Da’awa: Wasu hotunan da wani mai amfani Facebook sun nuna gawar da ke cikin akwati, tare da ikirarin cewa gawar tsohon shugaban kasa Buhari ce.

Hukunci: Yaudara ce. Hotunan da ke yawo ba daga dawowar gawar Buhari ba ne, an ɗauki hoton ne daga jana’izar Awujale na Ijebuland, wanda ya rasu a watan Yuli 2025.
Cikakken Bayani
A ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti a birnin London, kamar yadda fadar shugaban ƙasa da iyalansa suka tabbatar.
Yayin da ake jiran dawowa da gawarsa domin gudanar da jana’izarsa a gidansa da ke Daura, wasu hotuna suka fara yawo a kafafen sada zumunta.
Wasu daga cikinsu sun nuna wani babban akwatin gawa da akayi dafifi da manyan mutane ciki har da Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, da Aliko Dangote, ɗan kasuwa sananne da kuma wasu gwamnonin Najeriya.
An ɗora taken cewa “Gawar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ta Isa Jihar Katsina” Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da rikicewar fahimta a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, in da wasu ke cewa ba gawar shi ba ce wasu kuma na yi masa addu’a
Hotunan wanda wani Shafin Nigeria Post ya wallafa a ranar 15 ga Yuli, 2025, an yada shi sau 92 cikin sa’o’i biyar, yayin da aka yi sharhi akansa kusan 50.
Akan wannan ne DUBAWA ta yi bincike domin tabbatar da asalin wadannan hotunan da kuma inda suka fito.
Tantancewa
DUBAWA ta saka hotunan a cikin shafin nema na Goodle wanda ya nuna cewa ba gawar Buhari ce ba.
Binciken da DUBAWA ta yi ya nuna cewa hoton an ɗauke shi ne a birnin Ijebu Ode, Jihar Ogun, yayin da ake gudanar da jana’izar Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Adetona.
An wallafa hoton a shafin Instagram na gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo Olu (@jidesanwoolu) da kuma shafukan jaridu da dama, inda suka bayyana a fili cewa wannan hoto daga jana’izar Awujale ne.
Hakama, hotunan da ake yadawa ba su nuna alamar filin jirgin saman jihar Katsina ba, wanda aka tabbatar cewa a can ne Buhari ya sauka. A maimakon haka, hoton yana nuna masallachi da gine-gine da alamomin da ba na filin jirgin ba.
A halin da ake ciki, sanarwar fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu ne ya karɓi gawar Buhari a Katsina, kuma tuni aka binne shi.
A Karshe
Hotunan da ake yadawa cewa yana nuna zuwan gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga London zuwa Najeriya, an ɗauke su ne daga jana’izar Awujale na Ijebuland, kuma babu Shugaba Tinubu a cikin hoton.