Nan da shekara guda, shugaba Muhammadu Buhari zai ajiye madafun ikon Najeriya bayan da ya shafe shekaru takwas yana jan ragamar mulkin kasar, hasali ma tuni aka fara dambarwar neman wanda zai maye gurbinsa a zabukan masu zuwa na shekrar 2023.
A inuwar jam’iyyar shugaban kasar ta APC Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana yekininsa ga ‘yan Najeriya a matsayin daya daga cikin wadanda ke hankoran kasancewa a kujerar shugabancin kasar.
A wata hirrar da ya yi kwanan nan da jaridar Daily Trust, Tinubu ya yi zargin cewa lokacin da ya ke gwamnan jihar Legas, ko daya bai sami wani kasafin kudi daga Federal Account Allocation Committee (FAAC), wato kwamitin da ke kula da yadda ake kasafin kudin asusun tarayya ba.
Ya kuma kara da cewa bacin haka jihar Legas ta kasance jiha mafi karfin tattalin arziki a Afirka duk kuwa da rashin tallafi daga FAAC.
“Ba tare da wani tallafi daga FAAC ba, na gudanar da sauye-sauye a jihar Legas kuma a yau ita ce jiha mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka,” ya ce.
Ganin yadda wadannan kalamai na sa suka dauki hankalin jama’a da ma irin tasirin da zai iya yi a zukatan al’umma a lokacin da suka je yin zabe, mu ka ga cewa yana da mahimmanci DUBAWA ta binciki wannan batun
Zargin Farko (1) – Dan takarar kujerar shugaban kasa, Bola Tinubu a wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust ya ce Legas ba ta taba samun kasafin kudi daga kwamitin da ke kula da yadda ake kasafin kudin asusun tarayya ba lokacin da ya ke shugabanci a jihar
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi dangane da wani kudin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta bai wa jihar Legas amma ba ta ba ta ba. Daga nan ne mu ka gano wani rahoto a jaridar All Africa na shekarar 2005 inda shugaban kasa na wancan lokacin Cif Olusegun Obasanjo ya ke bayar da dalilansa na hana jihar Legas samun kudaden da aka ware wa kananan hukumomin jihar a wancan lokacin.
Bacin haka, ba da dadewan nan ba ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga gwamnoni da su rika zuba jari sosai a bangarori ko ayyukan da jihohinsu su ka fi karfi ta yadda za su rika samun kudaden shiga daga abubuwan da jihar ta mallaka domin yin hakan zai hana su dogaro kacokan da kudin da gwamnati ke bayarwa. Da ya fadi haka ne ya yi kwatance da sadda gwamnatin tarayya ta rike kudin da aka ware wa jihar Legas dan kananan hukumomin ta a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shekarar 2004.
A shafin Wikileaks wanda ke yawan tsegunta batutuwan siyasa da zamantakewa Dubawa ta gano wata takardar da aka rubuta a shekarar 2005 wanda ke bayanin yadda Obasanjo ya dakatar da kudin a 2004 amma an daina hakan sadda marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’adua ya hau mulki a 2007.
Dan haka daga cikin shekaru 8 din da Tinubu ya shafe yana gwamna a jihar Legas (199-2007) Tun shekarar 2004 jihar ba ta sake samun kasonta na kudin da gwamnatin tarayya ke bai wa kananan hukumomi ba har sai 2007 lokacin da ‘Yar’adua ya hau mulki
Wasu karin bayanan da aka yi a shafin Wikileaks sun ce matakin da jihar ta dauka wajen kirkiro sabbin kananan hukumomi ne a watan Afrilun 2004 ya sa Obasanjo ya dakatar da kudaden kananan hukumomin.
Ganin cewa Tinubu ya fara mulki a 1999 ne kuma sai 2004 aka dakatar da kudaden wato shekaru biyar bayan da ya fara mulki. Wannan furucin na shi ba dai-dai ba ne.
A Karshe
Bola Tinubu bai bayyana wa’adin lokacin da aka dakatar da kudaden a tsakanin shekarun da ya kasasnce gwamna ba, kuma bai fada takamaimai cewa kudin na kananan hukumomin jihar ba ne. Dan haka bai fadi cikakkiyar gaskiya ba.
Zargi na biyu (2) – A wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust Bola Tinubu ya yi zargin cewa jihar Legas ce jiha mafi karfin tattalin arziki a Afirka
Bisa bayanan shafin kididdiga na Statista Najeriya ta kasance kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka cikin shekaru 30 din da suka gabata.
Jimilar abin da kasa ke samu kowace shekara wato GDP na Najeriya ta karu da kashi 3.4 cikin 100 a bara, bayan ya ragu da kashi 1.92 cikin 100 a shekarar 2020, a cewar Al Jazeera.
A waje guda kuma, Legas ta riga ta yi suna a matsayin cibiyar ayyukan dijital wadda a yanzu haka take sauyawa zuwa cibiyar tattalin arzikin da ke aiki ba dare ba rana kuma bugu da kari tana bayar da kashi 10 cikin 100 na jimilar abin da kasa ta ke samu kowace shekara wato dala biliyan 432.3.
A cewar rahoton Aljazeera, jihar Legas din ce mafi karfin tattalin arziki a nahiya Afirka.
Mun lura da cewa wata kila ma dan takarar na nufin mafi karfin tattalin arziki a biranen Afirka.
A Karshe
Najeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka. Sai dai Tinubu na takamar cewa jihar Legas ce mafi karfin tattalin arziki a Afirka dan haka wannan zargin karya ne.