African LanguagesHausaMainstream

Matar da ke shan tabar Hookah a hoton da ke yawo ba ‘yar takarar gwamnar jihar Legas a inuwar LP ba ce kamar yadda ake zargi

Zargi: “Hoton matar da ya bazu ko’ina a soshiyal mediya tana shan tabar hookah ‘yar takarar mataimakiyar gwamna ne a jam’yyar LP a jihar Legas”

Matar da ke shan tabar Hookah a hoton da ke yawo ba ‘yar takarar gwamnar jihar Legas a inuwar LP ba ce kamar yadda ake zargi

Sakamakon Bincike: KARYA. Bincikenmu ya nuna mana cewa matar da ke shan tabar hookah a hotun da ya bude gari ba ‘yar takarar mukamin mataimakiyar gwamna a jam’iyyar LP a jihar Legas, Pricess Abiodun Oyefusi ba ce.

Cikakken bayani

Yayin da zabukan da aka daga na gwamnoni a jihar Legas da sauran jihohin kasar ke karatowa, yakin neman zabe ya kara zafi.

Kwanan nan, hoton wata mace mai shan tabar hookah ya bi ko’ina a duniyar yanar gizo inda ake zargin cewa matar da ke takarar neman mukamin mataimakiyar gwamna a jihar Legas tare da abokin takararta Gbadebo Rhodes-Vivour, a karkashin inuwar jam’iyyar LP ce.

‘Yar takarar mukamin mataimakiyar gwamnan jihar Legas ita ce Princess Abiodun Oyefusi, wadda abokin takararta ya kwatanta a matsayin “abokiyar takara mai hazaka da kwarewa.” Oyefusi (@PrincessOyefus1) ta kasance tsohuwar ‘yar takarar sanata a mazabar kudancin Legas  a inuwar jam’iyyar PDP a shekarar 2019.

Ranar litin 13 ga watan Maris 2023 mai amfani da shafin Twitter Ayekooto (@DeeOneAyekooto) ya yi zargin cewa matar da ke cikin hoton ‘yar takarar mataimakiyar gwamnan ce a jam’iyyar LP. 

“Ga ‘yar takarar mataimakiyar gwamna a wata jam’iyya a jihar Legas,” sakon ya bayyana.

Mutane sama da miliyan guda suka kalli bidiyon a yayin da wasu 8,721 suka latsa alamar likes, mutane 1,130 sun sake raba labarin, da wasu 253 wadanda suka yi amfani da hoton wahen yin tsokaci ya zuwa ranar Litini sadda muka duba batun.

Hoton dauke da tsokaci makamancin na Twitter ya sake bulla a shafin Facebook. Wani Tunde Salam ne ya raba labarin da taken “Lobatan,” wanda ke nufin “an yi an gama” da harshen yorubanci saboda an hango ‘yan takarar na shan tabar ta hookah.

“‘Yar takarar mukamin mataimakiyar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar LP Princess Islamiyat Oyefusi,” sakon na Facebook ya bayyana. Lobatan!”

Binciken hoto a google ya kai mu ga wani labari a shafin Momedia da taken “ka da ku yi zabe kawai, ku yi bincike kafun nan – martanoni yayin da Kemi Olulonyo ta wallafa irin hotunan da ba safai ake gani ba na ‘yar takarar mataimakiyar gwamna a jam’iyyar LP na jihar Legas.” Labarin ya yi bayyana majiyarsa a matsayin labarin da aka gani a wani shafin Instagram na ‘yar jaridar nan mai rigima, Kemi Olulonyo tare da hoton da zargin. 

Wata mai amfani da shafin twitter Nkechi2Lagos (@NkechiofLagos2), wadda ta nuna ta yarda da Oyefusi ita ce ta karyata zargin ta ce ba ‘yar takarar ba ce a hoton wasu ne kawai ke neman su bata mata sun. Abun da ta kira “shirin da ba shi da mahimmanci.”

A nata martanin, mai amfani da shafin twitter Persian Queen (@teeana_world), ta yi tambaya game da sahihancin labarin. 

