Da’awa: Mai amfani da shafin X (@Comrdebarde) ya wallafa bidiyon da ke da’awar wai ‘yan ta’adda sun kakkabo daya daga cikin jiragen sojojin saman Najeriya wato NAF suna amfani da bindiga kirar AK-47 a Zungeru da ke jihar Neja.

Hukunci: Babu isasshen hujja. Babu hujjar da ta nuna mana cewa ‘yan ta’adda sun kakkabo wani jirgi na NAF
Ciakken bayani
Mai amfani da shafin X, @Comrdebarde, ranar 12 ga watan Yunin 2026, ya yi da’awa cikin wani bidiyo (ana iya ganin shi a nan) ‘yan ta’adda sun kakkabi wani jirgi mai saukar unguka ta NAF a Zungeru da ke jihar Neja da bindigogi kirar AK 49.
“… ‘yan ta’adda syn dauki bidiyo sun tura na jirgi da sojojin da suka kashe a Zungerun Neja. Sun ce bindiga kirar AK 47 suka yi amfani da shi wajen harbo jirgin,” wani bangare na labarin ya bayyana a shafin X.
Domin mai da’awar bai bayyana rana ko kwanan watan da abin ya faru ba, wani shi ma mai amfani da shafin, @_VatEra, ya yi tambaya cikin sashen tsokaci ko kwament, inda ya bukaci sanin ko kwanan nan ne wannan lamarin ya afku.
“Kwanan nan ne?” @_VatEra ya tambaya. Mai da’awar @Comrdebarde kuma ya amsa ya ce eh.
Bidiyon ya nuna jirgi mai saukar ungulun da ya lalace tare da wasu gawawwaki. Haka nan kuma akwai wasu mutanen da suka yi dammara kewaye da gawawwakin suna ihun “Allahu Akbar”
Daga 15 ga watan Yunin 2026, mutane samda da 5756 sun kalli bidiyon, akwai alamar like 59, mutane 11 sun kai karar shafin yayin da wasu 39 kuma suka adana bayanin.;
Ga wasu daga cikin martanonin da masu amfani da shafin suka bayar dangane da batun.
@Omarparouq, cewa ya yi, “Haka za mu cigaba?”
Wani kuma, @ OfficialKAMALA, ya yi bayani kamar haka, Wannan sojoji ne, suna so bi sahunsu ne ko.”
Bisa la’akari da irin wannan da’awar da tasirin da zai iya yi a kan yadda al’umma ta ke kallon tanadin da ake wa tsaro da ma irin yunkurin da gwamnati ne ya sa DUBAWA gudanar da bincike kan sahihancin wannan batun.
Tantancewa
Mun fara tantance bidiyon da manhajar InVIl. WMun cire mahimman hotuna daga bidiyon muka yi amfani da su cikin manhajar tantance hotuna.
Wannan binciken ne ya kai mu ga wani rahoton da PR Nigeria ta wallahi ranar 20 ga watan Agustan 2023 mai taken “NAF Helicopter Crash, Terrorists’ Propaganda and Military Sacrifice.” Wanda a hausa ke nufin faduwar jirgi mai saukar ungulun NAF ‘Yan ta’adda, farfaganda da sadaukar da kan da sojoji ke yi.
Rahoton na daukeda wannan hoton a matsayin hatsarin jirgin da suke nufi.
Jaridun Cable da Punch su ma sun dauki labarin ranar 14 ga watan Agustan 2023,
Rahoton PR Nigeria ya yi bayani dalla dalla ranar 14 ga watan Agusta, inda ya ce jirgi mai saukar Ungulu na NAF mai lamba MI-171E ya fadi a kauyen Chukuba da ke karamara hukumar Shiroro a jihar Neja
Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama (NAF), Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da hatsarin na shekar 2023 cikin wata sanarwar da ta gabatar a hukumance.
Yayin da wasu mazauna garin suka fadawa wa kafar yada labaran AP News cewa ‘yan bindiga ne suka kakkabo jirgin, mahukuntan NAF sun ce ana kan gudanar da bincike kan abin da ya yi sanadin faduwar jirgin.
Rahotannin da aka bayyana a sama da sanarwar da suka bayar a hukumace duk sun nuna cewa hatsarin da ya afku a 2023 ya faru ne a kauyen Chukuba da ke karamar hukumar Shiroro na Zungeru ba kamar yadda ake da’awa.
Cikin wata hira ta daban da aka yi da Arise News, Air Vice Marshal Gbolahan Adekunle mai ritayi ya yi watsi da da’awar cewa bindigar AK 47 za ta iya saukar da jirgin mai lamba MI-171E, abun da ya kwatanta da walakin goro a miya.
Mun sake gano wani rahoton shi ma na jirgi irin na NAF a jihar Nejar wanda ya shafi wani karamin jirgi irin wanda aka sani da Alpha Jet da turanci. Wannan hatsarin shi kuma ya afku ne a kusa da Karabonde wanda ke karamar Borgu ranar 6 ga watan Disemban 2025, bayan da aka sami matsala ta gaggawa a cikin jirgin. Sai dai an yi sa’a matukan jirgin biyu duk sun fita lami lafiya ba tare da yin wani rauni ba.

Hoton faduwar jirgin Alpha jet a shekarar 2025. Asalin hoton: Babban shafin NAF.
Haka nan kuma, rahoton the Cable ya ambato Ehimen Ejodame, darektan sashen kula da hulda da jama’a na NAF ya ne cewa hatsarin ya afku ne bayan da ake wani gwaji na matakan gaggawan da aka tanadar a karshen wani bincike na musamman da suka yi.
Ita kanta NAF ta yi martani dangane da hatsarin cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta ranar bakwai ga watan Disemban 2025.
Mun gudanar da bincike na mahimman kalmomi dan ganin ko kwanan nan ne abin ya faru amma ba mu ga wani labari mai kama da wannan ba.
A Karshe
Hujjojin da muka samu sun nuna cewa hadarurrukan sun faru ne tsakanin shekarun 2023 da 2025, ba a shekarar 2026 ba.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.