Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa (claims) cewa Gwamna Fubara ya ba da umarni na a rufe kamfanin mai na NNPCL da wasu kamfanonin mai a jihar Rivers saboda batun kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa jihar.

Hukunci: Karya ce. Fitattun kafafan yada labarai kamar Punch da Channels TV sun ba da rahoto inda suka nunar da cewa da’awar ba gaskiya ba ce inda ma suka rawaito yadda kwamishinan sadarwa da yada labarai a jihar Joseph Johnson, yayi fatali da da’awar da ya bayyana da cewa farfaganda ce.
Cikakken Sako
Tsamin dangantaka tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Babban Birnin Najeriya Nyesom Wike da wanda ya gaje shi Siminalayi Fubara, na ci gaba da ruruwa musamman duba da a baya-bayan nan Babbar Kotun Tarayya (recent Federal High Court’s order) ta hana Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da kudaden da Gwamnatin Tarayya ke tura wa jihar ta Rivers.
Ana tsaka da wannan dambarwa sai wani mai amfani da shafin Facebook Amb. Okorie Sylvester Chidubem ya wallafa zargin cewa gwamnan jihar ta Rivers Mista Fubara ya ba da umarni na a rufe kamfanin mai na kasa a Najeriyar NNPCL da wasu kamfanoni a jihar da ke a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
Mai amfani da shafin na Facebook yayi rubutu kamar haka “Labari da dumi-dumi: gwamnan jihar Rivers Sim Fubara ya rufe kamfanin NNPC da sauran kamfanonin mai a jihar ta Rivers, ya bayyana cewa idan babu kudin da ke zuwa jihar Rivers daga tarayya to babu mai ga Najeriya.”
“A wani yunkuri na daukar mataki mai tsauri, gwamnan jihar Rivers Sim Fubara ya ba da umarni na a rufe kamfanin NNPC da sauran kamfanonin hakar mai a jihar ta Rivers, inda ya bayyana cewa muddin babu kudi na jihar daga Gwamnatin Tarayya to babu mai ga Najeriya. Cikin ‘yan mintuna da rufewar Najeriya ta samu koma baya a jadawalin kasashe inda ta tashi daga mataki na 4 zuwa mataki na 24. A bayyane take Gwamna Fubara ya kalubalanci minista Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu don su dauki mataki kan wannan hali da ake ciki ko su zura ido Najeriya na tafasa.” a cewarsa.
Daga lokacin da aka wallafa wannan labari a ranar Alhamis 30 ga watan Oktoba, 2024 wannan wallafa ta samu mutane 23 da suka nuna sha’awa (Likes) da 22 masu sharhi (comments) da mutane biyar da suka sake yada labarin (shares).
Bayan nazartar irin sharhi da mutane ke yi kan wannan wallafa DUBAWA ta ga cewa masu amfani da Facebook na nuna goyon bayansu ga umarnin da ake zargin cewa gwamnan ne ya bayar da shi.
“Mataki mai kyau, mu je gaba,” a cewar Nelson Chibuike Iregbulem.
“Yayi kyau,” a cewar China Sommy. Shi kuwa Ebele Temple ya rubuta cewa , “Wike ya shiga rudanii.”
Mun kuma samun irin wannan da’awa anan ma (here.)
Duba da irin hadarin da wannan batu ka iya haifarwa da kara ta’azzara rudani na siyasa tsakanin wadannan gaggan ‘yansiyasa DUBAWA ta ga ya dace ta gudanar da bincike kan wannan da’awa.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a dangane da rufe kamfanin na NNPCL da aka ce Mista Fubara yayi, ga kuma karyata labarin daga bangaren gwamnatin ta Rivers kan wannan zargi.
Jaridar Punch ta ba da rahoto cewa kwamishinan yada labarai a jihar ta Rivers Joseph Johnson yayi watsi da zargin wanda ya bayyana da zama karya da kuma farfaganda.
“ An jawo hankalin gwamnati cewa a kwai labari mara tushe da ke yawo a shafukan sada zumunta akan Gwamna Siminalayi Fubara ya rufe kamfanin mai na kasa NNPCL da sauran kamfanoni da ke aikin hakar mai a jihar Rivers,”a cewar wani bangare na jawabin da aka raba wa manema labarai.
“ Labarin ba kawai karya ba ce, amma karya ce tsabarta da aka kirkira don farfaganda irin ta mai hada labarin kuma makiyin jihar, an kuma yada labarin a wasu kafofi wadanda ba muhimmai ba, da ba a tantance su ba,” a cewar karin haske da kwamishinan yayi.
Kafar yada labarai ta Channels ta rawaito bayanin da gwamnatin ta jihar Rivers ta yi a game da labarin inda ta bayyana da’awar da “tsararriyar farfaganda.”
Haka ita ma TheCable ta ba da rahoto da cewa martanin da bangaren gwamnati yayi kan da’awar karya ce. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauki labarin a matsayin na “karya.”
Har ila yau mai da’awar ya kara da zargin cewa bayan umarnin na gwamnan, matsayin da Najeriya take akai a duniya cikin kasashe masu fitar da mai ya sauka daga na 4 zuwa na 24. Sai dai bayanan mizanin kasashen a wannan fanni a duniya (Worldometer) ya nunar da cewa Najeriya na a matsayi na 15 wajen fitar da mai, haka kuma ita ce ta 37 wajen amfani da mai, sannan ta 10 a fagen yawan mai da take da shi a duniya.
A Karshe
Da’awar karya ce kamar yadda kafafan yada labarai suka nunar bisa kafa hujja da jawaban bangaren gwamnati, a nasu martani na cewa karya ce.