African LanguagesHausa

Rahotannin cewa bayan mutuwar auren Achraf Hakimi da mai dakinsa Hiba Abouk ta bukaci rabin kaddarorin shi amma komai na cikin sunan mahaifiyarsa karya ne

Zargi: Rahotanni da dama a shafukan soshiyal media da ma wasu kafofin yada labarai na zargin wai matar tauraron kungiyar kwallon kafar PSG Achraf Hakimi ta bukaci a ba ta fiye da rabin kaddarorin shi a matsayin wani bangare na dukiyar da ya kamata ta samu bayan sun rabu, sai dai a maimakon hakan sai ta gano cewa yawancin dukiyar da ya mallaka a sunar mahaifiyarsa su ke

<strong>Rahotannin cewa bayan mutuwar auren Achraf Hakimi da mai dakinsa Hiba Abouk ta bukaci rabin kaddarorin shi amma komai na cikin sunan mahaifiyarsa karya ne</strong>

Sakamakon Bincike: Karya! Kwakwarar binciken da DUBAWA ta yi ya nuna mata cewa batun ya fara bulla daga wani shafin bogi ne kafin mutane suka dauka suka fara yadawa.

Cikakken bayani

Kafofin sadarwa na soshiyal mediya a ciki har da Facebook na cike labaran da ke zargin wai Hiba Abouk, matar tauraron kwallan kafar nan na kungiyar PSG wato Achraf Hakimi ta nemi saki daga wurin mijin kuma ta bukaci ta a ba ta rabin kadarorinsa.

Labarin ya kuma kara da zargin cewa lokacin da ake kokarin tabbatar da sakin ya bayyana cewa Hakimi ya sa kusan duka kadarorinsa a sunan mahaifiyarsa ne kuma kashi 80 cikin 100 na euro miliyan daya na albashin da ya ke samu kowani wata daga PSG duk asusun mahaifiyar ya ke zuwa. 

Ga takaitaccen bayanin da aka wallafa a shafin Facebook:

“Matar dan wasan kwallon kafa Achraf Hakimi ta nemi saki daga wurin shi kuma ta bukaci da a bata fiye da rabin kadarorin da ya mallaka da ma dai wani kaso na arzikin dan kwallon kafar mai asalin Maroko. Yana daya daga cikin ‘yan wasan masu mafi yawan albashi a Ligue 1 inda ya ke samun fiye da miliyan daya  na euro kowani wata. Dan haka da tsohuwar matar ta taki sa’a amma sai suka gano cewa Ashraf Hakimi ba shi da kadarori bare ma kudi a banki

Achraf Hakimi ya sa duk wani abun da ya mallaka a sunar mahaifiyarsa tun da dadewa,” labaran wanda aka fassara daga harshen Faransanci ya bayyana. 

Wannan labarin ya shiga kusan ko’ina kuma ya ma kasance babban labari a shafukan labarai na kasa da kasa kamar wannan, wannan da wannan.

Kafofin yada labaran intanet a Ghana ma ba’a bar su a baya ba wajen kawo labarin na Hakimi mai kayatarwa kamar yadda muka gani a nan da nan.

Bacin irin yaduwan da labarin ya yi, akwai abubuwan da suka sa mu shakkan sahihanci wannan labarin wadanda suka ja hankalinmu muka ga cewa ya kamata DUBAWA ta tantance gaskiyar lamarin.

Na farko dai, manyan kafofin yada labarin duniya masu nagarta ba su dauki labarin ba, duk kuwa da yadda labarin ya shiga ko’ina. Rahoton da muka gani dangane da Hakimi shi ne wanda ya ce ana gudanar da bincike kan tauraron kwallon kafar bisa zarginsa da aikata fyade.

Jaridar Marca ce kadai ta yi rahoton amma kuma ita kanta majiyar da ta yi amfani da ita ta kara sanya alamar tambaya ne dangane da sahihancin labarin na ta. 

To daga ina aka fara jin wannan labarin? 

Ta yin amfani da manhajar da masu tattarawa da wallafa labarai ke amfani da ita wajen tantance mafari da sahihancin labarai, DUBAWA ta duba duk wuraren da aka yi amfani da sunan ‘Achraf Hakimi’ daga ranar 7 zuwa 14 ga watan Afrilun 2023, kuma labarin da ya fi dadewa labari ne wanda aka danganta da wani wshafi mai suna Papa Ado.

Shafin  ya wallafa labari daga misalin karfe 8:08 na yamma ranar 13 ga watan Afrilu, 2023, inda ya zuwa yanzu ya sami martanoni fiye da 76, 000.

Shafin Facebook da ke tabbatar da gudanar da abubuwa a bayyane ya nuna cewa daga kasar Ivory Coast ake kula da shafin kuma yana da mabiya kusan 450,000. Sai dai a gurbin kwatancen abun da shafin ke yi, masu shafin sun bayyana kansu a matsayin masu labaran barkwanci na shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara kuma babban abun da suke yi a shafin shi ne “barkwanci da sa mutane dariya.”

Sakamakon da muka samu daga binciken Crowdtangle ya nuna cewa shafukan Facebook da dama sun dauki labarin na shafin Papa Ado mintoci kadan bayan da suka wallafa labarin.

Yawancin shafukan da suka fara yada labarin daga Ivory Coast ne. Bayanan da muka samu daga Crowdtangle sun kuma nuna mana cewa wadansu shafukan da ake kula da su daga kasashen Ghana, Najeriya, Uganda, Afirka ta Kudu, Kenya da kasashen Afirka da dama hatta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya duk sun yi amfani da labarin har ma sun da gishiri dan sun kara wa labarin armashi.

