African LanguagesHausa

Wani mawaki dan Najeriyar da ya rasu shekaru 12 da su ka gabata, an ga sunarsa a jerin sunayen wadanda ‘yan sandan Saliyo ke nema

Zargi: ‘Yan sanda a Saliyo sun wallafa wadansu sunaye na wadanda ake zargi da kaddamar da zanga-zangar da ta yi sanadiyyar rayuka ranar 10 ga watan Agustan 2022. Sai dai daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna “DaGrin” wani mawaki dan asalin Najeriya ne wanda ya riga ya riga mu gidan gaskiya, amma jami’an ‘yan sandan sun ce dan asalin Saliyo

Wani mawaki dan Najeriyar da ya rasu shekaru 12 da su ka gabata, an ga sunarsa a jerin sunayen wadanda ‘yan sandan Saliyo ke nema

Ba gaskiya ba ne! duk da cewa DUBAWA ba za ta iya tantance duk wadanda ke cikin jerin sunayen ba, bincike ya tabbatar da cewa daya daga cikinsu DaGrin ya yi shekaru 12 da rasuwa dan haka babu yadda za’a yi ya kasance cikin wadanda su ka haddasa rikicin

Cikakken bayani

A ‘yan kawanakin nan Saliyo ta shiga kanun labarai sau daya amma bisa dalilai marasa dadin ji. Zanga-zangar da ta kamata ta kasance na lumana ranar 10 ga watan Agusta 2022 ta rikida ta zama tashin hankalin da ya kai ga hallakar mutane fiye da 20 a ciki har da jami’an ‘yan sanda.

Har yanzu ba a kai ga tantance ainihin wadanda suka shirya zanga-zangar ba duk da cewa gwamnatin kasar na zargin ‘yan adawa da shirya taron da ma haddasa kashe-kashen da suka biyo baya.

Shugaban kasar, Julius Maada Bio tare da jami’an tsaro sun sha alwashin gudanar da binciken da zai gano wadanda suka aikata wanann ta’asar domin a ladabtar da su. Dan haka gwamnati ta girka wani kwamiti mai mambobi 15 dan gudanar da binciken.

Ko da shi ke tun ma kafin gwamnati ta kafa kwamitin, ‘yan sandan na Saliyo su ka kaddamar da bincciken gano makasudin rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar. Haka nan kuma an fitar da wani jerin sunaye na wadanda ake zargi da shirya rikicin na ranar 10 ga watan Agusta.

Sunayen wadanda ke dauke da hotunan wadanda ake zargi ya bulla da tambarin kasar Saliyo tare da bayanin cewa duk wadanda ke ciki ‘yan Saliyo ne. A karkashin sunayen kuma akwai lambobin wayar da aka ce na ‘yan sanda ne. Lambar ce ake kira ga duk wanda ya san wani a cikinsu ya kira ya bayar da karin bayani cikin sirri kuma za’a ba shi kudi, 3,000 Nle.

Sai dai daya daga cikin hotunan ana kyautata zaton hoton wani mai suna Olaonipekun Oladapo Olaitan ne wani dan Najeriyar da ake wa inkiya da DaGrin, abin da kuma ya yi sanadin jayayya.

Wani mai rubuce-rubuce a soshiyal mediya a Saliyon wanda ake kira Kings Cross ya wallafa hoton a shafin shi da takaitaccen bayani kamar haka: “Hukumar ‘yan sandan Saliyo ta fitar da hotunan wadanda ta ke zargi da shirya zanga-zangar da ta rikida ta zama tashin hankalin da ya yi sanadiyar rashin rayuka da ma lalata dukiyoyi.

“Daga cikin wadanda ake zargi har da wani mawakin Najeriyar da ya rasu shekaru 12 da suka gabata. Bari tun yanzu mu bai wa ‘yan Najeriya hakuri dangane da damuwa ko rashin jin dadin da wannan bayani zai iya janyowa domin kawo yanzu Sfeto Janar din mu bai gama lakantar aikin shi ba.”

Da yawa masu amfani da taskokin blog su ma sun wallafa hotunan da tsokaci makamancin na King Cross.

Tantancewa

Lallai DUBAWA ta dauki wannan batun da mahimmancin gaske saboda alakar da ya ke da shi da tsaron kasa da kuma zanga-zangar da ta riga ta yi sanadiyyar mutane sama da 20 wadanda a cikinsu har da jami’an tsaro. Yanzu kuma da bullar sunan DaGrin cikin sunayen da ‘yan sandan su ka fitar abun ya dauki sabon fasali.

Domin tantance wannan zargin DUBAWA ta fara da tantance ko ita kan ta kasidar da ke dauke da hotuna da sunayen wadanda ake zargin ya fito daga ofishin ‘yan sandan ne ko a’a. Mai gudanar da wannan binciken ya tafi ofisoshin ‘yan sandan da ke Lumley da Kissy, yankunan da aka wallafa hotunan dan tantance ko ‘yan sandan ne suka fitar da hotunan a zahiri. To sai dai jami’an ‘yan sandan wuraren biyu duk sun ki su yi magana da mai binciken a hukumance. Daga nan ne DUBAWA ta kira lambar wayar da aka lika a hoton, nan da nan wani dan sanda ya amsa amma kuma da aga tayar da batun DaGrin sai ya yi wuf ya kashe wayar. Da aka yi kokarin sake kira ba wanda ya amsa. Sai dai mun iya mun tabbatar cewa lallai ‘yan sandan ne suka fitar da sunayen.

Binciken Hotuna

Bayan da muka tantance cewa kasidar ta fito daga ofishin ‘yan sanda ne, DUBAWA sai ta fara tantance hotunan daya bayan daya musamman na DaGrin.

Binciken ya nuna cewa shafukan labarai da dama sun yi amfani da hoton na DaGrin inda su ka yi bayanin yadda mawakin ya rasu sakamakon ciwon da ya ji bayan wata hatsarin motar da ya yi a jihar Legas a shekarar 2020 lokacin da ya afka wa wata katuwar motar da ke tsaye.

DUBAWA ta kuma yi amfani da manhajar Tineye wacce ke tantance mafarin hotuna. A nan ne muka gano hoton a wani shafin labaran Ghana mai suna modernghana. Shafin ya yi amfani da hoton ne a labarin da ya yi na rasuwar DaGrin din wanda su ka wallaga 15 ga watan Mayun 2010.

Mun kuma sake gano wani shafi a instagram mai suna @dagrin_official wanda ya nuna cewa shafin da ma’abotan mawakin suka kirkiro ne. Daga cikin hotunan da ke shafin, akwai wanda mawakin ya yi sarka da bindiga a wuyarsa. Shafin ya wallafa wannan hoton ranar 30 ga watan Yulin 2014, wannan shekaru hudu ke nan bayan mutuwarsa.

Duk da cewa babu wata hujja takamaimai dangane dainda aka aka dauki hoton, kafofin yada labarai da dama sun ce mawakin dan Najeriya ne amma ya yiwu yana Saliyo a lokacin da aka dauki hoton.

Wannan hujja ne ma ya tabbatar cewa ba DaGrin a shekarar 2010 ya mutu kuma babu yadda za’a yi a ce ya kasance a wurin zanga-zangar ta ranar 10 ga watan Agusta 2022

Me ‘Yan Najeriya ke cewa? 

 DUBAWA ta tuntubi wani mai sharhi kan wakokin Najeriya mai suna Emmanuel Daraloye dan samun karin bayani dangane da DaGarin.

“DaGarin mawakin rap ne wanda ke yin wakokin na sa a yarbanci, shi ne ya haskaka sauran masu yin wakoki irin na rap a harshen yarbancin a shekarun 2010. Shi ya fara bulla kafin irin su Olamide, DDQ da sauran mawaka irin shi,” Daraloye ya bayyana.

