Shin gaskiya ne mahara sun bukaci mazaunan Kebbe a jihar Sokoto su ba su gudunmawar tilas na naira miliyan 40?

Map of Sokoto State. Photo source: The Tribune Nigeria News.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Bakatsine a shafinsa na X ya ce mahara sun bukaci mazaunan garin Kebbe dake jihar Sokoto su biya su harajin naira miliyan 40 ko su kashe kowa da kowa tare da kona garin idan har ba a biya kudaden ba.

Shin gaskiya ne mahara sun bukaci mazaunan Kebbe a jihar Sokoto su ba su gudunmawar tilas na naira miliyan 40?

Hukunci: Gaskiya ne. Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar cewa mahara sun bukaci harajin naira miliyan 40 daga hannun mazaunan Kebbe sannan fannin rundunar dake yaki da garkuwa da mutane za ta dauki mataki a kai.

Cikakken Bayani

A ranar Laraba 2 ga Satumba 2026 Bakatsine a shafinsa na X (@DanKatsina50) ya wallafa da’awar cewa mahara sun bai wa mazaunan Kebbe dake karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto wa’adin kwanaki ko su kawo musu hari idan har basu biya harajin naira miliyan 40.

A rubutun da ya yi ya nun ace “Labari da dumin sa: Jiya da rana mahara sun bukaci a biya harajin naira miliyan 40 a Kebbe dake karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto kuma maharan na barazanar kashe kowa da kowa a kauyen idan har ba a biya harajin ba. Majiya da dama a jihar sun shaida cewa maharani sun yi waya ne ta wayar hannun wani manomi zuwa ga hakimin Kebbe inda da farko suka kai wa kauyen kwanaki biyar su hada kudaden amma bayan an roke su maharan suka bada kwanaki bakwai (Talata mai zuwa).

Bakatsine ya ne maharani sun yi gargadin cewa wayar da za su kira ya zammana cikin caji yadda a duk lokacin da suka kira za su iya samun mutanen garin domin tantance maganar biyan harajin.

Zuwa ranar 3 ga Satumba 2026 mutum 39,600 sun duba da’awa, 87 sun sake wallafawa da 22 sun mai da martani.

Skyler Sympson a shafin s ana X ya rubuta cewa “Sannan mutanen dake wahala a dalilin wadannan mahara za su zabi Tinubu da jam’iyyar APC wadanda suka kasa ceto su daga hannun mahara.

Joseph Isibor  ya ce “Babu dattijon kriki a Arewa. Duk sun sama ragwaye sun bari yara kanana ‘yan ta’adda sun kama su wadanda da farko suke mara wa baya.

Da yake nuna takaicin sa YarimaAhmed ya ce “Wannan abu na faruwa kamar a was an kwaikwayo. Allah ya kawo mana sauki.

Tantancewa

DUBAWA Ta gana da rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto game da rahotan inda jami’in hulda da jama’a na rundunar PPRO DSP Ahmed Rufa’I ya tabbatar cewa jami’an tsaro sun samu rahoto kan harajin da mahara suka saka sannan har sun aika da jami’an su doimin samar da tsaro.

“Muna da masaniya gane da wannan lamari sannan jami’an mu dake fannin yaki da garkuwa da mutane sun dauki mataki. Inji Rufa’i.

Kakakin rundunar bayan ya tabbatar da harajin naira miliyan 40 ya bada kwanakin wa’adin da maharani suka bada daban da wanda Bakatsina ya fada inda kakakin ke cewa maharani sun ce a hada kudaden harajin zuwa ranar Lahadi.

Kebe karamar hukuma ce a jihar Sokoro dake yawan fama da hare-haren mahara musamman kashe rayukan mutane da jami’an tsaro.

A Karshe

Da’awar cewa mahara sun bukaci harajin naira miliyan 40 daga hannun mazaunan Kebbe a jihar Sokoto da kuma basu wa’adi su hada kudaden gaskiya ne. Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da haka.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union)