African LanguagesHausa

Shin farantin Solar da ke kan Murg Plaza ne ya yi sanadin gobarar da ta ci ginin kamar yadda wani mai amfani da shafin X ke da’awa? 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin soshiyal mediya na zargi wai gobarar da ta barke a Murg Plaza da ke Area 10 a Abuja, ya yi mafari ne saboda  — da aka sanya a kan rufin

Shin farantin Solar da ke kan Murg Plaza ne ya yi sanadin gobarar da ta ci ginin kamar yadda wani mai amfani da shafin X ke da’awa? 

Hukunci: Karya ce! Har yanzu ba’a kai ga sanin abun da ya yi sanadin gobarar ba. Amma an gano cewa Solar din da aka hada akan rufin ginin ba shi da wata alaka da gobarar.

Cikakken bayani

A duniya baki daya yanzu, ana fama da gibi wajen samun wutar lantarki,  kuma da wannan da matsalar sauyin yanayi a hade suna sa al’ummomin kasa da kasa neman sabbin hanyoyin samar da makamashi wadanda suka banbanta daga hanyoyin gargajiyar da aka saba.

Daya daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da shi da yanzu shi ne hasken rana ko kuma sola kamar yadda ake kira da turanci, a matsayin irin makamashin da ake sabuntawa wanda kuma ake samu ta hanyar dora farantan da ke jan hasken ranar su mayar da shi makamashi a saman gidaje da dai sauran gine-gine. A shekaru 11 da suka gabata, makamashin da ake samu daga haken rana ya karu da kashi 146 cikin 100. Wannan habbakar da aka samu ya nuna yadda ya sami karbuwa da kuma yiwuwar bunkasar shirye-shirye masu amfani da makamashin da ake samu daga hasken rana a kasar.

Did solar panels cause the fire outbreak at Murg Plaza, as posited by an X user?

Sakamakon wannan karuwar da aka samu wajen amfani da hasken ranar a Najerita, yanzu ba sabon abu ba ne a ga irin farantan solar a saman gine-gine.

A watan Afrilun 2024, wani mai amfani da shafin X ya wallafa wani bidiyon da ya nuna yadda wuta ke cin wani kanti da ke Area 10 a Abuja. Bidiyon ya gwado yadda wutar ta lakume farantan solar da aka sa a saman ginin; sa’annan watakila hakan ne ya sa mawallafin ya kara da cewa wadannan faratan ne suka yi sanadin gobarar da ta kama ginin. Did solar panels cause the fire outbreak at Murg Plaza, as posited by an X user?

Hoton ginin da gobara ta kama a  Murg Plaza, Area 10. Abuja

Taken da aka yi wa labarin na cewa, “Duk ma da farantan solar, ginin ka zai cigaba da kasancewa cikin hadari, idan kun yarda ku yi hattara ku kuma kula.”

Yayin da yawancin wadanda suka yi tsokaci suka rika nuna damuwa da tausayi wa wadanda suka rasa shagunansu a gobarar, akwai kuma wadanda suka rika tambayoyi suna shakkun da’awar da aka yi ko kuma ma dai danganta gobarar da farantan solar da ke kan ginin.

Ga kadan daga cikin wadanann sakonnin:

Wani mai amfani da shafin @tamizoo ya ce “Ke nan Solar na iya janyo gobara?”

Wani kuma, @designemir7, ya rubuta, “lallai! Na dauka Solar ya banbanta daga lantarki.”

A lokacin da muka hada wannan labarin, mutane sun sake rabawa sau 250, akwai tsokaci 119, alamar like 539 sa’annan wasu 118 sun adana shi a bookmark.

Baya ga wannan mai amfani da shafin na X, wasu mutane da dama su ma sun  yi tsokaci dangane da abun a shafukan soshiyal mediya kamar yadda za’a iya gani a nan da nan.

Yadda wannan batun ya yi yawo da ma yadda aka gaza fayyace shi yadda ya kamata ua sa muka ga kaman zai iya janyo rashin fahimta da rikici wa wadanda ke da ra’ayin habaka amfani da solar. Wannan ne ya sa DUBAWA tantacen gaskiyar da’awar da aka yi tare da hoton bidiyon.

