Hoton Atiku da Tambuwal na karbar shugaban ‘yan bindiga zuwa jam’iyyar ADC , an hada ne da fasahar AI

Bello Turji Photo Source: Trust TV.
Bello Turji
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa fitaccen danta’addar nan Bello Turji ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar ADC kuma ya samu tarbar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Sanata Aminu waziri Tambuwal.

Hoton Atiku da Tambuwal na karbar shugaban ‘yan bindiga zuwa jam’iyyar ADC , an hada ne da fasahar AI

Hukunci: Karya ce, hotunan da aka yi amfani da su don karfafa da’awar anyi amfani da AI ne wajen hada su. 

Cikakken Labari

A ranar Litinin 12 ga Oktoba,2026 wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa Bello Turji sanannan danta’addar nan jagoran ayyukan fashin daji a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ya fice daga jam’iyyar  Peoples Democratic Party PDP zuwa  African Democratic Congress ADC.

Wallafar kamar yadda aka adana (nan) an yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal a hukumance sun karbi Turji zuwa jam’iyyar ADC.

Sakon da aka wallafa da ya yadu  an rubuta shi kamar haka, “CHANZA SHEKA DAGA PDP ZUWA ADC…. Ayau ne Dan’takarar Shugaban kasar Nigeria a karkashin tutar jam’iyar ADC Alhaji Atiku Abubakar Da tsohon Gwamnan Jahar Sokoto sanater Aminu Waziri Tambuwal Sun karbi Shararen Dan’bindiga wanda yayi Suna A Nigeria Da idon Duniya Daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar ADC Muhammad Bello Turji, Daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar ADC Ayau 12/10/2026.”

Domin ya karfafa da’awar tasa mawallafin ya hada da hoton Atiku da Tambuwal suna rike da hannun juna tare da shugaban ‘yanbindigar da ake nema ruwa a jallo. 

Ya zuwa ranar 13 ga watan Oktoba,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 234 da masu tsokaci 364 da wadanda suka sake yadawa 24.

Wannan wallafa ta samu  martani kala-kala daya daga cikin masu martani Zainab Mohd tayi tambaya ne da cewa, “Shin ya kammala yi masu aiki ne?”

Wani mai amfani da shafin Tafida Gatawa yayi watsi da da’awar da ya bayyana da zama wacce aka kirkira: “Mu ba mahaukata ba ne, dukanmu mun san AI, kaje ka fadawa wanda bai taba zuwa makaranta ba.”

Mun kuma samu wata da’awar irin wannan da aka sake yadata a nan.

Da’awa da ake yi ana alakanta manyan ‘yansiyasa da shugabannin ‘yanbindiga zai iya shafar yadda masu zabe ke kallon wadannan ‘yansiyasa gabanin zaben da za a yi a 2027, don haka DUBAWA ta yi bincike a kai.

Tantancewa

Hoton da aka bincika ta Google ya kai DUBAWA ga wata ganawa da aka yi tsakanin Sanata Aminu Tambuwal da Bashir Gorau wanda ke wakiltar Gada/Goronyo a majalisar wakilan Najeriya tare da dantakarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar ADC Atiku Abubakar a watan Satumba,2026. Yayin wannan ganawa Atiku ya daga hannun Bashir a matsayin yana tare da shi, kasancewar yana sake neman wannan kujera ta danmajalisa.

Bayan da muka kwatanta wannan hoto da ya yadu da na waccan ganawa, mun lura cewa dukkaninsu akwai wani hoto makale a bango, sannan haduwar hannun ta saba da na halitta, yanayin hada fuskar ma yayi kama da wanda ake yi da fasahar ta AI.

Photo collage of the viral and original images. 
Source: DUBAWAHoto da aka hada da wanda shine na asali

Tushe: DUBAWA

Sake bincikar hoton da ke tare da Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaimu ga wata wallafar a shafin na Facebook wanda aka wallafa a  Agusta 2026. Idan aka kwatanta hoton na asali da wanda aka yi aiki a kansa, an sanya shi Turji ne a cikin hoton a kokari na cimma wata manufa wacce ta karya ce.

Photo collage of the viral image of Tambuwal and the original image
Hoton da ya yadu kamar wutar daji da hoton na Tambuwal wanda shine na asali

DUBAWA ta gudanar da bincike kan wannan hoto ta hanyar amfani da hanyar gano asalin hoto ko na AI ne da Google, sakamakon ya nunar da cewa an hada hotunan da gyara su ta hanayar amfani da OpenAI.

Photo collage of the SynthID results.
Hoto daga sakamakon SynthID

Haka nan da aka turawa Hive don nazartar hoton sakamakon ya nuna cewa kaso  89.9%  hada hoton aka yi na Turji da Atiku.

Haka nan ya nuna cewa kaso 89.3%, an hada hoton Turji da Tambuwal ne da kirkirarriyar basira.

Collage screenshot of HiveAI result. 
Hoton sakamako daga HiveAI

Mun kuma gudanar da bincike ta hanyar Google da manyan kafafan yada labarai da wallafar jam’iyya, amma babu inda aka samu Bello Turji yayi rijista da jam’iyyar PDP ko jam’iyyar ADC.

DUBAWA ta kuma tuntubi Yakubu Kware, sakataren jam’iyyar ta ADC a Sokoto wanda yayi watsi da wannan da’awa.

“Da’awar gaba dayanta karya ce. Kokari na abokan adawa ne na ganin sun zubar mana da kima ta jam’iyya.”

Wannan lamari ya nuna yadda ake alakanta Turji da wasu jam’iyyu na siyasa. A watan Janairu, 2026 masu aikin gano asalin labari sun watsar da batun cewa ya kasance mamba ko yi masa ma rijista da jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A Karshe

Da’awar cewa jagoran ‘yanbindiga Bello Turji ya fice daga PDP zuwa ADC kuma ya samu karba ta Atiku da Tambuwal karya ce.

ADC ta karyata batun haka kuma bincike ya tabbatar da cewa hotunan da aka yada an hada sune da fasahar AI.

An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) karkashin OSINT a Arewa maso Yamma da tallafin  Kungiyar Tarayyar Turai.