Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Akwai bukatar mazaje su rika yin jima’i sau 21 a duk wata don kaucewa kamuwa da cutar da ke da alaka da dajin mafitsara.
Sakamakon bincike: YAUDARA CE! Bincike da ke a kasa ya nunar da cewa akwai tufka da warwara, wanda ke nuni da cewa akwai bukatar zurfafa bincike, kwararru sun yi watsi da wannan da’awa a matsayin abin da masana kimiya suka gano, kasancewar har yanzu ana nazari kan batun.
Cikakken Sakon
Matsalolin mafitsara su kan zama na daban ne ga mazaje saboda abin ya shafi wata gaba muhimmiya wajen haife-haifen dan Adam. A kwai matsaloli guda uku da ke shafar mafitsara (three types of prostate problems):
Karyewar garkuwa (inflammation (prostatitis)), kumburin ‘yanhalitar da kan toshe mafitsarar (BPH, or benign prostatic hyperplasia) da cutar dajin mafitsara.
Cutar dajin mafitsara wani yanayi ne da akan samu wata halitta a cikin mafitsara yanayin ta kamar gyadar bature (walnut-shaped) za ta rika girma ba kakkautawa, wannan halitta ce da ke a mafitsarar maza ke fitar da wani ruwa mai yauki da ke taimakawa tafiyar maniyi.
A baya-bayan nan an samu wani bidiyo da aka yada (shared) ta kafar Naija (@Naija_PR) inda aka nuna wani jami’in lafiya da aka bayyana a matsayin Dr. Ken ke da’awar cewa lafiyayyen mutum ya kamata ya rika jima’i da mace sau 21 a wata guda don kada ya samu matsala da ke da alaka da mafitsara.
Daga bayanan da aka tattara daga bidiyon na minti daya da dakika 23 mun gano cewa bidiyon daga wani shiri ne na rediyo “The Discourse” da ake yi a gidan rediyon Classic FM, 97.3. Mutmin na jaddada cewa akwai bukatar cika yin jima’i, kuma ana so maza su samu abokan yin jima’i da yawa ma idan ta kama, don cika adadin yin jima’in da ya kamata su yi a wata.
“Abu ne da ya shafi lafiyar mai rai, ko dai a amfana da ita ko a rasa. Wannan ne abun da halittar cikin mafitsara (Prostate) ke bukata lokacin saduwa, gaba ya mike” Don haka nazari ya nunar da cewa lafiyayyen mutum ya kamata yayi jima’i sau 21 a wata don gudun kada ya samu matsala da ke da alaka da mafitsara, ko cutar dajin mafitsarar da abin da ya shafi zuciya. Idan ba ka jima’in akai-akai wannan halittar cikin mafitsarar za ta girma ta zama sila ta samun cutar dajin mafitsarar.
Ya zuwa ranar Juma’a 9 ga Fabrairu, 2024, wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 235,000 (views), da wadanda suka sake wallafa labarin 805 (reposts) da 241 da ke kafa hujja (quotes) baya ga masu nuna sha’awa (likes) 2,320.
Ganin yadda yanayin labarin ke haddasa cece-kuce ya nunar da yadda ya kamata a samar wa al’umma cikakken sako, musamman abin da ya shafi lafiya, hakan ya sa DUBAWA sa himma ta gudanar da bincike.
Tantancewa
Bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ya sadar da samun wata makala da wata gidauniya ta fitar (Urology Care Foundation) wacce ta yi nazari kan mazaje 32,000 a tsawon shekaru 18. Wannan nazari ya gano cewa mutanen da suke fitar da maniyi ko inzali akasari (mafi kankanta sau 21 a wata) suna da ragin kaso 20 cikin dari na yiwuwar su kamu da cutar dajin mafitsara fiye da wadanda ke iya fitar da maniyin sau hudu zuwa bakwai a wata guda. Sai dai gidauniyar ta ja hankali cewa fitar da maniyin na iya tasiri ko akasin haka ga yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsarar. Duk da cewa yana taimakawa wajen fitar da wasu sinadarai masu hadari da ke haduwa da maniyin, wannan baya nufin kai tsaye zai kawar da yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsarar.
Yana iya faruwa saboda wasu dalilai kamar tsarin kula da lafiyar mutum, gidauniyar ta nunar da bukatar kara zurfafa bincike, don gano ko yawan fitar da maniyi na rage yiwuwawr kamuwa da cutar dajin mafitsara ko akasin haka.