Ganin yadda labarin ya yadu ne da mahimmancin shi ga irin shawarar da masu zabe zasu yanke ne ya sa muka dauki nauyin tantance wannan labarin.

Tantancewa

Mene ne ko kuma daga ina wannan hoton ya yi mafari?

Duk da cewa DUBAWA ba ta iya gano mafarin hoton ba, ta gano cewa ba sabo ba ne tunda an taba amfani da shi a kafofin sadarwa na soshiyal mediya tare da bayanai daban-daban.

Daga zargin cewa wanda ke cikin hoton ‘yar takarar jam’iyyar Leba ce zuwa mai cewa “iyaye mata na zamani” masu amfani da shafukan yada zumuntan na amfani da hoton su yi sharhi kan batutuwan da suke fi ci musu tuwo a kwarya. Mai amfani da shafin Twitter da sunan H.O.D Vawulence Department for PO (@festiveplug), ya raba  hoton ranar 10 ga watan Maris da taken “Iyaye matan zamani nan  gaba.” 

Binciken mahimman kalmomin da muka yi ya kai mu shafin Facebook zuwa farko-farkon sadda aka yi amfani da hoton ranar 7 ga watan Maris  tare da wani tiren abinci, wanda Ojong Agbor ya wallafa yana kiran wadda ke cikin hoton Amaka.

Shin hoton na da alaka da Oyefusi?

Oyefusi ta mayar da martani dangane da hoton a shafinta na Twitter inda ta ce matar da ke cikin hoton ba ita ba ce kuma ta ce duk farfaganda ce.

Babban sakataren jam’iyyar LP a jihar Legas Sam Okpala a wata hira da ya yi ta wayar tarho da mai binciken DUBAWA, ya karyata zargin shi ma ya danganta shi da aikin masu hana ruwa gudu. “‘Yar takarar mukamin mataimakiyar gwamnanmu gimbiya ce wadda ae mutuntawa sosai a jihar Legas kuma ba ta shan taba,” ya bayyana

Mai amfani da shafin twitter (@festiveplug) wanda ya wallafa hoton ranar 10 ga watan Maris 2023, ya bayyana cewa ya san matar da ke cikin hoton kuma ba ‘yar takarar ba ce.

“Hoton ya fito daga wuri na ne, na san matar da ke shan tabar. Ban san yadda wani zai hada hoton matar da fuskar ‘yar takarar ya ce sun yi kama ba,” @festiveplug ya rubuta.

DUBAWA ta tuntube shi dan samun karin bayani da tantancewa. Ya sake jaddada cewa matar da ke cikin hoton ba ‘yar takarar LP Abiodun Oyefusi ba ce. Ya yi zargin cewa matar ‘yar Afirka ta Kudu ce. Sai dai ba zai iya ba mu sunarta ba.

Kwatanta Abiodun Oyefusi da matar da ke shan hookah

Baya ga bayyanar da hoton da ake zargi ya yi a shafukan soshiyal mediya da dama dauke da take iri-iri, da muka sa hoton da ainihin hoton ‘yar takarar LP a mahajar da ke tantance hotuna ta Forensically, manhajar ta bayyana mahimman banbance-banbance a fasalin fuskokinsu da wasu gabobin jiki.

Banbanci a bayan/gwawun yatsun hannu

Gabobin saman yatsun ‘yar takarar LP sun fi na matar da ke cikin hoton haske, bacin haka yatsun ‘yar takarar LP ba su kai na wadda ke hoton kauri ba.

Fasalin hanci

Da aka duba hancin kowacce, an gano cewa hancin Oyefusi ya fi na matar da ke cikin hoton tsawo. Hancin wadda ke cikin hoton kuma ya fi fadi kuma a manne yake ba shi da tsinin da na ‘yar takarar LP ke da shi.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa ‘yar takarar mukamin mataimakiyar gwamna a jam’iyyar LP, Abiodun Oyefusi, ba ita ce a hoton matar da ke shan tabar hookah ba. Dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »