Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyon da ke nuna dalubai a Ilori suna zanga-zanga a gaban fadar sarki.
Sakamakon bincike: Bincikenmu ya tabbatar mana cewa wannan bidiyon tsoho ne kuma ana sake yada shi ne a sunan sabo. Dan haka wannan da’awar yaudara ce kawai.
Cikakken bayani
Kwanan nan, Najeirya ta fuskanci zanga-zanga masu yawan gaske dangane da kuncin rayuwa. Yayin da farashin rayuwa ke cigaba da karuwa, wani bidiyo na nan na yawo a soshiyal mediya. A cewar wasu masu amfani da shafin Facebook, an yi zargin cewa an dauki bidiyon ne a gaban fadar sarkin Ilori inda matasa suka gudanar da waya zanga-zanga ranar 16 ga watan Fabrairu.
A bidiyon mai tsawon minti 27, an ga matasa da yawa suna raira kasidu suna cewa “Ebi ń pàlú, ” abun da ke nufin cewa “al’umma na cikin yunwa.” Wannan bidiyon yanzu ya yadu sosai da shafukan WhasApp, da Facebook, ya na dauke da taken cewa “Labari da dumi-duminsa: Yunwa: Rahotanni sun ce sarkin Ilori ya tsere daga fadarsa yayin da ‘yan Najeriya suka yi kakagida a fadar suna neman abinci.
Yanzu bidiyon ya bulla a dandaloli daban-daban har da, nan, nan, nan, nan, nan da nan. DUBAWA ta tantance wannan labarin ne saboda yawan martanonin da ya janyo da ma yadda ya yadu.
Tantancewa
DUBAWA ta fara lura da cewa wannan bidiyon ne kadai irinsa da ke bayani kan wannan batun. Mun gudanar da bincike mai zurfi mu ga ko zamu ga wani bidiyon da aka dauka dangane da batun amma daga wani wuri na daban amma ba mu gani ba. Daga nan sai muka dauki hoton bidiyon muka duba mu gani ko lallai fadan sarkin ilorin ne kamar yadda aka san ci. A nan bincikenmu ya nuna cewa lallai fadar ce.
Bayan nan sai muka fara binciken mahimman kalmomi a shafin Facebook, wanda ya cigaba da kai mu kan wannan bidiyon wanda ya ke shafukan intanet tun watan Mayun 2021. Wanda kuma wani mai amfani da shafin facebook ne Rufai Solomon, ya wallafa ya na cewa : Mutanen Ilori sun tafi fadar sarkin Ilori a dubbansu suna nuna adawa da matsalar yunwar da suke fama da shi a kasar.
Wani abun da ya sake goyon bayan bincikenmu kuma shi ne shi kansa sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari ya yi watsi da bidiyon ya ce tsoho ne. A wata sanarwar da aka bai wa ‘yan jarida ranar 18 ga watan Fabrairun 2024, ya ce abun da ya kai ga zanga-zangar da ake gani a wannan bidiyon ya faru ne a gabannin zabukan da aka yi a shekarar 2019.
Ga kadan daga cikin sanarwar:
“Muna so mu bayyana da babbar murya cewa abin da ke cikin bidiyon nan abubuwa ne da suka faru a gabannin zaben gama gari na shekarar 2019. Bidiyon ba shi da alaka da abubuwan da ke faruwa yanzu. Idan ba ku manta ba, a duk lokutan da aka taba shuga yanayi irin wannan, sarkin ya kan bayyana damuwarsa dangane da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’umma.”
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyon tsoho ne wanda ake kokarin a nuna cewa bai dade da faeuwa ba. Dan haka wannan da’awar yaudara ce kawai.