Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Adekunle Gold ya kasance abokin buga kwallon Mbappe a tawaga guda.

Sakamakon bincike: KARYA NE. wasu bayanai da ke zama sanannu sun nunar da cewa Kylian Mbappen shekarunsa shida ne kacal lokacin da ya shiga makarantar koyon kwallon AS Bondy shi kuwa Adekunle Gold yana da shekaru 17 .
Kari a kan wannan, a hirar da gidan jaridar Punch yayi ya nunar da cewa Adekunle Gold bai taba bugawa makarantar kwallo ba koma ya zama kwararren dankwallo.
Cikakken Sako
Ba sabon labari ba ne yadda masu shiga shafukan sada zumunta kan shiga muhawara kan rayuwar wasu fitattun mutane da abubuwan da ya shafi rayuwar su.
Wani mai amfani da shafin Facebook Sunday Godpaid, ya rubuta a shafinsa cewa mawakin nan kuma mai rubuta waka Adekunle Kosoko (wanda a fannin kwarewarsa ake kira Adekunle Gold da AG Baby) tsohon abokin kwallo ne ga danwasan gaban Faransa kuma sananan dan wasan Paris Saint-Germain (PSG) Kylian Mbappe.
Ashe Adekunle Gold ya taba buga kwallo a tawaga guda da Mbappe? Alheri” abin da ya wallafa kenan.
Makale da wannan rubutu da ya wallafa hoto ne na Mbappe da abokan wasansa a rigar ‘yanwasa na Bondy wanda ke nuna tawagar ‘yankwallon makarantar. A dukkanin hotunan an kewaye danwasan gaban na Faransa da Adekunle Gold don a nuna cewa a kulob daya suke.
Ya zuwa ranar Talata 20 ga watan Nuwamba, 2023 wannan labari da aka wallafa a shafin Facebook ya samu nuna sha’awa (Likes) 108,000 da masu tsokaci (comments) 5.000 da wadanda suka yada (shares) sau 789.
Tsokaci da mutane ke yi kan wannan labari da aka wallafa sun banbanta. “Alheri a gare su duka” abin da Miller Sweetlife ya fada kenan (commented.)
“ Da Allah ka ce wani abun daban. Mun sani cewa wannan abin ba zai yiwu ba. Ka je ka huta ka ji” a cewar Eseoghene Gift (remarked.)
Duba da cece-kuce da wannan kalamai ko wallafa ta jawo ya sanya mu tashi haikan don tantancewa.
Tantancewa
Mun gano cewa asalin hoton an dauko shi ne daga shafin masu sai da littafai na Polaris Gramatnica.
A wannan shafi an yi amfani da hoton don a nunar da yadda dan kwallon na Faransa Mr. Mbappe ya cimma gagarumar nasara a matsayinsa na kwararre a fagen buga tamola.
Britannica, da ke zama rumbun ajiyar bayanai a intanet ya bayyana cewa an haifi Mista Mbappe a ranar 20 ga watan Disamba 1998 kuma ya nunar da cewa yana da shekaru shida ne kacal ya shiga makarantar koyon kwallon ta AS Bondy.
Idan aka kwatanta za a ga Adekunle ya girme shi da shekaru 11 wanda ya nuna cewa a lokacin da Mbappe ya shiga AS Bondy a shekaru shida Adekunle na da shekaru 17 da haihuwa.
Idan kuma aka kalli hoton da ya nuna yaron da aka bayyana a matsayin mawakin na Afro bai kama da namiji dan shekaru 17 ba.
Idan kuma aka duba tattaunawar da Punch ta yi da shi don jin sha’awarsa da wasanni Adekunle Gold ya bayyana cewa yana da sha’awar kwallon kafa da Tennis, har ila yau ya kuma ce duk da yana da jiki da zai iya kwallon kafa yayi amanna cewa abin da zai yi a rayuwarsa shine kida da waka.
Ko da dai mawakin ya tuna da yadda yake sha’awa da son ‘yanwasan Super Eagles a wasan kwallon duniya a 1994 da 1998 bai taba nuna cewa yayi wasa a tawagar ‘yankwallo ba ta makaranta.
Ko da yake mun tuntubi Adekunle Gold kan wannan da’awa har yanzu bai ce komai ba game da tambayar da aka yi masa.
Kammalawa
Da’awar da aka yi kan wannan labari karya ce. Majiyoyi da dama sun tabbatar, haka nan kafafan jaridu a tattaunawa da mawakin na Afro beat bai taba nuna kansa a matsayin dan wasan makaranta ba ko wanda suka yi wasa da Mbappe.