African LanguagesHausa

Karya! Adadin da aka bayar na yawan kararrakin kashe aure a Abuja cikin watan Janairun 2023 ba dai-dai ba ne

Zargi: Wani mai amfani da Twitter ya wallafa labarin da ke zargin wai ma’aurata 4,000 suka bukaci kotu ta kashe musu aure a cikin watan Janairun 2023.

Karya! Adadin da aka bayar na yawan kararrakin kashe aure a Abuja cikin watan Janairun 2023 ba dai-dai ba ne

Sakamakon bincike: Karya ne! Bincikenmu ya nuna mana cewa adadin ma’auratan da suka nemi kashe aurensu a kotun Abuja cikin wantan Janairun 2023 bai kai ku kusa da da 4,000ce filed in January in the FCT are way lower than 4,000.

Alkaluman da muka samu daga babbar kotun da ke Maitana wadda ke zama hedikwatar kotunan Abujan sun bayyana mana cewa kararrakin da suka danganci saki ko kashe aure a watan Janairun 2023 guda 32 ne kawai.

Cikakken bayani

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya sun numa damuwa dangane da karuwan da ake gani na mace-macen aure, musamman a ma’aurata matasa, abun da kuma ya ke kara rage kimar auren a idon wadanda ba su riga sun yi ba.

Jaridar Premium Times ma ta yi wani rahoton da ke cewa yawancin ma’aurata kan nemi kashe auratayyarsu ne saboda batutuwan da suka danganci, rashin jituwa, ko kuma wani ya yarfar da wani, bin mata/ko maza, da dai sauransu. Irin wadannan batutuwan ne ke kara mahimmancin samar da bayanai masu gaskiya ga al’umma musamman a kafofin sada zumunta irin na soshiyal mediya domin kada bayanai marasa gaskiya su mutane su baude daga hanyar da ta dace.

Wani mai amfani da shafin Twitter, Shaba Baba Muhammad (@spychief), a wani bayanin da ya yi da aka yi ta yayatawa fiye da lokuta 51,000, ya yi zargin cewa a watan Janairun 2023 kawai an shigar da kararrakin da ke neman kashe aure sama da 4,000. Ya ma kara da cewa yawancin ma’auratan ba su ma yi shekara guda da auren ba. To sai dai akwai wadanda suka kalbalanci sahihancin wannan zargin.

Tantance wannan zargin na da mahimmanci ganin yadda mutane suka rika tsokaci usn kuma ma’amala da wannan batun tun bayan da aka fara wallafawa. Yana kuma da mahimmanci a fadakar da al’umma dangane da daidai adadin wadanda suka bukaci kashe auren domin yin hakan zai taimka wajen rage yawan jita-jitar da akan baza kowace shekara. 

Tantancewa

Duk da cewa ana samun karuwa a adadin  aurarrakin da ke mutuwa yayin da matasa da ma sauran wadanda ba su yi aure ba suke alhinin lamarin, alkaluman da aka nunawa DUBAWA na wadanda suke neman kashe auren na su a bana bai kai 4,000 ba kamar yadda ake zargi.

DUBAWA ta ziyarci babbar kotun tarayya da ke Abuja, a Maitama inda ta gano cewa daga farkon watan Janairu zuwa ranar 24, mutane 32 ne suka shigar da karar neman kashe aure. Sai dai kotun ba ta baiwa mai binciken DUBAWA izinin daukar hoton takardar da ke da sunayen masu neman a kashe musu auren ba.

Ganin cewa birnin tarayyar na da kananan hukumomi shida ne, DUBAWA ta nemi fayyacewa daga masana shari’a a manyan ofisoshin shari’ar birnin daban-daban. Wadansu na bayyane daga kasa, wadanda suka hada da Kanu Agabi and Associates, wadanda suka fayyace mana cewa bacin kasancewar kananan kotuna a Abujan babbar kotun tarayyar da ke Maitama ita ce Hedikwata – ganin yadda take tsakiyar birnin Abujan.

Lauya kuma mai rajin kare hakkin kananan yara, Elizabeth Achimugu, a wata hira da ta yi da DUBAWA ta bayyana abun da kowace kotu ke la’akari da shi wajen kashe aure shi ne irin auren da suka yi.

Achimugu ta ce bisa tanadin dokokin Aure da na Sandain Aure, aure iri biyu ne; da na al’ada da kuma ta doka. Aure bisa tanadin doka ita ce aka fi sani wanda ake kira auren kotu. Wanda akan yi a wuraren ibadan da aka riga aka ba su lasisin yin hakan,ko kuma ma’aikatar da ta dace.

Ta cigaba da bayyana cewa duk kararrakin da aka shigar a babban kotun an yi haka ne saboda kotun ce hedikwata.

“Wa auren da aka daura bisa tanacin doka,  kotu ne za ta jagoranci kashe auren. Babbar kotun jiha ce za ta kashe aure bisa tanadin dokar. Dayan wanda shi ne auren al’ada shi ne irin wanda a kan yi a cocin da ba shi da lasisin daurin auren da kotu kan bayar, auren gargajiya da auren musulunci.

“A irin wannan auren wajibi ne ku tafi kotun al’ada. Muna da abun da ake kira Area Court a Abuja dan haka dole a je Area Court ko kuma kotun shari’a, amma wa duk wani auren da aka yi a karkashin doka dole a tafin babban kotu,” ta bayyana

Da DUBAWA ta je babban kotun karamar hukumar Bwari, kararraki 19 ta gani, sai dai ba ta iya samun adadin na sauran kananan hukumomin birnin tarayyar ba.

DUBAWA ta kuma tattauna da wani lauya mazaunin Abuja Stanley Alieke wanda ya ce wannan zargin ba daidai ba ne.

“Lauyoyi na samun kararrakin da suka danganci kashe aure, amma wadanda ake samu a Abuja ba su ma yi ko kusa da dubu daya a wata ba, wdansu kan sami guda daya ne kadai a rana guda, amma wannan adadin da aka bayar ba komai bane ill labarin bogi,” ya kara da cewa.

Wani lauyan shi ma, Femi Balogun, tshi ma ya ce wanna zargin da Twitter ta yi ba daidai ba ne kuma ya gota adadin da ake samu a Abuja a zahiri, nesa ba kusa ba. 

Haka nan kuma, binciken mahimman kalmomi ya nuna mana cewa ba yau ne aka fara yada irin wannan labarin ba, mun ga wanda aka yada a shekarar 2021 zuwa 2022 da yanzu kuma a 2023, kuma dukkansu sun yi amfani da adadi iri daya wato 4,000

DUBAWA ta tura sako ga mutumin da ya wallafa zargin a shafinsa dan jin inda ya samu wannan adadin ko ma da dan ya bayyana majiyarsa, sai dai bai amsa sakon ba.

Ko da shi ke wani mai suna James Alabaster IV(@alabaster_IV) ya yi gargadin cewa an dade ana yayata wannan zargin daga farkon kusan kowace shekara dan tsoratar da wadanda ba su riga sun yi aure ba. 

A Karshe

Binciken DUBAWA  ya nuna cewa kararrakin kashe auren da aka shigar a watan Janairu a Abuja baki dayansu 32 kuma ba su zo kuda da 4,000 ba, dan haka wannan zargin karya ce kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button