African LanguagesHausa

Jami’ar  FUOYE ta kammala daukar dalibai na 2023/2024 

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Mai amfani da shafin Facebook Adetunmobi Jibola na zargin wai jami’ar FUOYE da ke jihar Ekiti  na cigaba da daukar dalibai na 2023/2024.

Jami’ar  FUOYE ta kammala daukar dalibai na 2023/2024 

Sakamakon Binciken: FUOYE ta riga ta rufe daukar dalibai a hukumance musamman wadanda suka nemi shiga makarantar ta yin amfani da sakamakon JAMB. Sai dai a waje guda, jami’an makarantar na biytar sakamakon wadanda suka yi nasara a jarabawar JUPEB dan ganin ko akwai wadanda za su iya dauka. Dan haka babu cikakken gaskiya a labarin.

Cikakken bayani

Adetunmobi Jibola mai amfani da shafin Fecebook na bukatar  jama’a su yi watsi da batun cewa Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti ta daina daukar dalibai wadanda za su yi karatu a shekarrar 2023/2024, da zargin cewa dama can wa’adin 14 ga watan Nuwamba 2023 ne. Ya kuma kara da cewa akwai bukata ya musamman na dalibai sa’annan ya kuma shawarce su, da su tuntube shi ta hanyar tura masa sako kai tsaye idan har suna bukatar karin bayani.

Bisa la’akari da irin matsalar da wannan bayanin zai iya kawowa idan har ya kasance karya, DUBAWA ta yanke shawarar tantance gaskiyar batun.

Tantancewa

Da muka duba shafin facebook din Mr Jibola, mun gano cewa ya dade yana wallafa bayanan da suka shafi daukar dalibai a makarantar FUOYE, inda kusan kamar yana gabatar da kansa ne a matsayin wanda ke da wata alaka ta musamman da jami’ar ta FUOYE kuma yana iya bai wa jama’a damar samun shiga. Sai dai babu wani abu a shafin da ke nuna cewa shi ma’aikacin jami’ar ne ko kuma wadda ke da wata alaka mai nagarta da ita.

Daga nan sai Dubawa ta nufi shafin Facebook din FUOYE, inda muka gano wani bayanin da ke tsokaci kan cewa jami’ar ta rufe daukar dalibai na karo na 2023/2024 a hukumance.

“Daukar dalibai a karo na 2023/2024 ya kammala!!!” aka bayyana.

Bugu da kari, mun gano cewa mahukuntan makarantar, cikin wata sanarwar, sun shawarci wadanda ba su yi nasara a wannan karon ba da su shiga wani shirin da ta tanadar wanda ake iya yi kafin a fara jami’a.

“Mun fahimci cewa takaicin rashin samun damar shiuga jami’ar wannan karon na iya kashe wa mutun jiki, amma ka da ku damu! Muna da labari mai kayatarwa. FUOYE na da shirin da za ku iya farawa kafin ku fara karatun digirin, kuma shirin zai taimaka mu ku wajen shiryawa badi ya kuma kara muku damar samun shiga jami’ar dan daukar kowanne daga cikin kwasa-kwasai 77 da mu ke da su a jami’ar,” wani bangare na sanarawar ya bayyana.

DUBAWA ta tuntubi Wole Balogun, mai bai shugaban makarantar shawara na musamman kan harkokin kafafen yada labara, wanda ya bayyana mana cewa an kammala daukar dalibai wadanda suka yi JAMB amma kuma tana sa ran daukar wasu dalibai kalilan daga cikin wadanda suka dauki jarabawar JUPEB wadanda za su iya shiga makarantar kai tsaye.

“Akwai labarin da muka wallafa kwanan nan inda mahukuntan makarantar ke tabbatar wa masu sha’awar shiga makarantar cewa akwai gurabe wa wadanda suka yi shirin JUPEB kadai amma ba kowa ba,” ya bayyana.

A karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa mahukuntan FUOYE sun kammala daukar dalibai a hukumance na karom 2023/2024. Sai dai har yanzu suna duba sakamakon wadanda suka yi JUPEB. Dan haka wannan ya karyata zargin Mr. Jibola.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »