Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin zuwa su dangwala yatsunsu a takardun zabe, shawarar da za su yanke zai yi tasiri kan abubuwan da suka shafi tattalin arziki irin su hauhawar farashin kayayyaki, wadatar kudi, rashin aikin yi, tsaro da cin hanci, duk daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen auna yanyin cigaban dan adam.
Saye sa sayarda kuri’u ya zama dodon da ke cigaba da addabar tsarin zabukan Najeriya.
Babu shakka, sakamakon cinikin kuri’un na da da yawa amma’yan kasa na cigaba da shi wa kudi dan kalilan kamar yadda aka gani a zabukan da aka yi a baya. Lokacin da aka yi zabukan baya-bayan nan a Najeriya, akwai rahotannin da suka yi zargin cewa wasu sun sayar da kuri’un su kan farashin da ke tsakanin N4,000 da N10,000.
Wannan ko kusa bai kai yawan kudin da ‘yan takara suka kashe wajen sayen kuri’u lokacin zaben fid da gwani a jam’iyyunsu ba.
Mene ne sayen kuri’u?
Sayen kuri’u yawanci ana mi shi kallon ciniki ne na tattalin arziki inda mai kuri’a zai sayar da kuri’arsa ga wanda ya taya da tsada. Cibiyar Kasa da Kasa ta Shawara kan Taimakwa Zabuka a Dimokiradiyya ta ce sayen kuri’u ya sabawa dokokin zabe, amma kuma yana faruwa a kasashe da yawa, abun da ke rage darajar zabuka kuma yana lahani ga gwamnatin dimokiradiyya.
Me ya sa ‘yan kasa ke sayar da kuri’unsu?
Yawancin lokuta idan ana tattauna batun sayen kuri’u, ana yawan son sanin dalilin da ya sa mutane ke sayar da kuri’unsu. Da aka tattauna da ‘yan Najeriya daga angarorin kasar daban-daban, mun gano cewa yanayin tattalin arzikin kasar na daya daga cikin manyan dalilan.
Misali ga Emmanuel Ikenna, wani dan kasuwa a babban birnin Najeriya wato Abuja, yawancin ‘yan Najeriya kan sayar da kuri’un su ne saboda mawuyacin halin da suke fuskanta, a cewarsa, akwai iyalan da ba za su iya cin abinci sau uku a gidajensu ba, shi ya komin kankantar kudin da aka ce za’a basu a madadin kuri’unsu ba wuya sun yarda.
A daya hannun kuma, Nuel Samson wani mazaunin Abuja shi ma, ya dore laifin ne a kan ‘yan siyasa.
Ya yi bayanin cewa “‘Yan siyasa sun riga sun mayar da talauci makami wanda su ke amfani da shi a lokacin zabe don su gudanar da yakin neman zabe yadda su ke so. Wannan ne ke hana talaka samun wani zabi idan ba sayar da kuri’un ba.”
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) Mahmud Yakubu, a wani rahoto shi kan sa ya danganta sayar da kuri’un da talauci.
Wani hukunci ne ke tattare da cinikin kuri’u?
Bisa tanadin Dokar Zabe karbar kudi ko wani kyauta dan a yi zabe ko kuma ma kin zuwa a jefa kuri’a lokacin zabe babban laifin zabe ne. Akwai hukunci wa masu sayar da kuri’u (Idan aka kama ka) za’a ci ka taran N500,000 ko kuma a kulle ka na tsawon watanni 12. Ko kuma abubuwa biyun a tare.
9. Sanarwa ko wallafa sakamkon zabe na karya
Laifuka | Hukunci | Idan aka samo |
Jami’in zabe ko mai irga kuri’u ko ku wanda ya kai takardar shaida ta karya | Shekaru uku a kurkuku ko kuma biyan tara. |
10. Cin hanci ko hada baki a sayi kuri’u
Laifuka | Hukunci | Inda za’a sami hujja |
Biyan wani kudi a sunan cin hanci lokacin zabe | Idan har aka sami mutumin da laifi zai biya tarar N500,000 ko kuma ya shafe watanni 12 a gidan yari | Sashi na 124 E.A 2010 |
Karbar kudi ko kyauta daga wajen wani dan zabe ko kuma ma kin yin zaben baki daya a ranar zabe | Idan har aka sami mutumin da laifi zai biya tarar N500,000 ko kuma ya shafe watanni 12 a gidan yari ko kuma duka biyun |
Ta yaya za’a iya dakatar da sayen kuri’un lokacin zabe?
Domin dakile wannan matsalar da ya ki ci ya ki cinyewa a tsarin zabukan dimokiradiya a kasashen duniya baki daya, babu wata hanya mai sauki.
Jide Ojo, wani mai bayar da shawara dangane da cigaba kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullun ya ce gurfanar da masu laifi a gaban kuliya zai taimaka wajen rage afkuwar lamarin. Ya kuma yi kira ga hukumomin da suka dace da su yi yaki da batun a boye ba lallai yadda aka saba ba.
Ya kuma yi kira ga majalisar dokoki da ta hanzanrta daukar matakan da za su taimaka wajen zartar da kudurin dokar laifukan zabe wanda zai taimaka wajen shawo kan wannan kalubalen.
Mukhtar Imam, masanin tattalin arziki na siyasa ya ce saye da sayar da kuri’u abu ne da ya shafi da’a da hali a Najeriya. Ya kuma kara da cewa rashin da’a da kishin kasa su ne ke kara rura wutar abubuwa irin haka.
Idan har ana so a kawo karshen wannan matsalar na sayar da kuri’u dole sai an kawar da rashin daidaito a tsarin albashi, da ma wajen rabon arzikin kasa, a kuma rufe gibin da ke tsakanin masu shi da marasa shi.
Imam ya ce sabbin dabaru na fasaha kamar su BVA za su taimka duk da cewa ba kai tsaye ba, za su dai taimaka wajen dakile matsalar tun daga tushe.
A Karshe
A ‘yan kwanaki masu zuwa, za a sami sakamakon zaben 2023 wanda zai share fagen irin cigaban da za’a samu a fuskokin tattalin arziki da zamantakewar kasa. Saye da sayar da kuri’u kamar an sayar da makoma ne saboda kudi dan kalilan wanda kuma yawancin lokuta ba dadewa suke yi ba.