|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Manaja a harkokin gudanar da bincike ta fasahar zamani a Cibiyar Fasahar Kirkire-kirkire da Sharhi kan Bayanai da ake yada wa barkatai (DAIDAC) Silas Jonathan, ya bayyana cewa kungiyoyin ‘yanta’adda na amfani sosai da bayanan karya da ake yadawa da gangan don su yada manufarsu a yankin Tafkin Chadi me fama da rikici.
Ya bayyana haka ne a makalar da ya gabatar a lokacin da yake bayani ga ‘yanjarida lokacin taron ‘yanjarida masu samun horo kan gudanar da bincike a aikin jarida na kwanaki uku, (AIJC2024) wanda aka yi tsakanin 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, 2024 a birnin Johannesburg na Afurka ta Kudu.
Yayin da yake bayani kan manufar “Yaki da ‘yanta’adda a yankin Sahel”ya bayyana muhimmanci da ke akwai na tuntubar al’umma wajen tattara bayanai da ake yawan tattaunawa a rikicin. “Duk lokacin da irin wannan tattaunawa ta taso, ba kawai tunanin ba, ku yi tunani ya za ta kasance idan kuka samu kanku a yanki da ake fama da rikice-rikice.”a cewarsa.
A matsayinsa na mai bincike a aikin jarida mai kuma nazari, Mista Jonathan ya mayar da hankali kan yadda bayanai suke taka rawa a rikicin yankin na Tafkin Chadi.
Yace, “daya daga cikin abubuwa da na gano shine ribatar tattalin arziki daga rikici da ma ba wa rikicin fifiko.’
Yace bangaren gwamnati da masu tada kayar baya na samun riba daga wannan rikici inda ya ba da misali da yadda dakarun soja ke hada rikici don samun abin duniya ko kudade a wajensu.
”Akwai kuma karin samun mutane da ke hijira yayin da mutane ke neman rayuwa mai inganci.” a cewarsa. Yace wannan ya zama silar tattalin arziki ya karkata ga masu fataucin mutane.”
Har ila yau ya sake haskaka raunin mulkin dimukuradiya a yankin na Sahel, abin da ya kara ta’azzara rashin zaman lafiya.
“A tarihance, dimukuradiyya ana sa mata ayar tambaya kan ingancinta wajen yakar ta’addanci.” a cewar Jonathan.
Ya kuma nuna yadda ‘yankasashen waje suka kara ta’azzara tashin hankalin da ke faruwa, musamman daga kungiyoyi kamar na kasar Rasha Wagner Group, wadanda suka kara dagula lamarin.
A bincikensa kan bayanan da ake yadawa barkatai wadanda ba haka suke ba, Jonathan yace bayanai na da tasiri ne wanda ke karuwa idan ana yada labaran karya ga al’umma. Wadanda ke tafiya kafada da kafada kamar yadda tarihi ya nuna a yakin basasar Rwanda da farfaganda ta ‘yanNazi, ya kuma yi bayani kan yadda masu tsatstsauran ra’ayi ke amfani da kafafan sada zumunta wajen daukar sabbin mambobi.
“A shafin Facebook da TikTok akwai shafukan da kungiyoyin na masu tsatstsauran ra’ayi ke kula da su inda suke wa mabiyan albishir na samun kyakykyawar rayuwa a agare su muddin suka mika wuya. ”A cewarsa.
Ya kara da cewa akwai nazari ko bincike da dama fiye ma da na cibiyarsa wadanda suka tabbatar da cewa labaran karya kan haddasa shigar al’umma masu rauni cikin rudani.
Mista Jonathan ya kuma tattauna batun yanayi na al’umma da suka fi amfani da shafukan na sada zumunta inda yace ‘yanta’addar na amfani da wannan dama ma su sake mamaya. “Mutane sun fi so su rika baza labarai da ke sanya tsoro a zukatan al’umma.”
Ya bayyana cewa al’umma su kan shiga yanayi na rashin karsashi ko kwarin gwiwa yayin da suka ji karar bindiga ko aka watsa wani labari mai firgitarwa a shafukan sada zumunta.
Ya kara da cewa safarar mutane wani babban lamari ne, idan ana maganar wannan rikici. Jonathan ya ba da labarin yadda wani dan Najeriya ya dena jin duriyar dan’uwansa tsawon shekaru shida tun bayan da ya kudiri aniyar zuwa Turai don neman rayuwa mai inganci.
Yace “Ko da yake wannan labarin na wani mutum ne daya, amma ya bayyana yadda za a iya samun labaran wasu da ke zama cikin rudani a kokari na ficewa daga yankin.”
Mista Jonathan yayi kira ga ‘yanjarida su yaki labaran karya, su kuma sa ido da bibiyar irin wadannan labarai.
Yace “Wannan rikici na sauyawa daga wanda ake gani a zahiri zuwa wanda ake a shafukan intanet na zamani.”A nan sai yayi gargadi da ma kira ga ‘yanjarida su sake duba sabbin hanyoyi na samar da waraka ga wannan kalubale.
Ya kuma sake nuni da cewa a zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan a Najeriya, an ga yadda wasu masu zanga-zangar suka rika daga tutar kasar Rasha, kana suna kira da cewa sojoji su zo su karbi mulkin Najeriya, wadannan alamu ne na kira ko jawo masu mulkin kama karya.
A karshe Mista Jonathan yace “Talauci shine babban sanadi da ke kara zafin rikici a yankin Sahel.” Sai ya jaddada bukatar da ke akwai ta kawar da talauci a yankin.




