African LanguagesHausa

Shin da gaske ne Putin yace Najeriya ta yi watsi da taimakon da Rasha ta so ba wa kasar a 1980?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani shafin Facebook Afrocania yayi da’awar cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin yace Najeriya ta yi watsi da tayin da Tarayyar Sobiyat ta yi mata na tallafa wa kasar waajen samar da hasken lantarki a shekarun 1980.

Shin da gaske ne Putin yace Najeriya ta yi watsi da taimakon da Rasha ta so ba wa kasar a 1980?

    Hukunci: KARYA CE, babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto kan wannan da’awa. Nazarin da DUBAWA ya yi ma ya nunar da cewa akwai yiwuwar wannan jawabi ma an samo shine ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira ta (AI). 

    Cikakken Sako

    Wani shafin Facebook, Afrocania, ya wallafa cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ba da bayanai cikakku kan yadda Najeriya ta ki karbar taimako daga kasar Rasha kan batun sama wa kasar wutar lantarki daga Tarayyar Sobiyat. 

    A cewar da’awar Putin yace Rasha ta tallafa wa Najeriya wajen gina kamfanin karafa na Ajaokuta a shekarar 1980 a kokari na inganta hulda tsakanin kasashen biyu, anan abin da ake fadi Rasha ta so samun damar amfana da juna tsakaninta da Najeriya a lokacin da take ganiyar hada-hadar albatrkatun man ta.

    Sai dai kuma ya zargi kasashen yamma wajen cusa kai a aikin, kuma har yanzu Najeriya ke ci gaba da asara, “Kasashen Yamma sun yi kutse kamar yadda suka saba, hakan ya jaza wa Najeriya aka bar aikin na Ajaokuta ba kulawa don ya lalace. Najeriya na ci gaba da fafutuka don gano makomarta a aikin, har zuwa yau kan wannan aiki da a yanzu ya sanya Najeriya a gaba a wajen aikin da ya shafi samar da karafa a duniya,” kamar yadda jawabin ya nunar.

    Ya zuwa ranar 1 ga Oktoba,2025 wannan wallafa (post) ta samu martani 20.000 mutane 3,700 sun yi tsokaci da wasu 5000 da suka sake yadawa. Da yawa cikin wadanda suka yi tsokacin  DUBAWA ya lura cewa suna nuna goyon baya ne ga da’awar.

    Muhammed Bah ya yaba wa Putin wanda ya bayyana a matsayin shugaban da ke wa Afurka fatan alkhairi. “Haduwarsa da duk wata kasa, magana ce ta cin riba kan riba. Kalli Mali da Burkina Faso suna ci gaba,’’ abin da ya rubuta kenan. 

    Wani mai amfani da shafin na Facebook, Olumide Matthew, yace,”Fada ne tsakanin Rasha da Burtaniya, Rasha ta yi nata kokarin amma shugabanninmu a wancan lokaci suka tsara su bi Birtaniya a matsayin kasar da ta yi masu mulkin mallaka, don suna kallon Rasha a matsayin ‘yar leken asiri.” 

    Isaiah Akpan yace, “Mun sani cewa Rasha ita ce mabudin ba wai Faransa ko China ko Amurka ba.”

    Ganin yadda wannan jawabi ka iya shafar harkokin kasar da manufofinta na kasashen ketare shirin DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan da’awar.

    Tantancewa

    DUBAWA ya tura tambaya ga Afrocania kan da’awar da yayi a shafin na Facebook, ya zuwa ranar 2 ga watan Oktoba,2025 tambayar da DUBAWA ta tura masa babu amsa duk da cewa alamu na ya karanta sun bayyana.

    Da muka yi amfani da wasu muhimman kalmomi don lalubo asalin da’awar babu abin da aka samu, haka nan babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta buga wannan labari , wannan ya sanya babbar alamar tambaya ta farko kan da’awar, ya kamata a ce wannan jawabi an ganshi a kafafan yada labarai na kasa da kasa ganin muhimmanci da yake da shi a ce shugaba irin Putin ya furta. Da kuma ya kamata a ce ga a wajen taron da ya furta wannan da’awa. 

    Mun kuma duba shafin fadar ta (Kremlin website), wacce ke wallafa bayanai ko makaloli (transcripts)  na shugaban da tattaunawarsa. Mun duba shafin ta hanayar amfani da wasu muhimman kalmomi daga wancan bayani, amma babu wani bayani  da ya nuna cewa Putin ya furta wadannan kalamai.

    DUBAWA ta tabbatar da cewa Tarayyar Sobiyat ta ba da tallafi na kwararru da na kudi a lokacin aikin na (Ajaokuta Steel) a shekarun 1970 lokacin  da Najeriya ke fafutukarta a harkokin samar da masana’antu.Kamfanin kasar Rasha TPE (Tyazhpromexport) ya shiga harkar dumu-dumu (heavily involved) a lokacin tsara ginin da aiwatar da shi..

    A tarihance bayanai sun nunar da cewa wannan aiki an yi watsi da shi musamman (primarily due) saboda dalili na cin hanci da rashawa da rashin iya kula da harkokin mulki da rashin sanya kudade daga bangaren gwamnatoci da suka rika biyo baya. Matsalar da ta sanya aikin ya tsaya na da alaka kai tsaye da harkokin cikin gida ba wai na kasashen ketare ba.

    Muhammadu Buhari da Putin sun rattaba hannu kan yarjrejeniyar fahimtar juna  (MOU) don dawowa kan aikin kamfanin karafan, wannan ya tabbata da nuna ci gaba da samun fahimta (ongoing cooperation) amma wannan baya tabbatar da waccan magana da aka alakanta da fadin da aka ce na Putin ne. 

    Har ila yau babu wata sheda da ta nuna bayanan Putin a tarukan koli tsakanin Rasha da Afurka 2019 da 2023  da ta nuna yayi kalamai na nuna kyamar kasashen yamma bare ma batun zarginsu kan harkoki da suka shafi gudanarwar kamfanoni.

    DUBAWA ta yi amfani da wasu kayan aiki don gano ko wadannan jawabai an yi amfani da kirkirarriyar basira (AI) wajen samar da su, sakamakon ya nunar akwai yiwuwar cewa kalaman na AI ne da kaso 67% kamar yadda Undetectable AI ya nunar, haka nan  Scribbr da kaso 57%  yayin da Grammarly ya nunar da kaso 100%. 

    A Karshe

    Da’awar cewa Vladimir Putin na zargin kasashen Yamma da tsoma baki kan harkokin samar da ababen more rayuwa a Najeriya da Rasha ke yi a yarjejeniya da ke tsakanin kasashen, babu wata sheda da ta nunar da haka, babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta wallafa labarin, kuma bincike da nazari na DUBAWA sun nunar da cewa akwai alamu masu karfi da suka nuna cewa an yi amfani da AI wajen fitar da jawabin.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button
    Translate »