Tantancewa

DUBAWA ta kai ziyara zuwa wurin da gobarar ta kama a ginin na Murg Plaza, da ke Area 10, Abuja, dan tabbatar da abin da ya yi mafarin wutar, mu san ko ya na da dangantaka da farantin solar da ke kan ginin kamar yadda aka bayyana cikin bidiyon.

A wata hirar da aka yi da daya daga cikin wadanda gobarar ta shafi shagunansu, sun bayyana mana cewa ba’a riga an san taka mai-mai abun da ya yi sanadin gobarar ba.

Mutumin, Mr Victor ya ce, “Shagon da gobarar ta yi mafari na kulle a lokacin da wutar ta kama dan haka ba wanda zai iya cewa ga abun da ya yi sanadin wutar.”

Haka nan kuma, Mr Victor ya bayyana cewa shagon da ake magana a kai ma ba ya amfani da solar. Dan haka ba za’a iya danganta gobarar da farantin solar ba. Ya ce wannan bayanin da ake dangantawa da bidiyon ba gaskiya ba ne kuma bai bayyana ainihin abun da ya faru ba.

Wani wanda ya gani da ido, Ogaji Simon a cikin wata hirar da ya yi da gidan talibijin na  Galaxy TV News ya ce gobarar ta yi mafari ne bayan da wata na’urar air condition ta fashe.

Ya ce, “wasu wayoyi ne a cikin air conditioner suka yi karo da juna, wanda ya yi sanadin fashewar.”

Wannan bayanin ya sabawa da’awar da aka yi na cewa farantin solar da ke saman ginin ne ya haddasa gobarar.

Shin farantin solar na iya janyo gobara kamar yadda aka bayyana?

Bisa bayanan wani kundin da ke fayyace batutuwa a yanar gizo, farantin sola na dauke ne da wasu karafan da aka sanyawa abubuwa masu daukar ido kamar madubi wadanda suke iya daukar hasken ranar su mayar da shi makamashi.

Da ma dai makamashi irin wanda ake sabuntawa kamar hasken rana, tsabtataccen hanyar samun makamashi ne wanda ba shi da lahani. Ya kan taimka wajen yaki da hayakin masana’antu, ta yadda zai bayar da gudunmawa wajen rage dumamar yanayi. Farantin solar ba ya gurbata yanayi, komai na da tsabta.

Bincike na nuna cewa farantan solar na iya janyo gobara amma ba mai yawa irin wanda har zai kona gini ba.

Bugu da kari, idan har an sami hadarin gobara, ba mamaki ba a hada shi da kyau yadda ya kamata ba ne, domin idan an hada da kyau, babu abun da zai faru.

Haka nan kuma wani kundin kasa da kasa wanda ke dauke da bayanai kan makamashin hasken rana shi ma ya tabbatar da cewa ana iya samun gobara daga sola ne idan har ba’a hada shi da kyau yadda ya kamata ba. Sa’anan kuma gobarar na iya faruwa idan har ya yi zafi sosai, ko kuma aka sami miskila wajen hada wayoyi, ko kuma ba’a kula da shi da kyau ana mi shi sabis a lokutan da ya kamata, ko kuma ya yi karo da walkiya.

Wani labari da masu yaki da gobara suka rubuta, shi ma ya jaddada hadarin da ke tattare da kama wutar farantin sola ba shi da yawa, sai dai ba wai ba su kama wuta ba ne baki daya, kamar dai sauran fasahohin da ke samar da wutar lantarki, suna iya kamawa da wuta.

Bisa la’akari da wadannan bayanan da muka samu, farantin sola a saman ginin Murg Plaza ba shi da alaka da gobarar da ta kama ginin.

A Karshe

Bisa bayanan shaidun gani da ido, ba’a riga an tantance abun da ya yi mafarin gobarar da ta kama a Murg Plaza da ke Area 10 a Abuja ba. Dan haka batun cewa farantin solar da ke kan ginin ne ya yi sanadin gobarar ba gaskiya ba ne.

Wannan bincike an yi shine a shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024   karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Dataphyte, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »