Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo da ke nuna ‘yanta’adda suna cewa ba su ke da alhaki na lalata Najeriya ba face ‘yansiyasa da ayyukansu na cin hanci da rashawa.

Tantancewa: Yaudara ce. Duk da cewa abin da mai amfani da shafin na Facebook ya yada hotunan na gaske ne da wurin da abin ya faru, DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da AI wajen sauya asalin abin da ‘yanfashin dajin ke fadi.
Cikakken Labarin
Ana tsaka da matsalar tsaro da farmakin ‘yanta’adda wani abu da ke zama sananne a shafin sada zumunta shine masu aikata laifukan kan yi amfani da hotuna da bidiyo su nuna wadanda suka yi garkuwa da su su nemi kudin fansa ko nuna wasu ayyuka da suke yi a cikin daji.
A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin Facebook @Obie Wiliam ya yada wani bidiyo, ‘yanta’adda suke sukar masu cewa sune suka lalata Najeriya. A wannan bidiyo kamar yadda aka (alkinta shi a nan), ’yanta’adda” sun yi da’awar cewa ‘yansiyasa masu aikata cin hanci da rashawa suke da alhaki wajen lalata kasa saboda satar dukiyar al’umma da lalata makomar kasa.
Abin da taken labarin ke cewa, “Yanzu haka kimanin yara miliyan 200 basa zuwa makaranta, ba wai saboda dalilin wata annoba ba, face saboda yadda wasu ‘yansiyasa suke kwashe kudaden al’umma da aka warewa fannin ilimi. Duka muna korafi wai ‘yanfashin daji, amma babu wanda ke kallon ‘yansiyasa masu cin hanci da rashawa.”
A wannan bidiyo mai tsawon dakika 15, ya nuna wani gungu na masu dauke da bindigu yayin da a bangare guda kuma ga wasu gungu na mata da yara da maza wadanda ke zaune a kasa.
Mutumin da ke dauke da bindiga na cewa, “Ya ku ‘yankasa ta Najeriya, kuna cewa ‘yanfashin daji sune silar lalalcewar Najeriya, tabbas, amma mantawa ake yi da ‘yansiyasa masu cin hanci da rashawa wadanda ke satar dukiyar kasa su Rusa makomar al’umma. Wata kila babu danfashin daji a cikinsu. Mutumin da ke jin yunwa sata yake ya ci abinci, shi kuwa dan siyasa sace makomar al’umma yake, ‘yanfashin daji basu da kyau amma ‘yansiyasa masu cin hanci da rashawa lamarinsu yafi muni.”
Ya zuwa ranar 14 ga Agusta,2026 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla sama da mutum miliyan biyar da masu nuna sha’awa 78,000 da sama da 8000 da suka sake yada bidiyon.
DUBAWA ta nazarci irin tsokaci da al’umma ke yi don gane Ina ne tunaninsu ya dosa a dangane da da’awar.
@Afolabi Adebayo yace, “Kuskure biyu ba za su taba ba da mafita ba.
@Mandela Kalu ya mayar da martani da cewa “Idan haka ne ku kaiwa ‘yansiyasa hari ba wadanda basu ji ba ba su gani ba.”
@Atawal Ayuba Mike yace yallabai danta’adda dama ka san ‘yansiyasa na sace mana dukiyar shine ka zo ka gallabe mu. Duk tafiyar taku iri daya ce.
Tabbas ‘yansiyasa sun sace makomar mu, amma ku ‘yanta’adda kun sace rayuwarmu ta yau.
Don haka idan bamu rayu ba a yau, wa ya damu da abin da zai faru a gobe?Don haka da danfashin daji da ‘yansiyasa duk abu guda ne.”
Mun kuma lura cewa wasu masu Amfani da shafin na Facebook sun yada wannan labari kamar a wadannan wurare; nan, da nan da nan.
Ganin yawan wadanda suka kalli wannan bidiyo ko tsokaci akansa abin da ya nuna cewa da dama sun aminta da abin da ake fadi. Hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin gudanar da bincike kan wannan da’awa da idan har ta tabbata za a yaudari al’umma mai tarin yawa.
Tantancewa
DUBAWA ta yi filla-filla da bidiyon ta hanyar amfani da manhajar InVID, don gano asalin bidiyon, bincikenmu ya kaimu ga wallafar Daily Trust, Inda ta nuna irin wannan bidiyo da irin wannan kamanni a shafinta na YouTube.
A cewar rahoton ‘yanbindigar sun saki mutane 40 da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
A cewar rahoton an sako mutanen ne bayan kudin fansa da aka biya, bayan tattaunawa da aka yi tsakanin ‘yanta’adda da wakilan al’umma.
A ci gaban rahoton ya nuna komai yanayin wajen da mai maganar a matsayin jagoran duk iri daya ne da bidiyon waccen wallafa.
A wannan bidiyo an ji mutumin na cewa “ Kamar yadda kuke gani wadannan mutane an sake su bayan cika alkawura, biyo bayan tattaunawa da muka yi aka kulla yarjejeniya ta zaman lafiya a yankin Faskari karamar hukumar a jihar Katsina, adadinsu 72.
Babu wanda yayi mana barazana ko ya fi karfinmu kafin sakin wadannan mutane, mun saki ne saboda alkawari da muka yi.”
Jagoran ‘yanta’addar ya ci gaba, inda ya zargi jami’an tsaro da kai farmakin da yayi sanadi na rayukan jami’ansa da wasu mutane da kwace masu babura da wasu kayayyaki. Yace irin wannan ka iya lalata kwarya-kwaryar yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla a lokacin tattaunawar da bayanta.
Har ya kammala kalamansa babu inda yace wani abu da yayi kama da abin da ake fadi a da’awar ta shafin Facebook.
Mun kuma gano irin wannan rahoto dauke da irin hoton kamar a wadannan wurare nan da nan da nan, kuma a cikinsu babu inda aka nuna bayani irin wanda yayi kama da na maida’awar a shafin na Facebook.
Baya ga rashin tafiyar bayanan da hoton bidiyon akan daki-daki idan aka kwatanta da asalin rahoton da da’awar shafin na Facebook, mun kuma lura cewa muryar danta’addar ta banbanta daga wacce take a shafin na Facebook da asalin bidiyon.
Yanayin muryar bata yi kama da ta gaske ba shima motsin jikin bai kama da na gaskiya ba.
Sai muka yi amfani da Hive, manhaja da ke gano asalin bidiyon, sakamakon kuma ya nuna cewa kaso 99.8%, an same shi ta hanyar Mutumin Giri na AI.
Sakamakon daga Hive.ai
DUBAWA ya kuma yi amfani daZhuque AI Detector, wanda sakamakon ya nuna cewa Bidiyon hada shi aka yi da AI, kamar yadda sakamakon ya nunar da kaso 95.14%

Sakamakon Zhuque AI Detector.
Gaba daya sakamakon ya nunar da cewa bidiyon dabarun ne aka yi aka hada shi da Mutummutumin Giri na AI
A karshe
Da’awar da ta nuna cewa jagoran ‘yanta’adda na sukar cewa ‘yanbindiga sune sanadi na lalacewar Najeriya inda yake cewa ‘yansiyasa masu cin hanci da rashawa sune sila Yaudara ce.
DUBAWA ta gano cewa Bidiyon dabara ce aka yi aka hada shi ta hanyar amfani da AI.