African LanguagesHausa

Kwararru sun ce shan Malt da Madara ba ya kara jini a jiki

Zargi: Masu amfani da soshiyal mediya na zargin cewa shan malt da madara na kara yawan jini a jikin mutun. 

Mutane da yawa sun yi imanin cewa idan aka hada lemun kwalban da aka fi sani da malt tare da madara aka sha, zai kara yawan jini a jiki. Dan haka masu amfani da yanar gizo suka fara rubuta bayani dangane da batun suna wallafawa. 

Alal misali a shekarar 2017 wani mamban shafin Nairaland ya wallafa wani labarin da ke ikirarin cewa malt da madara na kara yawan jini a jikin mutane.

Haka nan kuma a shekarar 2020, shafin Zikoko wanda sananne ne a Najeriya ya wallafa wasu daga cikin hanyoyin da iyaye mata a Najeriya za su iya amfani da su wajen kara jini a jikin ‘ya’yansu. Malt da Madara ne ya kasance farko a cikin jerin abubuwan.

A shekarar 2021 wani shafin labaran ya sake raba labari mai taken “hadin da ke kara jini”. Shafin ya ma wallafa sunayen asibitocin da ke bayar da hadin ga wadanda ke zuwa bayar da jini kyauta dan ya kara musu yawan jini a  jikinsu.

A waje guda kuma, a wani fim na Nollywood wanda Odunlade Adekola da Olaniyi Afonja suka yi. Olaniyi Afonja ya yi zargi irin wannan wanda watakila yana daga cikin irin abubuwan da suka sanya jama’a daukan zargin a matsayin gaskiya. 

Tantancewa

DUBAWA ta fara da duba mahimman kalmomi wanda ya kai ta ga labaran da aka riga aka ambato daga sama. Wannan ya nuna cewa kusan kowa na sane da cewa ana amfani da madara da malt dan kara jini. To sai dai duk wani binciken da muka yi bai kai mu ko’ina ba wajen ganin ko ana iya samun hujjar hakan a kimiyance. 

Dan haka ne muka nemi jin ta bakin kwararru dangane da wannan batun. 

Bayanai daga Kwararru 

Wata farfesa a sashen lafiya da abinci mai gina jiki a jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, Beatrice Ogunba ta fadawa jaridar Punch cewa babu wata hujja a kimiyance wadda ta tabbatar da zargin, ta ce ‘yan Najeriya ne kawai ke cewa ana iya hada malt da madara dan kara jini. 

Adedeji Moses shi ma kwararre ne a fanin koyar da yadda ake cin abinci mai gina jiki wanda kuma shi ne jagora a Adedamz Nutrition Consult, kuma ya bayyanawa DUBAWA cewa hadin malt da madara ba ya wani karawa mutun jini a jikin shi.

“Duk da cewa ana ganin shi a asibitoci da yawa inda bayan mutane sun bayar da jini, ake ba su madara ko malt ko hadin abubuwan biyu. Mutane ne kawai suka yi tunanin cewa ana ba su wadannan abubuwan dan kara yawan jinin da ke jikinsu bayan da suka yi kyautan jinin.”

Mr Adedeji ya ce ana iya baiwa mutun wannan hadin kuma duk da haka ya kasance ba shi da jinin.

“Wannan na iya faruwa idan har mutun ba ya cin irin nau’o’in abincin da ya dace, abincin da ke dauke da sinadaran da ke kara jini irinsu iron, copper, folate da Vitamin C,” ya ce.

Kwararre kan abinci mai gina jikin ya ce duk da cewa madara na dauke da sinadaran Calcium da vitamin D (masu inganta kashi) da wadansu karin sinadarai masu inganta lafiyar kashi, yana kuma samar da protein. A waje guda kuma, Malt na bayar da kuzari.

“Suna dauke da sinadarai masu mahimmanci. Suna rage damuwa, inganta yanayin narkar da abinci, inganta lafiyar zuciya da kuma rage yawan mai ko abin da aka fi sani da colesterol a turance a jiki. Sai dai madara shi kan shi ko malt ko kuma su biyun a hade ba su kara yawan jini.”

Emmanuel Oyebamiji shi ma kwararre a fannin abinci mai gina jiki a asibitin jami’ar Ibadan shi ma ya ce madara da malt ba hadin kara jini ba ne.

“Duk da cewa madara na dauke da sinadaran calcium da iron da kowani madara ba ne ke dauke da sinadaran domin akai madara iri-iri.

A Karshe

Wannan zargin ba gaskiya ba ne domin ba mu ga wani binciken da ya goyawa wannan zargin baya ba. Kuma kwararru a fanin abinci sun ce hadin ba ya karawa mutun jini. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button