Cikakken bayani
Darajar Naira ta samu mummunar koma baya a kasuwa. Rahoton da Business Day ta fitar ya nunar da cewa N1,851 daidai take da Dalar Amurka guda daya tilo a kasuwar bayan fage yayin da ake samun dalar guda akan Naira 1,571.3 a hukumance ya zuwa ranar 21 ga watan Fabrairu, 2024.
Ana tsaka da wannan yanayi na rashinn tabbas an rika watsa labarai a shafin WhatsApp inda aka rika kwatanta Naira da Dalar Amurka dama yadda hakan ke tasiri ga zamantakewa.
Shafin DUBAWA ya gano an yada wannan da’awa a shafin X a 2020kamar yadda ake gani nan da can.(here da here.)
Anan kasa ga wasu manya daga cikin irin da’awar da ake yi dama yadda muka lalubo hakikanin gaskiya.
Da’awa ta 1: Naira (0.80 k) shike daidai da dalar Amurka daya a 1980.
A cewar kafar yada labaran BBC Pidgin a shekarar 1980 ana siyar da dalar Amurka kan Kobo 0.55k. Sai dai bincike da aka gano daga hukumar da ke lura da canjin na kudade CEIC ta nunar da cewa Dala ta taba fuskantar kankanta da ta kai 0.530k a kudin Najeriya a watan Nuwamba 1980.
Hukunci : KARYA NE
Da’awa ta 2: “Yan Najeriya na hawa motoci kanana da bas-bas da ta dakon kaya da Peugeot da ake hadawa a Kaduna da Volkswagen da ake hadawa a Legas.
Wasu bayanai da suka fita daga hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati Bureau of Public Enterprise (BPE) sun nunar da yadda gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniya da kamfanin hada motoci na Peugeot da ke Paris a ranar 11 ga watan Agusta 1972. Yarjejeniyar da aka cimma na da burin ganin ana samar da motocin daukar fasinja a Najeriya a rika kuma harhada motocin Peugeot. An kuma kafa kamfanin a rukunin masana’antu na Kakuri a jihar Kaduna.
A cewar Motoring World International, tun a shekarun 1972, gwamnatin Najeriya tayi hadin gwiwa da kamfanin Volkswagen na kasar Jamus inda aka samar da kamfani da za a rika harhada motoci a kan babbar hanyar Legas zuwa Badagry. Bayanan sun nunar da cewa ya zuwa 1981 wurin harhada motocin na Volkswagen na samar da motoci 30,000 a duk shekara.
Hukunci: GASKIYA CE !
Da’awa ta 3: Leyland na samar da motocin dakon kaya da bas-bas a Ibadan da ANAMCO a Enugu
Bayanan harkokin kasuwanci a Najeriya dama bayanan da aka lalubo ta hanyar intanet a Finelib.com sun nunar da cewa Leyland Motor Company an kafa shi a 1976 , kamfani ne na harhada motoci da suka hadar da kananan bas-bas da bas da ke yawon cikin gari da kananan motocin dakon kaya da masu daukar shara da sauran kayayyaki da kayan gyara, kamafanin an kafa shine a Ibadan.
ANAMCO kuwa ya samu ne bayan wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnatin Najeriya da Daimler AG da ke zama abokin hulda na farko kuma abokin zuba hannun jari. An kafa kamfanin a ranar 17 ga watan Janairu,1977 aka kuma bude kamfanin a ranar 8 ga watan Yuli 1980 inda ya fara fitar da motar daukar kaya ta farko a watan Janairu 1981.
Shelkwatar kamfanin an kafa ta a birnin Enugu, kamar yadda bayanan hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati (BPE) ya nunar.
Hukunci: Gaskiya ce!
Da’awa ta 4: Kamfanin Steyr ya samar da motar aikin gona tarakta ta farko a Bauchi.
Hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati Bureau of Public Enterprise (BPE) ta bayyana Steyr Nigerian Limited Bauchi, a matsatyin babban kamfani hada motocin aikin gona mai taya hudu.
Kafar yada labaran The People’s Gazette ita ma a shekarar 2021 ta ba da rahoton cewa kamfanin da ke a Bauchi me shekaru sama 40 na hada motocin aikin gona da masu daukar kaya da bas-bas.
Hukunci: GASKIYA CE!
Da’awa ta 5: Vono da ke Lagos na hada kujerun mota
Vono, an kafa shi a 2016, reshe ne na kamfanin Vitafoam Nigeria Public Limited Company (PLC). a cewar shafin kamfanin yana samar da kujeru na wuraren shakatawa da ofisoshi da gidaje da hukumomi na gwamnati.
