|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken Sako
Mahukuntan Babban Birtnin Tarayyar Najeriya(FCTA), karkashin jagorancin ministan babban birnin Najeriya Nyesom Wike, na gudanar da aikin Rusau na gine-gine da aka yi su ba bisa ka’ida ba da kokarin dawo da wasu filaye, saboda dalilai na gyara kan filayen da aka ba da su ba bisa ka’ida ba, da gine-gine da ba a ba da damar yinsu ba a Abuja.
A kan irin wannan yanayi ne sai gashi shafukan sada zumunta sun dauki labarai a ranar 11 ga watan Nuwamba,2025 inda aka ga bidiyon takaddamar da ta barke tsakanin Minista Wike na Abuja da wani sojan ruwa a Najeriya.
Wannan takaddama da ta ja hankali, ta faru ne a lardin Gaduwa da ke babban birnin Tarayyar Najeriya a wani fili mallakar tsohon shugaban rundunar sojan ruwan Najeriya Awwal Gambo.
A lokacin da ministan babban birnin Najeriyar ya tunkari wajen, sojan ruwan da ke wurin Ahmed Yarima an yi zargin yayi wa ministan turjiya bayan da ya nemi wasu bayanai na takardu da ministan yace sojan ya gaza bayarwa a kan filin.
Takaddamar ta yi zafi sosai bayan da sojan ruwan ya jajirce cewa basu je wajen don barazana ga kowa ba daga hukumar babban birnin tarayyar na FCTA face su suna bin umarni ne.
Babban jami’in sojan ya kara bayyana cewa filin na wani babban jami’i ne abin da ya kara tada kurar rikicin.
Wannan lamari dai ya jawo muhawara inda al’umma ke neman sanin ko dama soja na da iko na shiga harkoki da suka shafi fararen hula.
Wasu wuraren da aka ga shigar sojoji sun hadar da nan da nan,
Duba da hakkin da ya rataya a wuyan DUBAWA a kan abin da ya shafi ilimantarwa da samar da bayanai (MIL), wannan shiri yayi kokari wajen ganin a ware aya da tsaba kan abin da ya shafi sojoji da faraen hula ta yadda al’umma za su fahimci abin da doka ke cewa; ta aminta a yi da abin da doka ta haramta.
Me doka ke cewa a game da wannan batu?
Karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana karara matsayar soja a Sashi na 217 (2). Ya bayyana cewa sojoji alhaki ne da ya rataya a wuyansu su ba da kariya ga iyakar kasa da duk wani abu da zai so yi wa kasar kutse daga waje don tsare mata iyakarta.
Kamar yadda wannan sashi ya nunar aiki na farko da ya rataya a wuyan sojoji shine tsare mutuncin kasa, ba abubuwan da suka shafi jagorancin fararen hula ba. ”Haka kuma wani abun muhimmi shine ana iya jibge dakarun tsaron a “wajen wani aiki kamar yadda dokar majalisar dokokin ta tanada.”
Wannan tsari ya nuna takaitar kai dakarun don harkoki na cikin gida sai dai idan ya samun goyon baya babba daga masu madafun iko, musamman shugaban kasa ko wata hukuma da aka dorawa wannan alhaki.
A wane lokaci ne sojoji ke shiga cikin fararen hula don gudanar da wani aiki?
Karkashin tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, akwai wasu yanayi kalilan da sojoji za su iya shiga harkokin fararen hula.
Dokar dakarun tsaron mai lamba (Cap A20, LFN 2004) wannan ta ba wa shugaban kasa dama ya aika dakarun soja a yanayi da za su taimaka wa mahukuntan fararen hula kamar jami’an ‘yansanda, a yanayi da aka samu kai na rashin bin doka da oda. Wannan ya fi bayyana a lokacin da aka samu wata babbar zanga-zanga ko rikicin kabilanci da ayyukan ta’addanci da kai wa mutane farmaki da aka samu a fadin kasa wanda aikin yafi karfin ‘yansanda.
Misalin irin wannan aiki ya hadar da na dakarun Operation Python Dance da dakarun murmushin kada (Operation Crocodile Smile) da dakarun Operation Safe Haven, duk wadannan na tallafa wa ‘yansanda ne su dawo da bin doka da oda a kasa.
Kari akan wannan dakarun sojan Najeriya za su iya taimakawa a harkoki da suka shafi tallafar al’umma a lokacin ambaliyar ruwa da lokacin da aka tafi nema da ‘yanto wasu mutane ko a wani lokaci na dokar kar-ta-kwana kamar a lokacin cutar (COVID-19) da aka rufe kasa, wanda ke zama wani bangare ne na aikinsu ga kasa baki daya.
Ana kuma iya jibge dakarun sojan wajen kare wasu kadarori na kasa kamar bututun mai na kasa da filayen jiragen sama da iyakokin kasa inda aka ga alamu na yin zagon kasa ko barazana ga tsaron kasa.
