Site icon Dubawa

Babu shaidar da ta nuna cewa wani yaro na da hannu a kama Janar Rabe

No evidence links boy in viral picture to General Rabe’s abduction

Manjo Janar Rabe Abubakar (rtd). Asalin hoto: PRNigeria.

,

Da’awa: Wani shafin Facebook, Spynigeria.NG ya yada labari inda ya nuna wani hoton karamin yaro bisa zargin cewa yana da hannu a kama Manjo Janar Rabe tare da matarsa a jihar Katsina. 

Babu shaidar da ta nuna cewa wani yaro na da hannu a kama Janar Rabe

Hukunci: Babu isassun shedu! Duk da cewa a kafafan sada zumunta da dama an yada labarin da alakanta yaron, babu wata kafar yada labarai sahihiya ko majiyar soja da ta tabbatar da hakan. 

    Cikakken Labari

    Wani shafin Facebook, mai suna Spynigeria.NG a baya-bayan nan ya yada wani labari kamar yadda yake(nan) dauke da hoton wani karamin yaro, a labarin an nunar da cewa shi wannan karamin yaron na da hannu a kama Janar Rabe mai ritaya da matarsa.

    Wannan da’awa ta yadu a daidai lokacin da ake tsaka da batun kama tsohon babban jami’in soja tare da matarsa a jihar Katsina.

    Wannan wallafa ta samu martani da dama daga masu amfani kafafan sada zumunta na zamani, da dama daga cikinsu alamu sun nuna cewa sun yarda da abin da ake fada.

    Ga misali wannan da ke amfani da kafar mai suna Tyokase Raphael yace “dan karamin danta’adda da kama tsohon babban sojan Najeriya da matarsa?’’ Shi kuwa  Dangana Musa Sauta ya rubuta cewa “Idan yana dauke da bindiga kai baka dauke da komai dolenka ka mika wuya.” 

    Wannan ya nuna irin yadda aka rika mayar da martani kan abin da ake magana a kai gaskiya ne.

    Duba da cewa wannan da’awa aba ce da za a yi taka tsan-tsan akanta ga kuma kalubalen tsaro da ake ciki da kuma barazanar da ke tattare da matsalar, hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin gudanar da bincike a kan wannan da’awa.

    Tantancewa

    DUBAWA ta gano cewa Janar Rabe mai ritaya da matarsa an kama su ne akan hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli a karamar hukumar Matazu a jihar Katsina kusa da kauyen Zakin Baure.

    Kafafan yada labaran Premium Times da DailyTrust da PUNCH duka sun ba da rahoto kan hakan.

    Daga bisani bidiyo daban-daban da aka rika fitarwa sun nuna janar din mai ritaya da matarsa a hannun masu garkuwa da mutane, inda suke kira da a kawo masu dauki, masu garkuwar sun bijiro da bukatar ganin an sako masu ‘yanuwansu tare da dabbobinsu da suke zargin an kwace daga gare su.

    A cewar jaridar PUNCH masu garkuwa da mutanen sun bukaci ganin an sako wasu mutane guda uku Sani da Aminu da Nasiru, tare da wasu dabbobi.

    A rahotanni da Daily Trust ta fitar ta bayyana wani gagarumin danta’adda  Kachalla Muhammad da cewa yana da hannu, inda ta nuna cewa jagoran ‘yanta’addar ya fara tattaunawa da iyalan mutanen da aka kama.

    Akwai ma wani sakon murya da aka rika yadawa a shafin Facebook ANN Politics,a cikin muryar da aka nada an bayyana cewa mai maganar shine Muhammadu Kachalla,wanda ke tattaunawa kan dalilin kama mutanen da batu kudin fansa tare da kira a sako masu ‘yanuwansu da dabbobinsu.

    Gwamnatin jihar ta Katsina ta tabbatar da batun tattara bayanan tsaro na jami’ai kuma sun tabbatar da cewa an tsara ne aka kama wadanda aka yi garkuwar da su.

    Duk da cewa an samu kafafan yada labarai da suka yi labarin, DUBAWA bata samu wani rahoto ba daga jami’an tsaro ko gwamnati ko kafar yada labarai sahihiya wacce ta nuna cewa yaron da ake nunawa a Facebook na cikin wadanda suka kitsa yin garkuwa da janar din na soja mai ritaya.

    Mun kuma tuntubi babban jami’i mai kula da harkokin yada labarai a rundunar sojan ta Najeriya Manjo Janar Edward Onoja, don jin bayani game da wadanda suka tsara yin garkuwar sai dai bai ce komai ba.

    Domin kara nutsawa dai don gano shi wannan yaro ko waye shi a hoton da ake nunawa a Facebook, DUBAWA ta hanyar gano asalin hoto ta nazarci bidiyon da masu garkuwar suka saki bayan kama janar din mai ritaya da matarsa.

    DUBAWA ta gano cewa wani mai amfani da shafin Instagram , @temilolasobola ya yada wani bidiyo da ya nuna Janar din mai ritaya tare da matarsa suna neman gwamnati ta kawo masu dauki, bayan wannan ne sai kuma aka nuna hoton wannan yaro, bisa da’awar cewa yana daga cikin masu garkuwar har yake dora bidiyon a shafin TikTok.

    Haka shima wani shafin X wanda a baya ake kira Twitter @firstladyship, da aka fi sani da Nefertiti, ya yada hoton inda yayi zargin wannan yaro shi ya yada hoton bidiyon a shafin intanet.

    Wallafar ta kara da cewa ana alakanta gungun “yanta’addar a matsayi mabiya jagoran ‘yanta’addar nan Kachalla Muhammadu, wanda ke dabdalarsa a jihar ta Katsina da yankin Arewa maso Yammaci.

    Sakamako da aka samu daga hoton dai ya nunar da cewa ana alakanta hoton yaron da bidiyon da ake yadawa a shafukan intanet na kama tsohon janar din na soja mai ritaya da matarsa.

    Sai dai duk da haka babu wata sheda da ta nuna yaron ko ta tabbatar da cewa da hannunsa a garkuwa da janar din na soja mai ritaya. 

    Karshe

    Babu wata sheda da ta nunar da cewa yaron da aka gani a shafin Facebook da ya yadu kamar wutar daji da hannunsa a garkuwa da Janar Rabe da matarsa.

    Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai. 

    Exit mobile version