African LanguagesHausa

Karya! Kungiyar ‘yan banga ta Filani ba ta yi rajista da CAC kamar yadda ake zargi ba.

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Charles Oputa, wani mawakin Najeriya, ya wallafa wasu takardun rajista da CAC, wato hukumar da ke rajistar kamfanoni da masu sana’o’i a Najeriya, wanda ya ke zargi mallakar wata kungiyar ‘yan bangan Filani ne

Karya! Kungiyar ‘yan banga ta Filani ba ta yi rajista da CAC kamar yadda ake zargi ba.

Sakamakon bincike: Binciken ya nuna mana cewa kungiyar da ya ke zargi ba ta a cikin kundin rajistar CAC, kuma bacin haka, satifiket din na bogi ne wanda aka gyara dan yaudarar jama’a

Cikakken bayani

Mawakin Najeriya Charles Oputa, wanda aka fi sani da Charly Boy, kwanan nan ya wallafa wani  labari a shafinsa na X mai zargin cewa “NOMAD VIGILANTE NIGERIA LTD,”wata kungiyar ‘yan banga Filani, ta yi rajista da Hukumar CAC. Sa’annan ya wallafa satifikrt din yin rajistar tare da wannan bayanin nasa. Har ila yau da wannan karin bayanin wadda fassarar ke daga kasa bayan abun da ya rubuta da turanci: 

“Can U imagine? IT’S NOW OFFICIAL – The Fulani “National” Vigilante Organisation! Now, INSURGENTS CAN have wings! IPOB was proscribed as a Terror Org. Sunday, IGBOHO & friends were imprisoned. BUT, GUN CARRYING, Kidnap & Terror Organisation was REGISTERED!! We Neva Ceeee shomtin!!

“Ku na iya fahimtar wannan? YANZU A HUKUMANCE YA KE – Kungiyar “Kasa” ta ‘Yan banga Filani! Yanzu “YAN TAWAYE na iya samun fuka-fuki! An kira IPOB kungiyar ‘yan ta’adda. Ranar Lahadi, IGBOHO da abokansa sun je gidan kasi. AMMA MASU DAUKAR BINDIGOGI, Satar jama’a da kungiyar ta’addanci ta yi RAJISTA!!! Ba mu ga komai ba tukuna!!

A watan Janairun 2024, shugaban kungiyar Filani ta Miyetti Allah ta kasa, ya kirkiro wata kungiyar ‘yan banga na makiyaya wadda za ta dafawa hukumomin tsaron kasar musamman a jihar Nasarawa. Wannan batun bai tafi salin alin ba domin an sami masu  damuwa da kuma adawa daga mambobin al’umma. DUBAWA ba za ta iya tantance gaskiyar wannan da’awar da Mr Oputa ya yi ba, tun da abu ne da aka wallafa a shafin Facebook sosai kamar yadda mu ka gani a shafukan da suka hada da wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, wannan, da wannan.

Yawan martanonin da wannan batun ya janyo ne ya sa muka dauki nauyin tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

Mun dauki sunan Kamfanin da lambar rajistar da ke kan satifiket din wanda aka ce sun samu daga hukuma CAC da yardar cewa lambar rajistar ce ta gaskiya. Sai dai da muka duba shafin CAC da wadannan lambobin ba mu sami komai ba. Wannan ne ya tabbatar mana cewa kungiyar ba ta yi rajista da CAC ba.

Karya! Kungiyar ‘yan banga ta Filani ba ta yi rajista da CAC kamar yadda ake zargi ba.

Daga sunan kamfanin da lambobin rajistar babu ko daya a kan shafin hukumar CAC.

Bayan da muka ga haka sai muka yi nazarin hoton ta yin amfani da manhajar Invid, wadda ke tantance hotuna. Sakamakon ya bayyana mana cewa an taba “lambobin rajistar” da kuma “sunan kamfanin.” Wannan ne ma ya kara tabbatar mana cewa an gyara hoton satifiket din ne kawai dan haddasa husumi da yada labaran karya.

Karya! Kungiyar ‘yan banga ta Filani ba ta yi rajista da CAC kamar yadda ake zargi ba.
Karya! Kungiyar ‘yan banga ta Filani ba ta yi rajista da CAC kamar yadda ake zargi ba.

Hujjojin da ke nuna cewa an gyara lambobin ne, wato ba lambobi na ainihi wadanda suka kasance a kan satifiket din ba ne

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa “NOMAD VIGILANTE NIGERIA LTD” ba shi cikin kundin bayanan hukumar CAC. Har wa yau shi kan shi satifiket din da aka yada na bogi ne kawai dan a yada bayana da za su yaudari jama’a.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »