuma halaliyarsu tunda ba wani ya yi musu aikin ba. Dan haka ga hanyoyin da za su iya taimakawa wajen banbanta takardun kudin masu sahihanci daga jabu.
Gwaji ta tabawa: Takardun kudin na ainihi suna da kaifi sosai a gefe daga an taba za’a ji, kuma suna da daukar ido, yayin da na jabun ba su da haske sosai kamar launukan na zuba kuma zanen rubutun ba shi da inganci. Kalolin kuma ko daya ba su yi kama da irin wanda ake gani a kan takardun kudin na gaskiya ba.
Dan haka idan takardun kudinku ba su da haske ko kaifi, jabu ne.
Gwaji na lambobin da suka zo da su daga kamfanin buga kudin: Bakaken lambobin da ke kan kowace takarda kan sauya launi zuwa kore idan aka kanga shi jikin wutar nan ta musamman wato ultraviolet light. Wannan na daya daga cikin matakan tsaron da aka dauka dan dakile matsalar jabun takardun kudin.
Haka nan kuma, takardun kudin na gaskiya na dauke da lambobi na musamman da ke banbanta su kuma an yi amfani da salon rubuta lambobi da harufa na musamman. Takardar N1000 ta na da dauke da lambobin cikin launin baki yayin da takardun kudin N200 da N500 ke dauke da salon rubuta lambobin na musamman.
Gwaji da falen zinari: A takardar N1000 ta gaskiya, akwai dan falen zinari a gefen damar da za’a iya kwazurewa. Bayan an kwazure za’a ga tambarin Najeriya da 1000 a rubuce a inda aka kwazure falen zinarin.
Kudin jabu ne idan har babu fallen zinarin ko kuma idan har an iya kwazure fallen zinarin cikin sauki.
Gwajin Kintinkiri: Sababbin takardun kudin na dauke da wani zare wanda ya yi kamar ya tsinke amma kuma idan aka kanga shi a jikin wuta ko haske za’a ga cewa layi daya ne ke tafe a tsaye. Wannan layin na bayan takardar N1000, sa’annan a gaban N200 da N500. An kuma rubuta ‘CBN’ a gaba da bayan takardun kudin a kananan harufa.
A Karshe
Wajibi ne jama’a su fahimci yadda ake gani takardun kudin jabu domin su kare kansu daga rasa kudadensu. Al’umma za ta iya gane kudaden jabinn idan har ta duba siffofin kudin, launi, inganci da kuma lambobin da aka basu tun daga wajen da aka buga takardun kudaden.