Me kwararru ke cewa
DUBAWA ya magantu da Francis Ochie, masani kan harkokin shari’a kuma mai ba da shawara daga jami’ar Veritas wanda yayi magana kan dalilai na halasci da ke sawa a kai sojoji wurin da ke zama na fararen hula ne.
Francis yace shugaban kasa ne kawai ke da iko ya tura sojoji saboda shine kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi wannan dama. “Karkashin tsarin sojoji a Najeriya shugaban kasa shi ke da iko ya tura sojoji kamar yadda ya samu dama daga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.” a cewar Francis.
“Dokar da ta kafa sojojin ma ta sashi na 218 ita ta ba da damar wannan aiki.”
Francis yace tura sojoji wurin fararen hula abu ne da ke da iyaka ana kuma sa ido a kansa.
“Amfani da sojoji na zuwa ne yayin dakile wata barazana ko tallafar fararen hula kuma na zuwa ne bayan samun umarni daga shugaban kasa, kuma abu ne da majalisa ke da ta cewa a kansa, tura dakarun ba haka kawai ake ba, sai da sanya idanu.”
Ya kara da cewa gwamnoni na iya neman tallafi na soja ta hanyar Sifeto Janar na ‘yansandan Najeriya a wasu lokuta na daban, kamar yayin ayyuka na ta’addanci da zanga-zanga da kai farmaki, sai dai a wannan yanayi ma sai shugaban kasa ya amince.
Har ila yau sashi na 218(4) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya nunar da cewa idan kai sojoji zai wuce wata daya to dole sai majalisar dattawa ta amince bayan duba na tsanaki.
Francis ya bayyana cewa soja ba shi da hurumi a doka na shiga harkokin fararen hula kamar takaddama kan fili ko tabbatar da ganin an bi umarnin kotu a gudanar da rusau.
Sojoji na tallafa wa fararen hula ne kawai idan lamura suka kazanta, ya zamana ‘yansanda ba za su iya shawo kan matsalar ba.
Sai ya ba da labarin abin da ya faru a 2005, abin da ya hada da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, inda kotu ta ba da umarni cewa shigar soja kan harkoki na zabe ya sabawa dokar da ta kafa aikin na soja.
Ya kara da cewa soja ba aikinsa ba ne ya tilasta yin abu, bai kamata ya shiga harkokin da fararen hula za su iya warware su ba.
DUBAWA har ila yau tayi magana da Yusuf Salawu lauya a ofishin lauyoyi na Tayo Laleye & Co., don jin nasa ra’ayin kan batun shigar sojoji kan harkoki da suka shafi fararen hula, kamar abin da ya shafi rikicin filaye ko tursasa ganin an gudanar da rusau na gwamnati.
Yusuf yayi bayani da cewa akwai wurin da soja kan iya shiga, kamar wajen tallafa wa mahukuntan fararen hula kamar ‘yansanda don ganin an maido da bin doka da oda da kare wasu kadarori ciki kuwa har da kadarori na soja, sai dai irin wannan aikin nasu na da iyaka a dokance.
Da yake magana kan abin da ya faru a baya-bayan nan da ya hadar da minisatan babban birnin Najeriya, yace kotun koli a Najeriya na jaddada cewa akwai iyakoki kan wannan.Hukunce-hukunce da aka yi kamar na Onunze da jiha (Onunze v. State (2023) da hukuncin shari’ar da aka yi tsakanin rundunar sojan saman Najeriy da James (Nigeria Air Force v. James (2002) sun nunar da cewa bai wajabta ba ga sojoji su bi umarni wadanda aka kafa su ba a bisa ka’ida ba, ko don son rai kamar kare wani fili mallakin wani ko kawo cikas a ayyukan wani jami’i da doka ta bashi wani aiki a hukumance.
“Jami’an da suka kakaba irin wadannan umarni da suka sabawa doka za su iya fuskantar hukunci karkashin dokar fararen hula da soja kamar yadda yake a sashi na 114 na dokar soja, za su kuma iya fuskantar hukunci a kotun soja saboda hana jami’in gwamnati gudanar da aikinsa,” a cewarsa.
Yusuf ya kara da cewa a wannan yanayi ministan bai yi komai akan ka’ida ba, kasancewar aikinsa bai samu goyon bayan doka ba, domin babu wani umarni ko oda daga kotu da ta bashi dama.
A Karshe
A takaice sojan Najeriya bashi da dama ya shiga harkoki na farar hula kamar batun rikicin filaye ko batu na rusau.
Shigar soja irin wannan lamari na da iyaka, sai a yanayi da mahukunta kamar shugaban kasa ya ba da umarni, shima bisa sahalewar doka, farar hula sune da alhaki a wannan yanayi su tabbatar da ganin an aiwatar da umarni ba soja ba.