“Ya mutu ranar 22 ga watan Afrilun 2010 a asibitin koyarwa na jihar Legas wato LUTH bayan da ya yi hatsarin mota,” ya ce da ya ke tabbatar da mutuwar DaGrin.

Daraloye ya yi mamakin ganin hoton DaGrin da ma sunan shi cikin sunayen wadanda ‘yan sanda ke nema bayan shekaru 12 da mutuwa, inda ya ce ya kamata ‘yan sandan Saliyo su rika kulawa sosai.

Me ‘yan Saliyo ke cewa?

DUBAWA ta tuntubi wani sananne a masana’antar wakokin Saliyomai suna Bockarie Mattia dan jin ko mawakin mai rasuwa ya yi wasa a Saliyo kafin mutuwarsa. A cewarsa babu abin da ya nuna cewa mawakin ya yi wasa ko ma ya je yin wani abu na kansa a Saliyo, sai dai ya bayyana cewa lallai DaGrin sananne ne a Najeriya wanda ya yi suna sosai daga shekarar 2008 a fagen wakoki kafin ya rasu.

Karin abubuwan da ya kamata a sani dangane da DaGrin

An haifi Olaonipekun Oladapo Olaitan (aka DaGrin) 15 ga watan Oktoba 1987 a jihar Ogun Najeriya

Aiki da wakokin DaGrin

DaGrin shaharren mawaki ne na hip hop kuma ya sami lambobin yabo a wannan fannin.

Ya na daga cikin ‘yan Najeriyan da suka rika wakoki cikin harshen su na haihuwa a maimakon turancin ‘yan Najeriya ko kuma pidgin english wanda aka fi amfani da shi a kasar. Yana daga cikin wadanda su ke da basirar wakoki domin ya yi hadaka da mawaka daban-daban irin su D.J Neptune, M.I Frenzy, 9ice, Konga da sauransu.

DUBAWA ta kuma gano cewa akwia faifan da ya yi wanda ya sami lambar yabo a 2010 – a bukin martaba mawaka da masu fina-finai a Najeriya wato Nigerian Entertainment Awards (NEA).

Mawakin ya yi wakoki da yawa amma wadanda su ka fi daukar hankali guda 50 ne wadanda su kahada da “If I Die, Kondo, DaGrinponPon Pon (Instrumental), Hola-Hola, Swag, Ghetto Dream, Da Grin – If I Die, Idi Nla, Kekere da sauransu.

Kadan daga cikin wakokin da ya yi tare da shahararrun mawaka sun hada da My Pain (Part 2) ft. Dude Tetsola, Bigiano da Omawumi Thank God; Mo ti Gboro ft. Isolate da sauransu.

DaGrin ya rasu ne bayan da ya yi hatsarin mota 14 ga watan Afrilu 2010 a hanyar Agege da ke Mushin jihar Legas.

Ra’ayin ‘Yan Sanda

DUBAWA ta tuntubi kakakin ‘yan sandan Saliyo Supt Birma Kamara dan tambayarsa yadda aka yi sunar wani wanda ya yi shekaru 12 da mutuwa ya bayyana cikin jerin sunayen wadanda hukumarsa ke nema da zargin hadasa rikici a watan Agustan 2022. Kamara bai amsa tambayar ba sai dai ya ce “na fita ina wajen jarabawa.” Bisa bayanan da muka samu dangane da tsarin gudanarwar ‘yan sandan Saliyo, babu wanda ya isa ya yi magana dangane da abubuwan da ke faruwa da ‘yan sanda sai shugaban sadarwa.

A Karshe

Binciken DUBAWA ya nuna cewa hoton daya daga cikin mutanen da ‘yan sandan Saliyo ke nema, mai suna Olaonipekun Oladapo Olaitan dan Najeriya ne, kuma mawaki wanda ya rasu shekaru 12 da su kagabata a hatsarin mota dan haka babu yadda za’a yi a ce yana tare da masu zanga-zanga a Saliyo a watan Agusta.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button