|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Issiaka The Blogger a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo dake nuna shigowar ‘yan ta’adda da dama Najeriya.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon tsoho ne sannan nuna yadda baki ‘yan ta’adda ke ketara iyakan kasa karya ne. an gano cewa an yi amfani da AI wajen hada bidiyon.
Cikakken Bayani
Issiaka The Blogger a shafinsa na Facebook a ranar 28 ga Agusta 2026 ya wallafa wani bidiyo da da’awar dake nuna cewa ‘yan ta’adda da dama na shigowa kasar har ma ya bukaci da ya san abin da ake kan tsaron iyakokin kasar.
Da’awar da aka saka a (nan) ya ce “Daga ina wadannan ‘yan ta’adda ke shigowa kasar nan sannan ta yaya suka iya tsallaka iyakan Najeriya? Wadannan sune tambayoyin da ya kamata ‘yan Najeriya su rika tambayar kansu”.
Bidiyon ya kasu zuwa rukunnai uku.
Rukunin farko ya nuna yadda wasu mahara dauke da bindigogi ke harbi a iska inda daga baya suka shiga wani daji, rukuni na biyu ya nuna wansu mahara dauke da bindigogi na zaune a wani mota kirar bus mai laufin fari yana tafiya a wani wuri dake kamada hamada sannan rukuni na uku ya nuna wasu mahara akan babura suna hanyar sun a shiga daji.
A ranar 2 ga Satumba 2026 mutum 2,200 sun kali bidiyon, 90 na shi’awan bidiyon, 42 sun sake wallafawa da 63 sun maida martani.
Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce daga wajen mutane a Facebook.
Axe Ganto ya rubuta cewa “sun shigo Najeriya kamar yadda ‘yan Najeriya ke shiga kasashen waje ba tare da izini ba”.
Anthony Osuagwu ya ce “Hukumar kula da shiga da fita na kasa dake Arewacin Najeriya su bada amsa”.
Lazarus M. Tar ya ce “Najeriya ta saka matakan tsaro a iyakokin kasanta ne dama? Wadannan mutane basu ketara iyakan kasa ba ta dazukan mu kawai suka shigo kasan.
Tantancewa
DUBAWA ta yi amfani da ‘the InVID verification plugin da reverse-image searches’ domin tantance bidiyon inda sakamakon ya gano cewa hotunan bidiyon na daga cikin hotunan da wasu gidajen jaridu ke amfani da su wajen nuna ayyukan mahara a labaran su.
A ranar 22 ga Maris 2023 a wani rahotan da gidan jaridar ‘People’s Gazette’ ta fitar mai taken ‘Mahara sun kashe sojoji biyu, da wasu 32 a Kaduna – Inji Hukuma’ sun yi amfani da hoto irin haka domin nuna mahara.
Sakamakon binciken ya gano irin hoton da ‘Entertainment TV’ a shafinta na Facebook ta yi amfani da shi domin nuna yadda mahara suka bukaci naira miliyan 100 kudin diyyan kowani mutum daya da suka yi garkuwa da su daga cocin ‘Christ Apostolic’ a jihar Kwara.
Daga nan kuma a ranar 29 ga Janairu 2026 BusinessDay sun yi amfani da hoto irin haka domin nuna binciken matsalar rashin tsaron dsa ake fama da shi a kasar nan da SBM Intelligence ta yi.
Sakamakon binciken ya kuma gano hotunan da aka yi amfani da su a shafukan X,Instagram da sauran kafafen sada zumunta na yanar gizo domin nuna ayyukan mahara.
@adesolayinka a shafinsa na Instagram ya wallafa hoto irin haka domin nuna yadda mahara da suka rufe fuskokinsu suka yi layi mai tsawo akan babura.
Amfani da wadannan hotuna yasa aka bukaci sanin asalin hotunan inda ake zargin cewa an yi amfani da AI wajen hada hotunan.
A binciken da gidan jaridar ta gudanar ta kula da yadda wasu hotunan bidiyon basu haduwa da sauran hotunan sannan ya nuna mutane a cikin bidiyon na tafiya wani iri wanda hakan yasa aka yi zargin an yi amfani da AI wajen hada bidiyon.
Gidan jaridar ta yi amfani da HIVE Detect yadda hotunan bidiyon suke motis inda ta gano cewa an yi amfani da AI har wajen kashi 42%.
VigilAI da DUBAWA ta yi amfani da shi ya nuna cewa bidiyon na bogi ne da aka yi amfani da AI wajen hada shi wajen kashi 98%.
Dubawa ta gano an yi amfani da ‘AI image -to-video tools’ wajen maida hoto bidiyo.
A taikace dai gidan haridar ta gano cewa hotunan tsofaffi ne wanda aka maida su zuwa bidiyo ta hanyar amfani da AI.
A Karshe
Bidiyon dake nuna yadda ‘yan ta’adda ke shigowa Najeriya yaudara ce. An yi amfani da AI wajen hada bidiyon ta hanyar amfani da wasu tsofaffin hotuna da aka yi shekaru da dama ana amfani da su domin nuna ayyukan maharaa labarai.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
