Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa alkaliyar da ta ayyana Shugaba ta bar gani bayan an yi masa tiyatar ido a Landan.

Hukunci: Karya ce. Hoton da aka wallafa da ikirarin na tsohuwar Babbar Alkalin Ghana, Mai Shari’a Gertrude Torkornoo ne, kuma babu wani alkali mai suna “Tsamma Abubakar” da ya kasance cikin alkalan da suka saurari karar zaben shugaban kasa na 2023.
Cikakken bayani
Wani shafin Facebook mai suna I News ya wallafa wani labari a ranar 3 ga Yuli, 2026, yana ikirarin cewa “Judge Tsamma Abubakar,” alkaliyar da ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, ta rasa ganinta bayan an yi mata tiyatar ido a wani asibiti na musamman da ke Landan.
A cewar labarin (an adana a nan), alkaliyar ta tafi kasashen waje domin a kula mata da lafiyar ido da aka bayyana a matsayin na yau da kullum, amma wasu matsaloli sun taso yayin aikin, wanda ake zargin ya sa ta makance gaba daya.
Wani bangare na labarin na cewa “Labari Da Dumi-Dumi: Alkalin nan mai suna Judge Tsamma Abubakar wadda ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, an ruwaito cewa ta makance a wani asibiti da ke Landan bayan an yi mata tiyatar ido.”
Zuwa ranar 4 ga Yuli, 2026, labarin ya samu martani sama da 4,800, sharhi 4,000, da kuma yaɗawa sama da 1,100.
Ikirarin ya kuma jawo martani daga masu amfani da shafukan sada zumunta.
Wani mai amfani da shafin Facebook, Emmanuel Succeed Ademu, ya bayyana ra’ayinsa da cewa, “wannan shi ne cikakken ma’anar cewa azzalumai ba za su tafi ba tare da hukunci ba.”
Ita kuwa Gloria Ntiyak Jatau cikin nuna tausayi ta ce, “Allah Ya sauwaka mata.”
An kuma makala liƙau da zai dauki masu karatu zuwa wani rahoto da shafin Igbotimes Magazine ya wallafa. DUBAWA ta taba yin bincike kan wannan shafi a baya saboda yada labaran da ba a tabbatar da su ba, ciki har da bayanan rarrabuwar kawuna da farfagandar kan kasar Rasha.
DUBAWA ta kuma gano irin wannan ikirari a Facebook, Instagram da X.
Saboda muhimmancin da ke tattare da ikirarin da kuma yadda ya jawo hankalin jama’a, DUBAWA ta binciki gaskiyarsa.
Tantancewa
DUBAWA ta fara yin binciken da manhajar Google reverse image kan hoton da aka wallafa tare da ikirarin.
Binciken ya gano cewa hoton na tsohuwar Babbar Alkalin Ghana, Mai Shari’a Gertrude Torkornoo ne.
DUBAWA ta kuma duba jerin alkalan da suka saurari karar zaben shugaban kasa na 2023 a Kotun Daukaka Kara da kuma Kotun Koli.
A Kotun Koli, kwamitin alkalan bakwai da suka saurari karar ya kunshi Masu shari’a Inyang Okoro, Adamu Jauro, Uwani Musa Abba Aji, Lawal Garba, I.N. Saulawa, Tijjani Abubakar, da Emmanuel Agim.

Hoton hadakar alkalan da suka saurari karar. Mallakar Hoto: Vanguard.
Haka kuma, rahoton gidan talabijin na Channels ya nuna cewa alkalan Kotun Daukaka Kara da suka saurari karar sun hada da Mai Shari’a Haruna Tsammani, Mai Shari’a Stephen Adah, Mai Shari’a Misitura Bolaji-Yusuf, Mai Shari’a Boloukuoromo Ugoh, da Mai Shari’a Abba Mohammed.
DUBAWA ba ta ga wani alkali mai suna “Tsamma Abubakar” cikin dukkan alkalan da suka saurari karar zaben shugaban kasa na 2023 ba, ko a Kotun Daukaka Kara ko a Kotun Koli.
Bincikenmu ya nuna cewa akwai yiyuwar masu yada ikirarin sun karkatar da sunan Mai Shari’a Haruna Simon Tsammani, wanda ya jagoranci Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa ta 2023.
DUBAWA kuma ba ta samu wani sahihin rahoto, sanarwa daga hukuma, ko bayanin hukumar kula shari’a da ke tabbatar da cewa Mai Shari’a Tsammani ko wani daga cikin alkalan ya rasa ganinsa bayan tiyata a Landan ba.
A Ƙarshe
Ikirarin cewa alkalin da ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 ya rasa ganinsa bayan tiyata a Landan karya ce.