Wata makala (article by Healthline) da tayi nazari kan wannan bincike ta gano wasu nakasu da binciken ke da su, daya daga cikinsu shine yadda binciken ya dogara da irin amsa da mutane ke bayarwa don radin kansu.(daya a shekarar 1992 da daya a 2010) kan yadda suka bayyana yadda suke inzali ko fitar da maniyi a kowane wata ko wannan ya sa sun kamu da cutar dajin mafitsarar, don haka sakamakon na iya sauyawa ko su manta saboda ajizanci na dan Adam ko dalilin halayyarsu. Har ilayau nazarin bai nunar da cewa fitar da maniyin ta hanyar saduwa da mace ne ko kuma wasa da al’aura, yadda ake fitar da maniyin na iya tasiri a nan. Wata makala ta (Medical News Today) ta duba batun alakar yawan fitar da maniyi da hadarin kamuwa da cutar dajin. Makalar ta ce babu tabbas yawan fitarwa ko akasin hakan ga mutane da ke da mabanbantan shekaru na tasiri wajen kamuwa da cutar dajin, saboda tari na bincike kala-kala da aka yi tsawon shekaru ya nunar da bukatar da ke akwai ta a kara zurfafa bincike.
Wannan makala ta yi nazari kan binciken da aka yi (2004 study) wanda yayi nazari kan mutane 29,000 kan yadda suke yawan inzali a tsawon sama da shekaru takwas. Binciken da aka fada tun da fari na 2016 karin nazari ne kan wanda aka yi a 2004, shima ya goyi bayan cewa mutanen da ke yawan inzali na da karancin fargabar iya kamuwa da cutar dajin mafitsara idan aka kwatanta da wadanda ke da karancin inzalin. Sabanin haka a wani nazari a (2009 study) ya gano, yayin da yawan wasa da al’aura a fitar da maniyi ga masu shekaru 50 ko sama da haka ke da karancin yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsarar, yana kuma iya haifar da hadrin kamuwa da cutar ga mazajen da ke tsakanin shekaru 20 zuwa 30.Wani binciken kuma na baya-bayan nan a 2017 ya gano yawan inzali ga mazajen da ke da shekaru 30 yana ba su kariya sabanin haka kuma ga wadanda ke da shekaru 20 da 40.
A wata makalar sake nazari a (2016 literature review) ta kammala da cewa wasa da al’aura da yawan inzali da shekaru duk suna tasiri ga maza idan ana magana ta cutar, da kan shafi mafitsara sannan babu cikakkun shedu da suka nunar da cewa wadannan abubuwan baki daya suna da alaka.
Haka kuma a wani nazari (2018 meta-analysis) kan bincike guda 22 da aka yi kan batun na fitar da maniyi da hadarin kamuwa da cutar dajin mafitsara sun gano cewa matsakaicin inzali sau biyu zuwa sau hudu a mako yana da alaka muhimmiya da karancin yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsara. Wannan ya ba da kiyasi na fitar da maniyi sau takwas zuwa sha shida a duk wata. Sabanin adadin wanda yake wannan da’awa.
Wadane abubuwa ne ke iya haifar da barazanar kamuwa da cutar ta kansar mafitsara?
Yayin da ake danganta batun inzali ko fitar da maniyi a abubuwan da ka iya jawo ko azalzala barazanar cutar kansar mafitsara kamar yadda binciken da aka yi a sama suka nunar, abin da ake ganin zai taimaka wa mazaje sanin abin da ka iya yin sanadi na samun cutar.
Wadannan dalilai sun hadar da shekaru (yayin da mazaje suke kara shekaru barazanar da suke fuskanta ta yiwuwar su kamu da cutar kansar na karuwa.) Kimanin kaso 60 cikin dari na mazaje da suke kamuwa da wannan ciwo suna da shekaru sama da 65 ne)
Mazaje da suka fito daga Afurka ko Amurkawa bakar fata sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar idan aka kwatanta da fararen fata.
Mutanen da suka fito daga Andulus ko Spaniya da Amurkawa daga yankin Asiya suna da karancin fuskantar barazanar kamuwa da cutar kansar mafitsarar idan aka kwatanta da wadanda ba daga yankin ba ko da fararen ne,) Tsarin labarin kasa (Geography) na da tasiri. (Masu cutar kansar mafitsarar sun fi yawa a Amurka ta Arewa da Nahiyar Turai da Australiya idan aka kwatanta da yankiun Asiya da Afurka da Amurka ta Tsakiya da Amurka ta Kudu), tarihin iyali da kwayoyin halitta (Sauyi a kwayoyin halitta na (BRCA genes) , na kara barazana ta kamuwa da cutar kansar nono da kansar mahaifa tana iya tasiri nan ma) haka nan ma idan mutum na ta’ammali da sinadarai (Wasu binciken da aka yi sun nunar da cewa sinadaran Agent Orange da dakarun sojan Amurka suka yi amfani da su a lokacin yakin Vietnam ta yiwu suna da alaka da haifar da cutar kansar mafitsara).
