Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: An wulakanta shugaban hukumar zabe CENI a bainar jama’a bayan da ya bayyana sakamakon bogi wanda aka yi aringizo a cikinsa.

Sakamakon bincike: Karya ne. Shugaban CENI namiji ne kuma hotunansa da sahihan kafofin yada labarai suka wallafa shi bai kama da macen da aka gani ba a bidiyon.
Cikakken Sakon
A lokacin zaben shugaban kasa (presidential election) a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango (DRC) sai ga wani bidiyo ya bayyana, wanda wata mai amfani da shafin Twitter ta wallafa da zargin cewa shugabar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (CENI) ya fuskanci tozartawa bayan da ta bayyana sakamako mara inganci da aka yi aringizon kuri’u a cikinsa.
Mai amfani da shafin na X, Nkirukamma (@SabinaNkiru), ta rubuta “Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango (DRC) ya fuskanci wulakanci bayan da ya bayyana sakamako mara inganci da aka yi aringizo. ”
A bidiyon an ga yadda wata mata ke kokarin kwatar kanta bayan da wasu masu zabe suka afka mata da duka a tashar kada kuri’a.
Ms Nkirukamma na kokari ne ta alakanta labarin da abin da ke faruwa a Najeriya bayan da a ake ta kiraye-kirayen samar da sauyin shugabanci a Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriyar (INEC) .
Ms Nkirukamma ta kara da cewa “Idan INEC da makusantanta za su tsorata da wani abu kamar haka, da mokomar da muke da ita a yau da ta inganganta.”
Wannan wallafa ta samu masu kallo (views) 719,000, da masu sake yada labarin (repost) 2,048, da masu tsokaci (Comments) 492, da wadanda suka nuna sha’awarsu (Likes) 2,999 da masu maki (bookmarks.) 371.
Daga irin tsokaci da mutanen kan yi wasu sun amince wasu ma na sake yada wannan da’awa ta Ms Nkirukamma.
“Ranar za ta zo nan ba da dadewa ba.” A cewar Kingboy (@kingboy02458754).
“ Ina fatan ‘yan Najeriya za su farka daga baccin da suke yi .” A cewar Royal King (@iam_royalkingg).
Duba da irin yadda wadannan sakonni ke iya zama masu hadari dole muka shiga bincike don tantancewa.
Tantancewa
Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a rahotannin kafar yada labaran Aljazeera (report) dangane da shugaban da ke kan mulki Felix Tshisekedi da kuma sake zabe a kasar ta Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango. Rahoton ya nunar da cewa Mista. Denis Kadima wanda aka bayyana a matsayin “shugaban zabe” ya bayyana cewa za a gabatar da sakamakon zabe ga kotun kundin tsarin mulkin kasa don ta tabbatar da shi.
Mista. Kadima shine kafar yada labarai ta Voice of Africa (VOA) ta bayyana a matsayin shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (CENI).
Shine dai aka wallafa hotonsa a kafar yada labarai ta kasa da kasa mai suna Breaking News Network (BNN) wacce ta bayyana “Dennis Kadima, a matsayin shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta CENI.
Duk da haka wani shafin Blog mai suna Fatshimetrie, ya ba da rahoto inda ya ce wata mata ta fuskanci tozartawa a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango saboda dalilinta na zabe. Mujallar ta bayyana yadda mace ta fuskanci tozartawa saboda ta zabi jagoran adawa Moise Katumbi a yankin Grand Kasai. Shafin ya nemi da a hukunta wadanda suka aikata cin zarafin. Har ila yau ya kuma wallafa wani labarin daga Kananga, daya daga cikin biranen na Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango inda wata matar ma mai sa idanu kan harkokin zabe ta fuskanci hari a lardin Apollo.
A Karshe
Da’awar karya ce. Shugaban hukumar CENI namiji ne kuma hotuna daga kafafan yada labarai sahihai sun nuna hotunansa wadanda sun sha bambam da matar da ake nunawa wacce aka kaiwa farmaki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Akwai ma wani rahoto da ya nunar da yadda aka aikata tozartawa mai alaka da jinsi a lokutan na zabuka.