African LanguagesHausa

Opay, Palmpay, Piggyvest, ba sa cikin hanyoyin hada-hadar kudaden da za’a dakatar

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Opay da Piggyvest da Palmpay na daga cikin hanyoyin hada-hadar kudade da za su daina aiki.

Opay, Palmpay, Piggyvest, ba sa cikin hanyoyin hada-hadar kudaden da za'a dakatar

Sakamakon bincike: Karya ce! Kamar yadda takardar da aka raba wa bankuna ta nunar. Wadannan bankuna Piggyvest da Opay basa daga cikin kafofin hada-hadar kudaden bankuna 32 da aka bayyana. Piggyvest da Opay sun fitar da takardar manema labarai inda suka nesanta kansu da wannan labari cewa suna cikin wadanda za a dakatar.

Cikakken sakon

Bankuna a Najeriya sun sami takardar sanarwa daga kamfanin da ke lura da harkokin bankuna na Interbank Settlement System Plc (NIBSS) cewa za a cire bankunan da ba a zuwa don ajiye kudade kamar masu hada-hada kawai ta internet da masu ba da basuka da wasu dillalai na musamman daga tsarinsu na hada-hadar kudade na NIP.

Wadannan hanyoyin hada-hada na NIP sun hadar da tsarin nan na USSD da ke amfani da lambobi don hada-hadar kudade da manhajar bankuna a wayoyin salula da tsarin hada-hadar kudade na PoS da na’urar ATM da ma wasu kafofi na yanar gizo.

Wannan shiri dai na so ne ya kawar da duk wasu tsare-tsaren hada-hadar kudade da ci gaban fasahar zamani ya kawo wadanda basu da lasisi na hada-hadar kudade a bankuna.

Wadannan kafofi da za a dakatar ana sa rai su jagoranci fitar da kudade zuwa bankuna ne amma ba tare da suna iya shigo da kudade ba.

Wannan ci gaba da aka samu dai ya haifar da muhawara mai zafi a shafukan sada zumunta cewa mai zai sa kamfanin na NIBSS ya dauki wannan mataki?

Mai amfani da shafin Twitter (X) Molaramills ta yada (shared) a shafinta cewa “Opay, Palmpay da dangoginsu za a dakatar da hada-hadar da suke yi” ta kara cewa “Gwamnatin Najeriya ta iya surutai da kara sanya al’umma a cikin matsi.”

“Opay da Kuda da PiggyVest da sauransu sun fuskanci tarin kalubale fiye da sauran bankunan kasuwanci na kasar a fafutkarsu ga ‘yan Najeriya, musamman a lokacin da al’umma suka shiga kanfar kudade. Yanzu sune matsalar su. Basa jin dadi yayin da al’umma ke zaune cikin walwala da abubuwan da suke yi.”

Wannan bayani da aka wallafa ya samu martani da dama; Frederick Eze  ya ce labarin karya ne, “Basa cikin wadanda za a dakatar. Ki je ki tantance bayananki da fari kafin ki wallafa. ”

Ore-ofe da ya amince da labarin ya rubuta cewa, “sun kware dama wajen sanya rayuwar talakawa cikin kunci. “

An samu irin wadannan labarai masu da’awa irin wannan a shafukan Facebook, tech blogs da sauran shafuka na X.

Bayan wallafa wannan labari ya samu masu kallo (views) 14,000 da masu nuna sha’awa 34 da masu sake wallafawa (reposts) 21 tun bayan da aka wallafa wannan labari a ranar 7 da watan Disamba.

To duba da irin yadda wannan labari ya haifar da cece-kuce ya sanya mu gudanar da bincike don gano sahihancinsa.

Tantancewa

DUBAWA ya nazarci sanarwar da NIBSS ta fitar tare da jerin sunayen bankunan da abin ya shafa. Cikin sunayen bankunan 32 bamu gano wadanda aka bayyana a sama ba.

Moniepoint da Kuda da PiggyVest da Opay da Paga da Palmpay basa cikin jerin sunayen, an dai zayyano sunayen kamfanonin da ba su da lasisin ajiya.

A shafinsu na X Twitter kamfanin Opay ya rubuta cewa “Muna farin cikin bayyana maku cewa bankin Opay baya cikin jerin sunayen da kamfanin NIBSS ya wallafa.”Manufar ta karkata ne ga masu warware bukatun samar da kudade  da masu hada-hadar ta intanet kawai da wasu dillalai na musamman. Opay shi ya kasance mai samar da kudade ne tafi da gidanka (Mobile Money Operator (MMO)) wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya ba shi lasisi kuma yana da inshora ta hukumar NDIC.

“Muna da tabbacin kudadenku babu abin da zai same su idan  kuna tare da Opay.”

Mun kuma gudanar da bincike kan  Piggyvest wanda suma sun rubuta sanarwar nesanta kansu (disclaimer): “Da Allah a yi watsi da wasu bayanai marasa tushe. Duk masu lambar asusu da Piggyvest na da lasisi daga abokan huldar mu, kuma basa cikin wadancan sunaye da aka lissafa. Kudadenku babu abin da zai same su.” Abin da suka rubuta kenan.

A cikin takardar sanarwar ta nunar da cewa hukumar ta NIBSS ta yi bayani ga kamfanonin hada-hadar (Switches, PSSPs, da SAs) cewa suna iya fitar da kudi zuwa 

banki amma ba su da damar karba kasancewar lasisinsu  bai ba su damar su rike kudaden masu ajiya ba.

Wannan tsari dai na da aniya ce ta cire masu hada-hadar ta intanet kawai ba tare da lasisi ba, karkashin sabuwar yarjejeniyar suna iya amfani da kafar su ne su isar da kudade zuwa bankuna ba wai su rika karbar kudade ba.

Wannan sanarwa ba ta shafi Opay da Palmpay da Piggyvest ba. 

A Karshe

Opay da Piggyvest da Palmpay basa cikin kamfanonin da aka lissafa a jerin sunayen da NIBSS ta fitar. Wannan tsari da aka fitar zai kawar da masu harkokin da ba su da lasisi na hada-hadar musayar kudade.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button