African LanguagesHausaNews

Shirin Masu shirya Gasar Mace mafi Kyau a Duniya (Miss Universe) ya musanta batun shigar Saudiya a gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya 2024

Getting your Trinity Audio player ready...

Shirin gano mace mafi kyau a duniya (MUO) ya musanta labarin nan da yayi shuhura cewa kasar Saudiyya za ta shiga a fafata da ita wajen fito da mace mafi kyau a duniya a shekarar 2024.

Rumy Alqahtani ‘yar kwalisa daga Saudiyya ta dauki hankali a duniyar kafafan sada zumunta bayan da ta bayyana shigar kasar ta a dama da ita gasar sarauniyar kyau ta duniya 2024.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram hukumar da ke shirya gasar ta bayyana cewa babu wani shirin tantancewa da aka yi a kasar Saudiyya da aka tabbatar, duk wata da’awa kan hakan kuwa karya ce da yaudara.

”Zakulo wadanda za a fafata da su don su wakilci kasarsu a gasar sarauniyar kyau ta duniya aiki ne tukuru wanda ke bin ka’idoji da tsare-tsarenmu.” Matsayar masu shirya shirin  kenan.

Duk da wannan kin amincewa daga masu shirya gasar, Ms Alqahtani da ke wakiltar Saudi Arabia a taruka na kasa da kasa da suka hadar Miss Arab Peace da Miss Planet da Miss Middle East bata cire wallafar da ta yi ba a shafinta na cewa kasar Saudiyya za ta shiga a dama da ita a gasar sarauniyar kyau ta duniyar ba.

Sharudan zabar sarauniyar kyau kai tsaye daga masu shirya gasar (MUO)

Sarauniyar kyau ta duniya 2024 an tsara za a yi a Mexico a watan Satimba inda ake sa rai mata sama da 100 daga sassa daban-daban na duniya za su shiga gasar a dama da su.

Masu tsara gasar sun jaddada cewa matakan zabar za su kasance na taka tsantsan inda za a tabbatar da adalci a fayyace komai a fili.

“ Kowace kasa za ta bi matakai daki-daki da kaidoji a tabbatar da daidaito da yin komai a fili wajan zakulo wadanda za su shiga a dama da su.” A cewar masu shirya gasar.

Yayin da Saudiyya ba ta tabbatar da shiga a dama da ita ba a matsayin kasa, Masu shirya gasar sun bayyana cewa kasar kawo yanzu tana gudanar da “shirin tantancewa” don yiwuwar shiga a dama da ita.

Jawabin masu shirya gasar ya kara da cewa “Saudiyya ba za ta samu gurbin shiga a wannan gasar sarauniyar kyau ba har sai a karshe kwamitinmu ya tabbatar da za ta shiga a hukumance.” 

Masu shirya gasar (MUO) sun jaddada cewa gasar da za a yi anan gaba a Mexico wadanda za su shiga a fafata da su sama da 100 za su fito daga kasashe daban-daban na duniya.

Masu shirya gasar sun tabbatar da cewa za su mayar da hankali kan duba banbance da ke akwai da tafiya da kowa wajen nuna baiwar kyau da basira na matan da suka fito daga sassa daban-daban na duniya.

Kafin masu shirya gasar su yi watsi da tabbacin shigar Saudiyyan, ‘yar kwalisan mai shekaru 27  ta shirya wakiltar kasar ta a zaben sarauniyar kyau ta duniya 2024, matakin da ka iya zama na sauya matsayar kasar a idanun duniya, kasar da aka san ta da ra’ayin rikau.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »