Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin sada zumunta yayi da’awar (claim ) cewa mazauna birnin Abuja sun afka wani rumbun ajiya mallakar Hukumar ba da Agajin Gaggauwa a Najeriya NEMA inda suka sace kayayyaki da ke rumbun.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon da aka bincika an gano cewa wani aikin batagari ne da suka afka runbun ajiya mallakar Hukumar Raya Ayyukan Gona da ke Abuja.
Cikakken bayani
A kwanakin baya-bayan nan an rika samun rahotanni da ke nuni da cewa, wasu al’umma ‘yan Najeriya na afkawa motocin dakon kaya dauke da kayayyakin abinci, wasu lokutan kuma na afkawa rumbunan ajiya ne su balle, su kwashe kayayyakin da ke ciki. Na baya-bayan nan shine abin da ya faru a Zaria, Kaduna da kuma wanda aka yi a kan hanyar zuwa Kadunan a yankin Suleja area of Niger state.
A ranar uku ga watan Maris, 2024 wani bidiyo da yayi shuhura a shafukan sada zumunta musamman na X ya nuna yadda mazauna birnin Abuja suka kutsa kai rumbun ajiyar kayan abinci mallakar Hukumar ba da Agajin Gaggawa NEMA.
Wani bidiyo da mai amfani da shafin na X @PIDOMNIGERIA ya wallafa ya samu wadanda suka kalla su 100,000 ya kuma buga taken labarin bidiyon kamar haka:
“Yunwa da Talauci a Najeriya: Mazauna birnin Abuja sun afkawa rumbun ajiyar kayayyakin abinci mallakar Hukumar ba da Agajin Gaggawa NEMA inda suka yi awon gaba da kayan abinci da kayan tallafi, Idan har baa yi wani abu ba, cikin gaggawa a tsayar da yunwa a fadin kasa, nan ba da dadewa ba abin da zai saura a sace shine abincin masu arziki.”
Wannan wallafar ta ja hankali (reactions) sosai, daga wadanda suke amfani da kafar. Mutane da dama kuma sun sake yada bidiyon a kafofin sada zumunta na zamani shafin X da Facebook ciki kuwa har da nan: here, here, da here.
Ganin yadda wannan bidiyo ya yadu da hadari da ke tattare da labarin mun shiga aikin binciken wannan da’awa ganin yadda suke biyo bayan zanga-zanga a sassan Najeriya inda jama’a ke kokawa da halin kunci na tattalin arziki da suka samu kansu a ciki.
Tantancewa
Da aka saurari sakon muryar, namiji ne da alama ya hada bidiyon wanda ke bayani duk da cewa akwai hayaniya a bayan muryar tasa.
“Wannan rumbun jiyar kayan abinci ne da ke Dei Dei Karimo da Tasha mutane na halin yunwa kamar yadda kuke gani kai tsaye.”
Bayanan ba su nuna cewa rumbun ajiyar mallakar hukumar NEMA ba ne.
Ita ma a nata bangare hukumar ta NEMA @nemaNigeria ta mayar da martani kan wannan bidiyo da ya yadu inda tace wannan lamari da ya faru ba a wajen ajiyar kayayyakinmu ba ne.
Bara mu dauko bayanan daya daga cikin masu wannan da’awa (claims,) ta yaudara da ke cewa NEMA ta ce:
.”Hukumar NEMA ta karyata yin sata a rumbun ajiyarta a ranar Lahadi a Abuja, kafafan yada labarai sun ja hankalin hukumar cewa wasu batagari a ranar Lahadi sun afka rumbun ajiyar kayayyakin abinci mallakar hukumar da ke Abuja.”
“Wannan jawabi ne da ke nuni da cewa wannan wajen ajiyar kayan abinci ba mallakin NEMA ba ne, sai dai duk da haka hukumar ta tausayawa wanda aka afkawa rumbun ajiyarsa aka yashe masa kayayyaki. Domin gudun kada ayi, Babban Daraktan hukumar ta NEMA Mustapha Habib Ahmed ya ba da umarni ga daraktocinsa na shiya-shiya da shugabannin sassan gudanarwa su karfafa tsaro a ciki da wajen ofisoshin hukumar da ma rumbunan ajiyar hukumar da ke fadin Najeriya.”
Daraktan tsare-tsare da hasashe a hukumar ta NEMA Onimode Bamidele, ya tabbatar (confirmed) cewa rumbun ajiyar da aka yashe mallakin sashin hukumar kula da ayyukan gona ce da ke Abuja. “Abin takaici mun tashi mun ji irin wannan labari, domin mu tabbatar da ‘yan Najeriya wadannan rumbuna ba mallakinmu ba ne sai du muka yi tattaki har zuwa nan don tabbatarwa.”
An sanar da mu cewa wadannan rumbunan ajiya mallakar sashin ayyukan gona ne na Abuja, inda ke ajiye hatsi. Abin takaici ne matuka abin da ya faru.”
Bayan da aka gudanar da bincike Zakari Alyu jami’in hulda da jama’a a sakatariyar kula da ayyukan gona a Abuja ya tabbatar verified da gaskiyar wawashe rumbun ajiyar sai dai bai yi karin haske ba.
A karshe
Bidiyon da ke nuna cewa an sace kayan abinci a rumbun ajiyar Hukumar ba da Agajin Gaggawa NEMA yaudara ce, lamarin ya faru ne a sashin kula da ayyukan gona hukumar da ke kula da Birnin Tarayya Abuja.