African LanguagesHausa

#Zaben 2023: Hakkokinku na ranar zabe a matsayin wadanda suka cancanci kada kuri’a

Hana sauyi kamar yadda ya faru a shekarun  2015  da  2019, mutane fiye da miliyan 84  suka yi rajistar jefa kuri’unsu domin zaben shugaban kasar Najeriya na 16 kuma na 6 a cikin wadanda aka zaba bisa turbar dimokiradiyya wanda za’a yi 25 ga watan Fabrairu.

A baya fitowa zabe ya kan kasance babban kalubale kuma ana yawan danganta wannan da yadda hakkokin masu zabe ke raguwa. Akwai binciken da Saheed Olasunkanmi ya yi dangane da “ilimantar da masu zabe da zabuka masu sahihanci a Najeriya: Batutuwa da Kalubalen babban zaben 2019” wanda ya nuna cewa akwai gibi sosai idan ya zo ga irin ilimin da ‘yan kasa ke da shi dangane da zabe sakamakon irin kutsen da mulkin sojoji ya yi a kasar. 

Domin kaucewa rashin yin zabe, ilimantar da jama’a kan tsarin zabe da samar da cibiyoyin zabe masu nagarta na da mahimmanci sosai wajen samun nasara a gudanar da zabe,musamman a yunkurin da Najeriya ke yi wanje inganta tsarin demokiradiyyarta.

Da kudurin dokar da aka zartar ranar 25 ga watan fabrairun 2022, akwai sauye-sauyen da suka shafi ‘yan takara, jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki wadanda har yanzu ba’a san su ba.

Wadanne hakkoki ne masu zabe ke da shi ranar zabe, kuma yaya za su kare su?

  1. Yancin kada kuri’a

Bisa tanadin kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara) duk wani dan kasa wanda ya cika duka sharudan da doka ta gindaya zai iya yin zabe kuma zai iya tsayawa takara,

Da katin zaben da ke nuna duka bayanan wanda ke rike da shi, wanda ya cancanci kada kuri’a na da ‘yancin yin zabe bayan an tantance ko shi wane ne kafin zaben ya fara

Wanda ke tsayawa takara ma tilas ne ya cika wadannan sharudan . Bayan an cika duk tanade-tanaden doka kafin ranar zabe, dan takara a inuwar jam’iyyar da ya ke takara na da ‘yancin yin zabe. 

  1. Zabin yin zabe cikin sirri

Masu jefa kuri’a na da ‘yancin yin haka cikin sirri. Kasancewar rumfunan zabe ma yana tabbatar da kariya ga masu zabe da kuma taimaka mu su wajen yin zabin su cikin sirri.

Idan aka shiga wani yanyi na tashin hankali ko kuma dai wata tarzoma, irin wadanda aka cika gani lokutan zabe a nahiyar Afirka, rumfunan zabe na tabbatar da kariya da tsaro ta wannan fannin. 

  1. ‘Yancin samun bayanai dangane da zaben

Lokacin zabe, wanda ya cancanci kada kuri’a na da ‘yancin yin tambayoyi dangane da abubuwan da bai fahimta ba ba tare da fargabar hukunci daga jami’an tsaro ko jami’an zabe ba. Tilas ne jami’an da ke wurin zabe su amsa tambayoyin da suka dangance tsarin yadda ake jefa kuri’ar.

Haka nan kuma duk wanda zai yi zabe yana da ‘yancin samun bayanai dangane da zaben ko bayan an kammala. Kudurin Dokar ‘Yancin Samun Bayanai, wanda ya zama doka a shekarar 2011, na bai wa duk wani wanda ya cancanci kada kuri’a ‘yacin tambaya da kuma samun bayanan da ke hannun mahukunta. Da kudaden jama’a ake zabe, shi ya sa wajibi a baiwa masu zabe duk wani bayanin da suke bukata.

  1. Sanya ido kan sakamakon zabe

Duk wanda ya yi zabe zai iya zaunawa ya jira har sai sadda za’a bayyana sakamakon zaben. Babu jami’in da ya isa ya kalubalanci masu hefa kuri’a har ma ya kore so daga rumfar zabe a lokacin, kafin, ko kuma lokacin da ake kidayar kuri’u ko ma bayan zaben.  

Masu zabe za su iya kidaya tare da wadanda ke yi dan a tabbatar an yi komai a bayyane. Haka nan kuma suna da ‘yancin su tambayi jami’an zabe idan sun ga wadansu abubuwan da ba su gane ba. Sai dai kuma babu mai zaben da ya isa ya tsoratar da jami’in zabe ko ma ya sa shi yin irin aikin da ba shi ne ba ne wajen kidayar kuri’un.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button