Site icon Dubawa

Alkalin da aka yi garkuwa da shi a Katsina a 2021 ne ba 2026 ba

Katsina judge’s abduction from 2021, not 2026
,

Da’awa: Wani shafin Facebook mai suna Agbama Dynasty, ya yada wani  bidiyo inda yayi da’awar cewa ‘yan fashin daji sun kama wani alkalin kotun Shari’a yana tsaka da sauraren shari’a a kauyen Bauren Zakat da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

Alkalin da aka yi garkuwa da shi a Katsina a 2021 ne ba 2026 ba

Hukunci: YAUDARA CE. Tabbas akwai wannan bidiyo amma lamarin ya faru ne a watan Mayu,2021 ba a baya-bayan nan lamarin ya faru ba.

Cikakken Sako

A ranar Juma’a 31 ga watan Yuli,2026 shafin Facebook mai suna Agbama Dynasty, ya yada bidiyo mai taken “ ‘Yanta’adda sun aiwatar da dokar ta’addanci kan alkalin kotun Shari’a da ke kauyen Bauren zakat da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina…”

Duk da cewa taken labarin da aka rubuta akwai bukatar karin haske, mai jawabi a bidiyon ya bayyana cewa alkali Samaila Husseini, na kotun Shari’a ta kauyen Bauren Zakat ya fada komar ‘yanta’adda yana tsaka da gudanar da shari’a a wannan kauye da ke karamar hukumar Safana Katsina.

“Oga, wannan harkar fim har yanzu bata kare ba a Najeriya, wani alkalin kotun Shari’a Sama’ila Hussein da ke shari’a a kauyen Bauren Zakat a karamar hukumar Safana a jihar Katsina ‘yanfashin daji sun shirya yin irintasu shari’a ta ‘yanta’adda a kansa, bayan da suka kutsa kai cikin kotun da yake suka yi awon gaba da shi don zuwa cikin daji su aiwatar da dokarsu ta ta’addanci akansa.

Oga, dakatar da shari’ar da kake yi:; muna so mu yi dokar ‘yanfashin daji akanka. Wannan lamari fa ya taba kowa a Najeriya, ‘yan Najeriya a ina ne za mu tsaya ne?” a cewar mai bayanin.

Ya zuwa ranar Litinin 3 ga watan Agusta,2026, wannan wallafa kamar yadda aka (alkinta a nan ) ta samu martanai 5,000 da tsokaci 141 da wadanda suka sake yadawa 522 da mutane 160 da suka nuna alama ta cewa za su sake komawa don kallon wallafar.

Da dama cikin masu tsokaci sun amince da wannan da’awa inda suke nuna murnarsu wasu na cewa Arewa ita ce kanwa uwar gami wajen samar da ayyukan masu fashin daji. 

Jacob Moses ya rubuta cewa “Da kyau, wannan ita ce Najeriya.”

Ajirngee Charles yace, “Yayi kyau, sune suka jawo duk wannan matsala.”

Raphael Part ya bayyana cewa “Labari mai dadi a ko da yaushe, yayin da  Nkechi Jerry ta yi tsokaci da cewa “Yayi kyau matuka.”

Ganin yawaitar martanin da irin tsokacin da ake yi hakan ya sanya DUBAWA ganin cewa ya dace a gudanmar da bincike kan wannan bidiyo.

Tantancewa

DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta duba don gano ko akwai wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi wannan rahoto amma babu ko guda daya da aka gani ta yi wannan labari.

Maimakon haka sai binciken ya gano cewa a ranar 30 ga watan Yuli,2026 akwai rahoto cewa ‘yanfashin daji sun kai hari wata kotun shari’ar ta daban a Gwarjo, karamar hukumar Matazu a jihar  Katsina. 

A cewar  rahotannin, alkalin kotu Mohammed Mukhtar, ya tsere inda ya fita ta taga lokaci kalilan gabanin ‘yanta’addar su shiga yankin kotun. Rahotannin sun nunar da cewa ‘yanbindigar sun harba bindiga a karo da dama a lokacin da suke binciken gano shi, sannan suka yi barazanar cewa za su sake dawowa bayan gaza nasarar kama shi. Babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto da ya nuna cewa an kama alkali ko an kashe shi.

Wannan lamari an ba da rahotonsa a kafafan yada labarai da dama kamar Daily Trust da The Guardian da Leadership News da Tribune da sauransu.

Tun da  babu wani rahoto da ya yi daidai da da’awar da aka yi a shafin na Facebook DUBAWA ta kuma zurfafawa a bincike ta hanyar duba wurare dama da bayanan da aka yi a bidiyon.

Binciken ya kai mu ga lamarin da ya faru shekaru biyar da suka gabata, a ranar 18 ga watan Mayu,2021 kafar yada labaran  Peoples Gazette, ta ba da rahoto da ta ce ta gano a jaridar Daily Trust, ta ba da rahoto cewa ‘yanfashin daji sun kai farmaki kotun Shari’a ta Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina inda suka kama alkalin da ke shari’a a kotun Husaini Sama’ila, yana tsaka da zaman shari’a.

Rahotan ya bayyana hujjarsa da samun bayanai daga shedu cewa sun ga masu harin sun shiga yankin kotun sun kuma yi awon gaba da alkalin, bayanan da aka samu daga Facebook ya nuna matsalar tsaron da aka samu yayi daidai da na 2021 da aka yi garkuwa ba wai a baya-bayan nan ba da ake nuna matsalar tsaro a Katsina ba.

Duk da cewa garkuwar da aka yi ta faru sai dai wanda yayi walafar ya gaza ba da bayanan cewa lamarin ya faru ne a 2021, inda ya bar masu kallo na ganin cewa kamar lamarin ya faru ne a baya-bayan nan.

A karshe

Da’awar yaudara ce. Duk da cewa akwai alkalin kotun Shari’a da aka yi garkuwa da shi a Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, lamarin ya faru ne a watan Mayu,2021 ba wai a 2026 ba.

Rahoton kai farmaki a kotun Shari’a a Katsina, hari ne da aka kai wata kotu ta daban a karamar hukumar  Matazu inda kuma a nan alkalin kotun ya tsallake rijiya da baya ya tsere ba tare da samun wata illa ba.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai. 

Exit mobile version