African LanguagesHausa

Karya! Gabon ba mambar Ecowas ba ce, dan haka kungiyar ba za ta iya sanya ma ta takunkumi dan juyin mulkin da sojojinta suka yi ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Dan mayar da martani dangane da juyin mulkin da sojojinta suka yi, Ecowas na iya sanyawa Gabon takunkumi a matsayinta na mambar kungiyar

Karya! Gabon ba mambar Ecowas ba ce, dan haka kungiyar ba za ta iya sanya ma ta takunkumi dan juyin mulkin da sojojinta suka yi ba

Sakamakon Bincike: KARYA. Kasar mai amfani da harshen faransanci ba mambar kungiyar Ecowas ba ce dan haka ba takunkumin da kungiyar za ta iya sanya ma ta. Ita mamba ce ta Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Tsakiyar AFirka (ECCAS)

Cikakken bayani

Yayin da hankalin duniya ya koma ga gwagwarmayar iko da ake yi a jamhuriyar NIjar bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin da ya hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, sojojin Gabon su ma sun sanar da cewa sun anshe mulki ba tare da zubar da jini ba daga Ali Bongo, wanda ya lashe zaben shugbaban kasar da aka kammala dan yin wa’adi na uku a madafun ikon kasar. Kafin juyin mulkin, ya shafe shekaru 14 yana mulkin kasar bayan da ya karbi ragamar daga mahaifinsa Omar Bongo, wanda shi kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 42 kafin ya rasu a shekarar 2009.

Wannan lamarin da ya afku a Gabon ya sa ta zama kasa ta bakwai a jerin kasashen da dakarun sojojinsu suka yi juyin mulki a yankin kudu da saharar Afirka tun shekarar 2020. Domin yakin da wannan abun da ya zama rikici yanzu, shugaban Ecowas Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban kasar Najeriya ya yi magana dangane da juyin muli a yankin yammacin Afirka da kakkausar murya. Kawo yanzu, kungiyar ta tabbatar da duk barazanar da ta yi wa wadanda suka yi juyin mulkin inda ta dauki matakai masu tsauri a kan Nijar sakamakon juyin mulkin. Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun nuna rashin amincewarsu da matakan da Ecowas din ta dauka.

 Bayan da aka sami labarin juyin mulki a Gabon, ‘yan Najeriya sun yi tunanin Ecowas za ta dauki matakai makamantan wadanda ta dauka a kan Nijar kuma da yawa sun bayyana tunaninsu suna amfani da kalaman da ke nuna rashin mutunci.

Misali shi ne wani mai amfani da shafin Facebool mai suna Maiyegun’s Diary Politico, wanda ya kwatanta Tinubu da Pablo Escobar, wanda ya shahara wajen sayar da miyagun kwayoyi a yankin kudancin Amurka. Ya ce, “(Me Tinubu) Pablo din Ecowas zai yi dangane da Ali Bongo na Gabon yanzu? Zai shiga ya mamaye Gabon?

Daga 30 ga watan Agusta, labarin ya sami tsokace-tsokace 738, mutane sun raba sau 105 sa’anann kuma wasu sama da 1,200 sun yi ma’amala da labarin. Mutane 628 sun fahimci cewa gatse ne saboda sun yi amfani da alamar dariya.

Wani mawallafi kuma Lineaker Kigunddu tambaya ya yi, ya na cewa me kungiyar za ta yi a kan juyin mulkin da ya hambarar da iyalin da ya shafe shekaru 56 a kan kujerar shugabancin kasar.

Ya rubuta, “Iyalin Bongo (Uba da Da) wadanda suka yi mulki a Gabon tun daga shekarar 1967, wato a hade sun shafe shekaru 56 ke nan suna rike da iko, yanzu an samu an yi fatali da mulkinsu. Bari mu gani idan Ecowas za ta bude bakinta ta kalubalanci wannan juyin mulkin.”

Daga wadannan shafukan ne muka lura cewa mutane da yawa sun zaci Gabon na yankin Yammacin Afirka ne kuma tana kungiyar Ecowas. Wannan rashin sanin ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance batun.

Verification

Binciken mahimman kalmomin da muka yi dangane da kasar ya nuna mana cewa tana yankin Tsakiyar Afirka ba Yammacin Afirka ba kamar yadda wasu suka dauka. Kasar na da iyaka da Kamaru daga yankin arewacinta yayin da ta ke makotaka da Jamhuriyar Kwango da Equatorial Guinea a sauran yankunanta. 

Bayan haka, mun duba jaddawalin kasashen da ke kungiyar ECOWAS inda muka ga cewa Gabon ba ta cikinsu. Kasashe mambobin Ecowas sun hada da  Senegal, Burkina Faso, Cape Verde, Cote D’Ivoire, Gambiya, Laberiya, Mali, Ghana, Saliyo, Guinea da Guinea Bissau. Najeriya na da iyaka da kasashen Nijar, Togo, jamhuriyar Benin, a jimilce kasashe 15 ke nan.

Mazaunin cibiyar gudanarwar ECCAS na Gabon, kuma a shekarar 1964 aka girka kungiyar da yarjejeniyar Brazzaville  . Kungiyar ce ke da alhakin tabbatar da cigaba da dorewar tattalin arziki a yankin tsakiyar Afirkar.

 A Karshe

Gabon ba kasa ce a yankin yammacin Afirka ba, kuma ba ta kungiyar Ecowas. Gabon na daga cikin kasashen da suka girka Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Tsakiyar Afirka wato ECCAS, dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button