African LanguagesHausa

Wace ce macen da ta fara kasancewa sanata a tarihin Najeriya? Ga abun da mu ka gano 

Yayin da ake kiraye-kirayen kara samun wakilcin mata a fagen siyasar Najeriya, mata kalilan ne suke taka rawar gani a guraben da ake jefawa kuri’a a zabukan da aka kammla kwanan nan duk da cewa dai adadin matan a guraben siyasa yanzu ya fi wanda aka rika samu a baya.

Daga watan Fabrairun 2023 kungiyar kwadagon hadin gwiwar ‘yan majalisa ta ce mata a Najeriya na matakin 182 daga ciki 186. Idan aka yi batun wakilcin mata a a majalisa, wanda ke nufin kasashe hudu kacal ta tsere ma wa.

Lokacin zaben 25 ga watan Fabrairu, Ireti Kingibe, ‘yar takara a inuwar jam’iyyar LP na daya daga cikin mata kalilan din da suka sami mukaman siyasa. Ita ce ta yi nasara a matsayin zababbiyar sanata na birnin tarayya Abuja, wato FCT.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Peter Obi, daga baya ya gana da Kingibe, inda ya ce ita ce sanata mace ta farko a FCT. Sai dai da muka gudanar da bincike mun ga wani binciken da Fact-Check Hub ta yi inda ta karyata wannan zargin. 

Bincike ya nuna cewa Khairat Abdulrazaq-Gwadabe ta taba rike wannan mukamin na sanatar da ke wakiltar FCT daga 29 ga watan Mayun 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2003.

Bacin tantance gaskiyar wannan batu, sabbin mahawarori dangane da batun sun sake bayyana a shafin Twitter abun da ya sa fayyace gaskiya ya zama a tilad.

Ranar 12 ga watan Maris 2023, wani mai amfani da shafin Twitter, @GbenroAdegbola, ya ce Ms Abdulrazaq-Gwadabe ita ce sanata ta farko a birnin tarayyar Abuja da watan Mayun 1999 zuwa 2003.

Ya kuma kara da cewa Franca Afegbua ita ce sanata mace ta farko a Najeriya, kuma a wancan lokacin ta wakilci mazabar arewacin tsohuwar jihar Bendel daga watan Oktoba zuwa Disembar 1983, yayin da Wuraola Esan ita kuma an ba ta matsayin ne ba tare da an je zabe an jefa mata kuri’a ba a shekarar 1960.

DUBAWA ta bibiyi tarihin sanatoci mata a kasar domin tantance rudani da ke kewaye da yadda aka sami sanatoci mata a kasar.

Shimfida dangane da majalisar dattawa

Majalisar dattawa na zaman daya daga cikin bangarori biyun da suka hadu suka samar da majalisar dokokin kasar a tsarin da Najeriya ke amfani da shi na majalisar dokoki mai bangarori biyu ko kuma bicameral legislature kamar yadda ake kira a turance.

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya na da bangarori biyu ne bisa tanadin sashi na hudu na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 wanda ya kunshi kujeru 109 na sanatoci bayan da aka raba duka jihohi 36 da ke kasar zuwa mazabu uku kowanne. Dukkansu kuma kan zabi sanata bayan an yi zabe. Birnin tarayya Abuja kuma ta kan zabi sanata guda daya ne ita ma bayan an yi zabe.

Tarihin sanatocin FCT Abuja, birnin tarayya

Bisa bayanan tarihi, Daniel Yakwo ya taba kasancewa sanata a majalisar dokoki ta biyu. Tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Alhaji Shehu Shagari (1979 zuwa 1984) ya ba shi matsayin shi ma ba zabe aka yi ba.

Haka nan kuma, an zabi Hassan Asa Haruna Tadanyigbe na jam’iyyar SDP ranar  4 ga watan Yulin 1992 a matsayin sanatan da ke wakiltan birnin tarayya. Shekara daya bayan nan ne aka rusa majalisar dokokin bayan da sojoji suka yi juyin mulki a karkashin jagorancin janar Sani Abacha.

Bayan da aka shafe shekaru 16 ana mulkin soji, Najeriyar ta koma ga mulkin dimokiradiyya a shekarar 1999 bayan da shugaban wucin gadi na wancan lokacin Janar Abdulsalam Abubakar ya sanar da hakan.

Kundin tsarin mulkin kasar ta sake farfadowa dan a cigaba da mulkin demokiradiyya, wannan ne ya sa aka sake maido da majilisun biyu wadanda suka girka majalisar dokokin kasar wato da majalisar dattawa da ta wakilai.

Macen da aka fara zaba a matsayin sanata a birnin tarayyar Abuja

Ms Abdulrazaq-Gwadabe ce aka fara zaba a matsayin sanatar da ke wakiltar the birnin tarayya a majalisar dokoki daga 1999 zuwa 2003, wanda shi ne ya sa ta zama sanata mace ta farko a cikin wadanda suka wakilci babban birnin Najeriyar a majalisa.

Sauran wadanda suka biyo bayan Ms Abdulrazaq-Gwadabe a matsayin sanatan sun hada da Isa Mania (2003-2007); Adamu Sidi Ali (2007-2011); Phillip Tanimu Aduda (2011-2023); and Ireti Kinigbe (2023 – har yanzu).

Cif Franca Afegbua: Sanata mace ta farko a Najeriya

Cif Afegbua, wadda ta yi suna a matakin kasa da kasa saboda aikinta na shamfo ko kuma gyaran gashi ta sami kuri’un da suka ba ta kujerar sanatan ne a shekarar 1983. Ta tsaya takara a zaben shekarar 1983 a karkashin inuwar jam’iyyar NPN inda ta yi nasara ta sami kujerar mazabar yankin arewacin tsohuwar jihar Bendel.

Mutane sun yaba wa marigayiyar saboda yadda ta jajirce ta tsaya takara duk da cewa tana jam’iyyar adawa ne a wancan lokacin.

A wata hirar, da aka yi da ita a shekarar 2022, ta ce “mutane sun san mata da cika alkawari. Wanna ne babban abun da ya sa aka zabe ni. Na yi niyyar cika duka alkawuran da na yi wa mutane, kuma sai da na tabbatar sun fahimci hakan.

“A tunani na an sami cigaba sosai tun bayan lokaci na. Ba’a taba samun mace a majalisar dokoki ba kafin ni, amma yanzu akwai mata. A lokacin ni ce kadai mace, amma yanzu akwai mata fiye da daya. A gani na adadin yanzu ma zai karu a hankali.”

Wuraola Esan: Sanata macen da aka fara bai wa mukamin ba tare da zabe ba

Wuraola Esan, mai gwagwarmayar siyasa ce wadda ta yi gwagwarmayar samarwa mata da ‘yan mata ‘yancin yin ilimi, wadda kuma ta kasance sanata mace na farko a majalisar dokokin Najeriya a jamhuriya ta farko.

An bai wa  Esan mukamin na sanata ne a yankin Yammacin Najeriya a karkashin Jam’iyyar Obafemi Awolowo ta AG a shekarar 1960.

Ta taka rawar gani sosai a kungiyar matasan Naajeriya, jam’iyyar NCNC (sadda take hade da Kamaru) 

Dan haka duk da cewa Ms Kingibe ce sanatan FCT yanzu tana daga cikin mata kalilan da suka rike mukamin a kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button