Hukunci: Karya ce!
Da’awa ta 6: Exide a Ibadan na samar da batura wadanda ake rarraba su a Afurka ta Yamma
Kamfanin da aka bayyana ya kamata a ce yana da adireshin intanet, wanda hakan ya sanya ake tantamar kasancewarsa ganin cewa ma yana fitar da kayayyakinsa a kasashe na Afurka ta Yamma. Excide shine kadai kamfanin da ka gano a shafin na intanet wanda kuma yana da reshene a Kalkota kasar Indiya
Kamfanin da ke a Indiya ya kasance kan gaba wajen samar da batiri domin motoci da baturan da ake amfani da su a masana’antu.
Hukunci: KARYA CE!
Da’awa ta 7: IsoGlass da TSG a Ibadan suna samar da glashin gaban mota
Kamar yadda a shekarar 2014 jaridar Business Day ta nunar Isoglass na samar da glashin mota sama da shekaru 30, kafar yada labaran ta bayyana wannan kamfani a matsayin “abin dogaro” ga kamfanoni irinsu ANAMCO da Volkswagen.
A cewar gwamnatin Najeriya da kamfanin da ke samar da motoci na kasa Federal Republic of Nigeria, the National Automotive Council (NAC) da Tripex Glass (TSG) ma na samar da glass ga kamfanonin samar da motoci a Najeriya. Ya kasance kamfani da aka kafa tsakanin 1970 da 1980.
Hukunci: GASKIYA CE!
Da’awa ta 8: Ferodo a birnin Ibadan na samar da birkin mota da fefen kuloci.
Ferodo ya kasance kamfanin kasar Birtaniya wanda ke samar da birkin motoci ya samar da kayayyaki nagartattu ga sama da ababen hawa miliyan 25 a shekara, kuma masu amfani da kayan kamfanin na alfahari da kamfanin a fadin duniya.
Sai dai gwamnatin Najeriya da Kamfanin da ke samar ababan hawa na kasa a Najeriya Federal Republic of Nigeria, National Automotive Council (NAC) ba su taba bayyana wani kamfani da sunan na Ferodo ba a matsayin kamfani da ke a kasar cikin jerin kamfanoni da take da su wadanda ke samar da birkin mota da fefen kuloci.
Hukunci: KARYA CE!
Da’awa ta 9: Dunlop na samar da tayar mota a Legas yayin da Michelin ke samnar da taya a birnin Fatakwal
Dunlop na aiki a Najeriya (operating in Nigeria) tun daga 1961 kamar yadda shafin intanet na kamfanin ya nunar, kamfanin na samar da tayar motoci da ke gyaran titi da tarakta ta noma, har ila yau kamfanin yayi suna (recognised) a matsayin na gaba wanda ke samar da tayoyi na mota manya da kanana a kasuwar siyar da tayar mota a Najeriya.Ya kuma kasance kamfanin tayar motar da ya samu lambar amincewa ta E.C.E shedar da ke ba da damar a fitar da tayar har zuwa kasashen Turai. Ya kuma kasance kamfani na farko a Afurka baya ga Afurka ta Kudu da suka samu lambar ISO 9002 certification.
Michelin na gudanar da harkokinsa a wasu kashen Afurka (African countries,) ciki kuwa har da Afurka ta Kudu da Kamaru da Najeriya. A yayin tataunawa da jaridar Business Day, Manajan darakta a kamfanin na Michelin Chioma Alonge, ta bayyyana cewa kamfanin samar da tayar na da reshe a birnin Fatakwal kuma shelkwatarsa tana a birnin Legas. Misis Alonge tace Michelin na gudanar da harkokinsa a Najeriya sama da shekaru 63.
Hukunci: GASKIYA NE.
Da’awa ta 10: Thermocool da Debo na samar da firjin kankara da na’urar sanyaya daki wadanda ‘yan Najeriya ke amfani da su.
Haier Thermocool ya kaance brand na PZ Cussons, wanda ya fara (started off) a kasar Saliyo a lokacin da wadanda suka kafa kamfanin, George Paterson da George Zochonis suka fara kasuwanci da kasar Birtaniya (UK). Haier Thermocool na gudanar da harkokinsa a Najeriya operating in Nigeria sama da shekaru 40 kenan.
Hukunci: YAUDARA CE
Da’awa ta 11: Kayayyaki da ake samarwa a a kamfaninUnited Nigeria Textile Limited (UNTL) a Kaduna da Chellarams a Legas kaya ne da ake samar da su daga audugar da aka samota a Najeriya.
Kamar yadda ya bayyana a makalar da aka wallafa a Cambridge University Press asalin audugar ana nomanta ne daga Najeriya domin sarrafawa a kamfanin na UNTL , domin shi UNTL na hadin gwiwa ne da kamfanin da ke Hong Kong na Cha Limited group da Northern Nigeria Development Corporation.
Haka nan shima kamfanin Chellarams Public Limited Company (PLC), wanda asalin mai kamfanin dan kasar Indiya ne da ya dawo Najeriya ya bude shagonsa a Legas Najeriya. Kamar yadda mujallar Forbes Africa ta wallafa. Daga bisani suka bude katafaren shago na siyar da kayayyaki da suka hadar da kayan shafe-shafe da kayan sawa da laturoni tsakanin 1950 zuwa 1992.
Hukunci: GASKIYA NE!
Da’awa ta 12: Kamfanin LPG gas na ajiye gas a manyan tukwane da ake samarwa a kamfanin NGC da ke Ibadan.
Kamar yadda bayanan hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati Bureau of Public Enterprise (BPE), ta nunar kamfanin samar da gas na Najeriya (NGC), wanda ke zama wani bangare na kamfanin mai na kasa NNPC ya zama kamfani mai rijista a ranar 25 ga watan Yuli, 1981, sannan ya fara gudanar da aikinsa a 1988.
Hukumar ta BPE ta kara da cewa NGC na rarraba gas zuwa ga masu siyan kayansa da kasuwanni da wasu wurarenta a yankin Afurka ta Yamma ECOWAS , tana samar da bututu na tura gas da ba da shawarwari da tsare-tsare ga gwamnati kan yadda za ta yi amfani da gas dama farashinsa.
Acewar BPE, manyan bututun man a Najeriya sune the Escravos-Lagos pipeline, Oben-Ajaokuta pipeline da Alakiri-Obibgo, Ikot Abasi.
Hukunci: Karya ne!
Da’awa ta 13: Ana samar da wayar Cables a kamfanin samar da waya na Nigerian Wire and Cable, Ibadan, da NOCACO a Kaduna, da Kablemetal a Lagos da Port Harcourt.
A cewar Nigerian Wire and Cable (PLC), an samar da kamfanin a 1974 don samar da waya da ake bukata a kasuwar wayar wuta a Najeriya.
SavyCon, da ke zama fitaccen kamfani me aikin hada-hadar samar da wayar ga masu bukata ya bayyana kamfanin na Northern Cables Processing and Manufacturing Company (NOCACO) a matsayin kamfanin da aka kafa a 1978. Yana samar da wayar wuta mai inganci da za a iya amfani da ita a cikin gida Najeriya da kasashen ketare tun daga 1980. Kamfanin babban reshensa na a jihar Kaduna ne.
Sai dai shi kuma Kabelmetal kamfanin Kabelmetal ne na Hannover Germany ya samar da shi an kafa shi ne a shekarar 1966. Kabelmetal Nigeria PLC da ke zama bangare na wancan kamfani ya zama jagaba wajen samar da waya a Najeriyar yana kuma da babban rashensa a jihar Legas.
Hukunci: AKASARI GASKIYA NE!
Da’awa ta 14: Bata da Lennard sun kasance ja gaba a wajen samar da takalma da ‘yan Najeriya ke sawa, kuma kayan hada takalman a cikin gida Najeriya ake samar da su ba daga kasashen ketare ba.
Kamar yadda bayanai da aka samo daga shafin na Bata (Bata’s website) suka nunar kamfanin ya bude babban shagonsa na farko a Najeriya a 1932. Kamfanin sai ya hada wata hadaka da ake tattara masa kayan aiki a jihar Kano kamar fatu da auduga da roba. An bude sabon kamfani na zamani a 1935 da 1965
Adexen, kamfanin da ke da ruwa da tsaki kan sha’anin samar da ma’aikatan kamfanoni a Afurka, ya bayyana cewa Lennard Nigeria PLC yana harkar da ta shafi samar da takalmin sawa da kasuwancinsa, ya zama cikakken kamfani a ranar 24 ga watan Fabrairu, 1953, ya kuma kasance reshe ne na kamfanin Greenlees Lennards Limited, England wanda aka ba shi sunan Lennards Nigeria Plc a ranar 26 ga watan Maris 1991.
Wata makala da aka fitar a Fortune and Class ta bayyana cewa Bata da Lennards sun yi harkokin hada-hadarsu a a Najeriya, sai dai ana fitar da takalman da ake zuwa a gyara su sosai a kasashen waje.
Hukunci: AKWAI KANSHIN GASKIYA!