Ra’ayin Kwararru
Mun yi magana da likitan mata Jeremiah Agim, wanda ya bamu shawarar mu nemi kwararre kan abin da ya shafi mafitsara amma ya bamu tasa fahimta, yace ai akwai dalilai da dama da ka iya jawo cutar da ta shafi mafitsarar ba kawai batun inzalin ba, idan kawai aka tsaya ga batun na fitar da maniyi ba lallai yayi tasiri ba.”Akwai dalilai da dama da ka iya zama sanadi, kama daga shekaru da tarihin iyali ( wato wadanda suka gaji kwayoyin halitta) har zuwa yanayin da mutum ke gudanar da rayuwarsa. Ko da kamuwa da kwayoyin cuta ko warkewa daga wani ciwon da ya shafi mafitsarar abun na iya shafa, da wasu abubuwan da ake samu daga muhalli, (misali bisphenol faga robobi), samun barazana daga sinadaran Iron da yin teba da yawan wasu sinadarai da suka shafi jima’in (sex hormone da wasunsu) Yawaitar inzali daya ne kawai, bana jin kara yawan jima’i wanda zai iya bude kofa ta wasu matsaloli, hakan zai iya tasiri kan abubuwa da ka iya jawo cutar ta dajin mafitsara. ”
Ya ma gano kuskure a irin fahimtar da me da’awar ke da ita kan amfanin halittar da ke cikin mafitsarar ta (Prostate) da yadda za a rika mommotsa ta da sunan atisaye:
“Na ga kuransa ga batun na amfani da rashin amfani. Idan aka kalli batun ta wannan fuska ita (Prostate) za ta za ma karama kenan babu samun cutar ta kansa, za ta kuma zama babba idan ana amfani da ita. Haka kuma ba sai lallai lokacin saduwa ba ne zakarin namiji ke mikewa . Sau tari yana mikewa idan mutum na barci . Idan zaka tuna ajin ka na Biology ilimin halittu masu rai wato darasin yadda halitta ta samu da girmanta (evolution) (Jean Lamarck’s theory of use and disuse.) Ya ma bayyana cewa samun bunkasar ana iya gadonsa.”
Da yake jawabi a dangane da bincike-bincike da aka yi, sai ya ce, “Idan ka koma baya ga bincike-bincike da aka yi , wadanda ke cewa fitar da maniyi akai-akai daya ne daga cikin hanyoyi na samun kariya daga cutar dajin mafitsarar ba su ce daga yin amfani da prostate ko dena amfani da ita ba.”Sun yi bayanin cewa fitar da maniyin na cire sinadarai marasa kyau ne wadanda idan ba a yi ba za su taru su zama barazana da ka iya jawo cutar ta kansar mafitsara.”
Mun kuma samu damar ji daga bakin masani kan abin da ya shafi mafitsarar kuma shugaban fannin kula da fida a Jami’ar Kula da Kimiyar Jinya (UNIMED) a jihar Ondo Olurotimi Ogundunniyi, wanda yayi fatali da wannan da’awa da ya bayyana a matsayin ra’ayin wani ba binciken kimiya ba.
”A baya mutane sun dauka yawan aikata jima’i da cutika da ake samu yayin saduwa su ke jawo cutar amma babu wani bincike da ya tabbatar da haka. Shin akwai wani bincike da ya tabbatar da cewa manyan malaman majami’a su suka fi kamuwa da cutar? Babu, don haka jita-jita ne akwai tarin makaloli wadanda ke fitar da bayanai amma babu bayanai na kimiya.Ina tabbatar maku da cewa yana bayyana ra’ayinsa ne ba bayanin kimiya ba.
Mun kuma yi magana da wani masanin a wannan fannin na iimi da ya shafi mafitsarar Emmanuel Adugba wanda babban darakta ne a asibitin Rock Creek Care Hospital Abuja. Mista. Adugba ya nunar da cewa ba a yi wani zurfin bincike ba a wannan fanni, amma batu ne na ra’ayin wasu.
“A wannan fanni babu wani zurfin bincike da aka yi. Duk wani abu da ya shafi jima’i mutane na son kambama shi, kowa na son bayyana nasa ra’ayi da kambamawa, ni nafi so a zurfafa bincike kan abubuwa ba wai mutum ya tsaya kan ra’ayinsa ba.”
Ya kara da cewa idan har yawan yin jima’i shine maganin cutar kansar mafitsara to babu shakka mutanen da basa yin jima’i ko wadanda suka kebe kansu su za su zama a gaba wajen kamuwa da cutar amma wannan ba haka yake ba.
A karshe
Yayin da aka sani cewar akwai tarin amfani na yin jima’i da yawan fitar da maniyi, wasu kuma bincke kadan sun nunar da cewa za a iya samun alakar da cutar kansar mafitsarar, babu wata alaka ta zahiri a tsakanin wadannan abubuwa biyu. Bincike da suke a kasa sun nunar da cewa akwai bukatar zurfafa bincike kan batun, sannan kwararru sun yi watsi inda suke kafa hujja da cewa har yanzu wannan batu ana ci gaba da nazari akansa.