|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa ‘yanta’adda sun kai wa wasu al’umma hari a Sokoto, inda aka kashe mutane sama da 100 fararen hula da sojojin Najeriya 10 da dansanda daya yayin da kuma aka kama wasu don garkuwa da su.

Hukunci: Karya ce, DUBAWA bata samu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da labarin kisan gilla irin wannan ba da aka yi zargi, kuma an gaza ganin wannan wajen da aka yi lamarin kuma sojoji da ‘yansanda sun tabbatar da cewa babu wannan ta’addanci da ya faru a jihar Sokoto.
Cikakken Labari
A ranar 5 ga Oktoba, 2026 wani shafin Facebook mai suna Hausaland Magazine, yayi da’awa cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai farmaki a Garin Gobir Gindin a jihar Sokoto, inda aka kashe fararen hula 100 da sojoji 10 da dansanda guda daya.
Wannan wallafa kamar yadda aka alkinta a (nan) ta hada da hotuna dauke da gawarwaki kwance a kasa, wasu kwance da kayayyaki irin na sojoji yayin da wasu ke sanye da kaya irin na fararen hula.
Wallafar ta bayyana lamarin da zama “kisan kiyashi” da “yaki kan Hausawa” inda aka alakanta abin da harin “Fulani ‘yanta’adda.”
Wani bangare na taken labarin na cewa “Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ake cewa an kulla Fulani ‘yanta’adda sun kai farmaki Garin Gobir Gindin harin da ke zama mai muni, an kashe sojojin Najeriya 10 da dansanda guda daya, an kama wasu an yi garkuwa da su, an halaka Hausawa sama da 100 an watsar da gawarwakinsu a kan titi, duk bayan sa’a ana kara samun wadanda suka rasu. Ina batun zaman lafiyar? Ina gwamnati? Ina yin adalci?
Wannan wallafa ta samu martani da dama wadanda da alama sun gaskata kuma suna kambama da’awar.
Jay Mafulul ya rubuta cewa, “Ya kamata Hausawa da ke Plateau a birnin Jos su kalli wannan, kullum suna murna idan Fulani suna kisa. A yanzu za su fahimci waye hakikanin shedanin.”
Wani mai amfani da shafin mai suna Onuigwe Emmanuel, ya rubuta cewa “ Ka ci gaba da neman amsa har sai Fulani sun kammala kashe Hausawa.”
“Yau Talata ce 6 ga wata ba 5 ga wata ba, Shin wannan da gaske ne?” a cewar Mathew K Zogo da ya kalubalanci da’awar.
DUBAWA ta gudanar da bincike kan da’awar, duba da yanayin matsalar tsaro da ganin wannan na iya haifar da fargaba da rudani.
Tantancewa
DUBAWA ta nazarci bayanan labarin kasa na yankin da bayanin yankin a jihar Sokoto. Mun gano cewa babu wani gari mai suna “Garin Gobir Gindin” a jihar.
Haka kuma mai da’awar yace harin ya faru ne a ranar Talata 5 ga Oktoba,2026, amma ranar 5 ga Oktoba,2026 a ranar Litinin ce.
DUBAWA ta kuma nazarci yanayin hoton don gano asalinsa, ko kuma za a ga wani labari da aka yada a shafin intanet irin wannan.
Bincikemu bai ga wata kafa da ta sanya wannan hoto ba, ko ta alakanta shi da kai farmaki a Sokoto kamar yadda yayi zargi.
DUBAWA ta tuntubi mukaddashin darakta mai kula da hulda da jama’a a rundunar sojan na Najeriya shiya ta 8 mai kula da sashi na biyu a rundunar FANSAN YAMMA Lutanal Kanal Olaniyi Osoba, wanda yayi watsi da wannan da’awa.
“Babu wani hari mai kama da wannan wanda yayi sanadi na rasa rayuka da dama a wannan jiha.”
Haka shima jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda a jihar Sokoto DSP Ahmed Rufa’i, yayi watsi da wannan da’awa, yana mai cewa “wannan lamari bai faru ba a jihar Sokoto.”
Bayanai da aka tattara daga bangaren jami’an tsaro a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya babu inda aka samu irin wannan labarin mummunan kisa, bayani guda da aka samu a irin wannan lokaci ya faru shine na ranar Lahadi 4 ga Oktoba,2026 a kauyen Ungushi na garin Kebbe inda ‘yanbindigar suka kashe mutane biyu da raunata wani kamar yadda rundunar ‘yansanda a jihar ta tabbatar.
Harin na Ungushi bai yi daidai da yawan mutanen da aka ce sun mutu ba a wancan hari da aka yi da’awarsa ba da Hausaland Magazine ta yi zargi.
A Karshe
Da’awa da Hausaland Magazine tayi cewa an kashe fararen hula sama da 100 da sojoji 10 da dansanda daya a harin da aka kai a “Garin Gobir Gindin” a jihar Sokoto karya ce.
An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai.