Da muka yi amfani da shafin binciken Twitter, mun gano ainihin shafin da ya yi mafarin labarin wani shafi mai suna First Mag Le Vrai – wanda ya wallafa labarain a twitter da misalin karfe  9:12 na yamma ranar 13 ga watan Afrilu – misalin sa’a guda bayan da shafin Papa Ado ya wallafa labarin a Facebok.

Labarin ya kai ga mutane miliyan tara yayin da wadansu 100,000 suka yi tsokaci a kai. Shi ma wannan shafin na da dangantaka da shafin Papa Ado.

Binciken da muka yi na gano duk labaran da aka wallafa a twitter da sunan ‘Achraf Hakimi’ cikin kwanaki bakwai a shafin twitter sadda abun ya faru duk sun nuna shafin First Mag a matsayin mafarin labarin a soshiyal mediya.

Gano gaskiya

Ranar 15 ga watan Afrilu DUBAWA ta tuntubi shafin Papa Ado a Facebook dan samun karin bayani daga wajensu dangane da ingancin majiyoyin da suka yi amfani da su amma ba mu sami amsa ba.

Rabuwar Achraf Hakimi da mai dakinsa

Matar dan kwallon kafar Hiba Abouk mai shekaru 36 wadda ya ke da yara biyu tare da ita, ta sanar a watan da ya gabata (watan Maris 2023) ta sanar cewa ta rabu da tauraron kwallon kafar na wani tsawon lokaci yanzu kuma tana jira ne kawai a kammala sakin.

Ta ce rabuwar ta su ta zo tun ma kafin ofishin masu shigar da kara a Nanterre su bayyana cewa ana binciken dan kwallon bisa zarginsa da yi wa wata ‘yar shekaru 24 na haihuwa fyade.

“Gaskiyar ita ce, na wani tsawon lokaci yanzu, bayan da muka tattauna muka kuma yi tunani mai zurfi, da ni da mahaifin yara na muka yanke shawarar kashe aurenmu, tun ma kafin abubuwan da ake gani a kafofin yada labarai dangane da ni yanzu su bulla,  duk wadannan daga waje ne,” ta bayyana.

Lauyar Achraf Hakimi, Fanny Colin, ta fadawa wata jaridar Faransa L’Équipe cewa Hakimi ya karyata zargin.

Dokokin Faransa

Bisa tanadin dokokin ma’aikatan kasashen ketare, da wata tawaga ta musamman ta lauyoyin kasa da kasa wadanda ke kula da lamuran da suka shafi saki da iyalai, matsayin dokar Faransa inda namiji da na mace ba su riga sun shiga yarjejeniyar aure ba “duk wata dukiya da suka samu a lokacin da ake zaman auren, tilas ne su raba shi dai-dai sadda auren ya mutu.” Sai dai duk abun da aka mallaka kafin auren zai  specialist team of international divorce and family lawyers, the default position of French law where a couple has not entered into a prenuptial agreement or a specific matrimonial regime, 

“the assets the parties acquired during the marriage will be split equally on divorce. However, anything acquired before the marriage will remain with the owner.”

In this case, the couple has a ‘contrat de mariage’ (prenuptial agreement) that is followed. 

Dokoin kasar Spain

Haka nan kuma, dokokin kasar Spain (wanda ake kira código civil) su ma sun amince da a raba duk dukiyar da aka saya bayan an daura aure dai dai wa daida tsakanin miji da mata, bisa bayanan BCN-advisors.

“Idan har código civil ya shafi shari’ar saki, ana sa ran kowane daga cikin ma’auratan zai rike kashi 50 na ‘yancin mallakar dukiyoyin da suka samu sadda suka yi aure. Sai dai idan har an mallaki dukiyar kafin a yi aure ne ba za’a iya rabawa  daidai har da wanna ba. Haka nan kuma har da kudaden da aka biya (misali kudin gado) kayayyakin da aka yi amfani da su wajen sana’a, da rigunan sa wa da kayayyakin wajen aiki wadanda ba wata darajar a zo a gani suke da shi ba.”

Da bayanan da aka yi a sama, zai yi wahala wa duk wani lauyan da ya lakanci dokokin Spain – inda ma’auratan suka yi wayo, ko kuma na Faransa – inda Achraf Hakimi ke zama, ya bukaci kashi 80 cikin 100 na dukiyar dan kwallon wa matarsa Hiba Abouk.

Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance dangane da shari’ar dan kwallon da matarsa wanda ma ake zargin ya janyo magana a kan wannan zunzuruntun kudin da ake cewa matar ta bukaci a ba ta.

Sakon email da na twitter zuwa ga lauyar Achraf, Fanny Colin, ya nuna cewa ya tafi kuma  ta samu amma ba ta ba mu amsa ba. 

Ma’ana

Yadda wannan labarin ya bazu a ko’ina ya janyo martanoni da kalaman da suka rika nuna kaskanci ga Hiba Abouk da ma mata baki daya. Ya kuma kara bai wa maza magidanta masu aure karfin gwiwar yin abubuwa makamantan wannan ga na su matan.

Yawanci sun rika amfani da kalaman batanci suna kwatanta Hiba Abouk, kalamai irin su “kwadayayya” ko kuma “gold digger” a turance kamar yadda muka gani a labarai kamar wannan da wannan.  

A karshe, daga binciken da DUBAWA ta yi ba mu ga wata hujjar da ke goyon bayan cewa Hakimi ya yi rajistan duk dukiyar da ya mallaka a cikin sunar mahaifiyarsa dan hana matarsa daga mallakar rabinsu bayin aurensu ya mutu ba. Shafin Facebook din da ya kasance mafarin labarin shafi ne na barkwanci ba na batutuwan gaskiya ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button