A mako na uku a cikin watan Maris,2026 rahotanni sun karade shafukan intanet cewa shafin Instagram zai dakatar da tsarin sadar da bayanai kai tsakanin masu tura sakonni da masu karbar sakonni wato end-to-end encryption (E2EE), nan da ranar 8 ga watan Mayu, 2026, abin da ke nuni da cewa kamfanin Meta zai iya sanin sakonni na masu amfani da shafin.
Wadannan rahotanni sun gamu da samun suka daga masu fafutkar kare sirrin al’umma dama samun rudani a cikin masu amfani da shafin wadanda basu da masaniya kan irin sarkakiya da wannan tsari ke da shi.
Wani mai amfani da shafin mai suna @tfunk.jams yace “me yasa haka?” shi kuwa @lunerwarrior2.0 yace “wannan na iya shafar sakonni da aka yi wadanda suka gabata ko sakonni da za su zo bayan an samar da wannan sauyi?” @realdritanlumani kuwa ya sanya alamar tambaya ne da cewa wannan sauyi ba haka kawai za a yi shi ba, akwai dai wata a kasa abin ba zai amfanar da mu ba, da bamu kariya ba,”
A shekarar 2016, shafin Facebook (da yanzu ake kira Meta) ya bijiro da wani tsari mai lakabin “tattaunawar siri” abin da ke sawa masu amfani da wannan tsari su gudanar da tattaunawarsu ba tare da sanin kowa ba da ake kira (end-to-end encryption) wanda ke sanyawa sakon ya tsaya tsakanin wanda ya aika da wanda ya karba kawai.
Sai dai wannan tsari mutane kadan ne suke amfani da shi yayin da a daya bangaren shekaru biyu kafin nan shafin WhatsApp na da tsarin sirrintawar na E2EE wanda ke killace bayanan ko tattaunawar masu amfani da shafin.
Bayan kusan shekaru 10 a shekarar 2023 Mark Zuckerberg ya bayyana cewa ya fitar da tsarin na sirrintawar na E2EE ga duk tattaunawar da aka yi ta sakon murya ko sako da kuma shiri na fadada aikinsa zuwa samar da wannan sako a Instagram, sai dai wannan tsari a Instagram baya fara aiki kai tsaye sai an yi amfani da waya ko kwamfuta a kunna shi, wannan tsari kuma ya takaita a wasu yankuna.
Sai dai a baya-bayan nan a sanarwa da ya fitar a sashin taimako Instagram ya nunar da cewa tsarin sirrintawar na (end-to-end encrypted) ba za a ci gaba da shi ba daga ranar 8 ga watan Mayu,2026.
Me ake nufi da sadar da bayanai kai tsaye tsakanin mai turawa da mai karba (End-to-end encryption)?
Sadar da bayanai kai tsaye tsakanin mai turawa da mai karba (End-to-end encryption) nau’i ne na tura sakonni cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba ciki kuwa har da kamfanin da ke aikin sadar da sakonnin ta hanyar amfani da wasu dabaru na fasaha kamar yadda IBM ya bayyana .
Ya kara da cewa E2EE ta sha banban da sauran hanyoyi na sadar da bayanai inda sakonni na bayyana ne kawai idan sakon ya isa wajen wanda aka turawa.
Har ila yau Instagram ya kara da cewa wadanda ke amfani da shafin wadanda wannan sauyi zai shafa za su ga sakonni kan yadda za su iya sauke wani sako ko wani hoto don ajiyewa idan suna muradin yin hakan.
Meta yayi bayani dalilin daukar matakin
Kafar yada labaran Guardian ta kafa hujja da bayanin mai magana da yawun Meta inda yace dalilin daukar matakin na Instagram saboda babu masu amfani da damar da yawa.
A cewar rahoton na Guardian yace “Mutane kadan ne suke amfani da tsarin na E2EE a tsarin tura sakonninsu don haka muka tsara mu cire tsarin a shafin na Instagram a watanni masu zuwa… Wadanda kuma suke da mradin ci gaba da tsarin suna iya ci gaba da amfani da shi a shafin WhatsApp.”
Wata matsaya ta daban
Wannan mataki na Meta dai ya gamu da martani kala daban-daban daga al’umma, wasu daga cikin masu fafutukar kare sirrin mutane sun yi suka kan matakin da wannan manhaja ko kafa ta dauka, wasu masana kan harkokin tsaro a intanet sun ba da shawara cewa masu tura sakonni su zama masu taka tsan-tsan kan sakonni da suke turawa mutane a kafofin sadarwar zamani, saboda babu tabbaci na sirrinta abubuwan da suke turawa.
Sai dai wasu na ganin matakin na Meta ba zai rasa nasaba da matsin lamba daga jami’an tsaro da gwamnatoci da masu kare hakkin yara ba, wadanda ke ganin wannan tsari zai ba da damar cin zarafin yara da wasu nau’ikan huldodi da ake yi a shafukan intanet.
Me ya kamata masu amfani da shafin su yi don kare kansu?
Masu amfani da shafin na iya sauke bayanan da suke bukata daga sashin tura sakonni ko (messenger) wadanda suke son amfani da su anan gaba kafin cikar wa’adin lokacin da kamfanin ya bayar. Wadanda suke da sha’awar yin hakan sai su sauke sabon Instagram wanda ke da sabbin damar fitar da sakonni da suke so.
Wasu kwararrun sun ba da shawara cewa masu amfani da shafin su dena yadawa ko su dakatar da yada bayanai ta sashin tura sakonni na Instagram musamman abin da ya shafi sirrinsu, shi kansa shafin na Meta ya bukaci masu amfani da manhajar su bukaci mutane su rika musayar sakonni ta kafar da ke ba da kariya ga bayanansu ta hanyar ta ( end-to-end encryption,) kamar ta manhajar WhatsApp.